← Book details Joy Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 46

Sashe 39

Joy Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Karfe bakwai da yan mintuna a k'ofar gidansu Ameen ta yi Aliyu, zama ya yi a kan dakalin wajen ya zaro waya da niyyar kiran shi, sai ga shi, babu yabo babu fallasa Aliyu ya ba shi hannu suka yi musabaha, zama ya yi kusa da shi yana murmushi, ya dafa kafad'ar shi ya ce "Timekeeper nawa, har yanzu kana nan da dabi'arka ta r'iko ko?" Ba tare da ya kalleta shi ba ya amsa da "E kamar yadda kaima dabi'arka ta kafiya bata canza ba haka nima." Murmushi ya sake yi ya ce "Baka ce min ya jikina ba." Dage kafad'a Aliyu ya yi ya ce "Naga ai ba ka damu da lafiyar taka ba bare aje yi maka ya jiki." Dariya ya yi ya ce "To naji baka tambayeni ya jikin My Meerah ba." "Wacece haka?" Aliyu ya tambaya, amsa mashi ya yi da cewa; Masoyiyata mana Amira wacce kake fushi da ni saboda ita." Sai lokacin Aliyu ya d'ago ya kalle shi. Ajiyar zuciya Ameen ya sauke a nan ya kwashe duk abin da ya faru bayan wucewar shi ran nan har zuwa yanzu. Ya daura da "Aliyu ina matukar tausayinta, na amince zan zama maji6ancinta zan rayu da ita koda a zuciyata babu d'igon soyayyarta." "Bare ma baza a rasa ba." Aliyu ya fad'a yana hararanshi, murmushi kawai ya yi ba tare da ya tanka ba, sun dad'e suna hira, sosai Aliyu ya nuna mishi jin dadinsa game da amicewarsa da Amira ya k'ara da nusar da shi alfanun hakan ga shi karankanshi, sai dai koda wasa bai sako zancen Dr Abdul ba, don so yake ya bi komai daki-daki.

Tare suka yi isha'i bayan sun dawo daga masallaci ne, Aliyu ya shiga gida suka gaisa da Ummi, ya ce "Ummi ya mai jikin nan na kwanaki." Fara'ar fuskarta ce ta fadada ta ce "Hmmm! Aliyu mai jiki ta ji sauk'i sai hamdala, kar kaso ka ganta yanzu kamar ba ita ba." "Masha Allah, Ubangiji ya k'ara mata lafiya." "Amin Amin Aliyu nagode sosai." "To Ummi ni zan tafi a gayar da Fatima idan ta tashi." "To zata ji Aliyu a gaida mutan gida."

Tare suka fito da Al'ameen don yi masa rakiya, "Aboki ya kamata ka kira Amira mu gaisa, ka gabatar dani a matsayin babban aboki tun yanzu." Harara Ameen ya watsa masa, ya ce "Dalla Mallam muje na raka ka, matata mai tsada ce ba'a ganinta haka a arha." Rik'e ha6a Aliyu ya yi ya ce Ya ce "Da bamu san asalin balbela ba da sai tace mana daga saudiya take." Had'e rai Ameen ya yi ya ce "Me kake nufi."dariya Aliyu ya yi ya ce "Naga dai bada wani yare na yi magana ba ko?" "Kai dai ka sani ja'iri." Haka suka yi ta raha suna wasa da dariya har ya rako shi bakin Babar titi a nan suka yi sallama kamar kar su rabu.

Direct gidan su Amira Al'ameen ya nufa, ta sheka wanka da kwalliya tana jiran shi, jin sallamar shi yasa ka yin wuf ta mike, kallon da Mama ta watsa mata yasa ta yi saurin k'asa da kai, Aysha dake kallon abinda ke faruwa sai dariya take mata, hararar ta ta yi ta gefen ido tare da yin kwafa.

Shiga falon ya yi ya zauna bayan ya risina ya gaisar da Mama, Aysha da sauran kannenta suka gaishe shi, da gefen ido ya saki kallon side d'in da take, jin idanunta na yawa a kan shi, gaba d'aya ta shagala da kallon shi, Mama jin kowa ya gaishe shi banda ita yasa ta kallonta, ganin yadda ta shagala yasa ta cewa "Amira." Ina sam bata ji ba, don ta yi nisa Sam bata jin kira, ganin haka yasa Mama sake kiran sunanta a karo na biyu a tsawace "Amira!!!!" Firgigit ta yi ta kalli Mama, wani irin kunya ce ta lullu6eta sai kawai ta tashi da gudu ta bar falon, tafa hannaye Mama ta shiga yi tana sallallami.

Juyowa ta yi da zumar yiwa Al'ameen magana, sai dai wayam! babu shi babu mai kama da shi a falon sam babu wanda ya kula da sanda ya sudad'e ya fice, ai sai ta sake rafka salati tana rik'e haba take cewa; Aysha kin ga abin da na gani kuwa, dariya Aysha ta kyalkyale da shi, cike da nishad'i, "Ikon Allah, yaran zamani ka haifesu baka haifi halinsu ba ai kuwa banga ta zama ba ni hafsatu, wannan abin farin ciki har ina." ta fada tana mikewa tsaye............

