← Book details Joy Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 46

Sashe 28

Joy Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zaman mintuna ka dan ta kara ta mike ta na cewa, "Ummi bari na je." Ummi ta ce "Har zaki tafi, to shike nan Amira sai da safe, ki biya dakin Yayan Fatiman, Bintan tana can daga nan ma kya gaishe shi da jiki." "To Ummi nagode." Ta fada tana ficewa.

Ta kusa minti biyar a bakin kofar dakin ta kasa shiga, dakyar ta yi ta maza ta yi sallama a hankali Kamar wata mai koyan magana, karfin jin da yake da shi yasa ya