Comment and share masoya

Oum Ummeetarh
09116099486
[12/29, 2:47 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀

~FARHAT~

*PAGE 36*

A firgice Mom ta shigo cikin makaranta, tana gurin aiki kirata same ta daga principal na school d'in Joy babu lafiya, office d'in principal ta nufa bayan gaisuwa principal da kanta ta yi mata jagora zuwa d'an karamin clinic d'in makarantar in da Joy ke kwance tana hutawa, don koda nurses suka tambayeta cewa ta yi kanta ke ciwo maganin ciwon kai kawai suka bata na kwaya ta sha, daga nan kuma suka bata bed rest kafin a iyayenta su zo.

Tun da ta kwanta idanunta ke lumshe, da gaske kanta ke yi mata ciwo, bayan ciwon da zuciyarta ke yi mata, har zuwa lokacin babu abin da ya ragu dangane da abin da take ji a zuciyarta,wannan kululun na nan tokare a kirjinta, babu abinda ke amsa kuwwa a kunnenta sai maganganun Fatima, babu yadda bata yi ba, don hawaye su zubo daga idanunta ko zata samu sassauci a zuciyarta amma abin ya faskara sai kukan zuciya take wanda irin wanda ke kara ma mutum kunci.

Cikin wannan yanayin Mom da principal suka iso d'akin, sarai ta ji su amma ta kasa bude ido ta kallesu, tana ji d'aya daga cikin nurses d'in wajen na yima Mom bayanin cewa kanta ta ke ciwo kuma sun yi mata abin da ya kamata sun bata magunguna, godiya Mom ta yi musu, ta matsa gaban gadon tare da dafa kanta, kan da d'umi, ga jijiya nan a goshinta sun tashi alamar dai ciwon kan mai yawa ne, kallon principal Mom ta yi ta ce "Dama tana da larurar ciwon kai tun tana k'arama, ina ga shine ya tasar mata, amma kuma gaskiya ya dad'e bai tashi ba don tun tana da shekara bakwai muka fitar da ita kasar Mexico ta ga wani babban likitan kwakwalwa shikenan bai k'ara tashi ba sai yau." Cike da Alhini principal ta jajanta lamarin. "Zan tagi da ita gida sai na kira Dr ya sake dubata." Cewar Mom, "Ok ba damuwa hakan dama shine daidai." Matso da mota Mom ta yi har bakin clinic d'in, da taimakon nurses ta samu ta isa motar don da ta mike jiri ne ya ringa dibanta dole a ka suka rirrik'eta suka taimaka mata.

Har a ka tashi Fatima kuka take yi, ta firgita sosai da yadda Joy ta yi, tunda suke tare bata ta6a ganin ta cikin yana yin makamancin wannan ba,ta yi nadamar fad'i mata wannan maganar yafi sau shurin masaki, sai dai taki baiwa zuciyarta damar gaskata zarginta na cewa Joy tana son Yaya Ameen ne, duk wani kofa da zai bata damar gasgata hakan ta toshe, har suka yi closing bata fahimci wani teacher da wani teacher bane suka shigo class d'in bare tasan me suka koyar, itama da nata kamashon ciwon kan ta koma gida, sa'arta d'aya Ummi bata nan, dama Yaya Ameen ta san baza ta same shi a gida ba daidai wannan lokacin sai da wani kwakkwaran dalili. Sallar azahar ta gabatar ko abinci bata iya ci ba, ta sha paracetamol ta hau gadon Ummi ta kwanta, babbar damuwarta rashin sanin halin da Joy ke ciki, gashi ko giyar wake tasha baza ta iya taka 'kafarta zuwa gidansu ba, haka ta yi kwanta cikin damuwa tana tunane tunane cikin sa'a barci ya yi awon gaba da ita mai cike da mafarkai barkatai.

**********

Dr Solo ya kalli Mom bayan ya gama duba Joy ya yi mata duk abin da ya makata ciki harda alluran barci don ta samu hutun zuciya da kwakwalwa, ya ce "Ciwon kan ta ne ya yi kokarin ta shi dalilin wani yanayin tashin hankali da ta shiga, amma zuwa yanzu da sauk'i, sai dai a kiyaye shigarta cikin irin wannan yanayin, gudun samun matsala." Cike da damuwa Mom ta ce "ok Dr mungode kwarai." A ranta tana mamakin wani irin tashin hankali ne Joy ta shiga haka. Sallama Dr ya yi ma Mom ya tafi tare da alkwarin sake kira zuwa dare yaji halin da ake ciki. Tare suka five da Mom daga d'akin don yi mashi rakiya.

Duk abin da Dr yake fada tana ji domin kuwa idanunta biyu, sai dai fitar su daga d'akin bai fi da minti biyar ba wani nannauyar barci ya yi a won gaba da ita.

Awa bakwai cur! Ta kwashe tana barci, kafin ta farka lokacin karfe shidda daidai na yamma, a hankali ta bud'e idanunta da suka mata nauyi, ta ji sauk'i sosai don wasai take jin kanta babu d'igon ciwo, haka ma nauyin zuciyarta ya ragu kaso hamsin cikin d'ari, a hankali ta lalla6a ta mik'e zaune, tankwashe kafa a tsakiyar gadon tare da rafka tagumi da hannayenta bibbbiyu.

Maganganun Fatima ne suka shiga dawo mata filla-filla, "Yaya Ameen ya yi budurwa very soon zai yi aure, zai auri Anty Amira." Kalmomin da su ka yi ta amsa kuwwa kenan a kunnenta suna neman rikitar mata da kwakwalwa, da sauri ta saka hannu ta toshe kunnenta da hannayenta tare da fashewa da kuka, take hawayen da take muradin fitarsu tuntuni suka samu hanya, a guje suka shiga wanke mata fuska.
Chapter 39 · 0% Book details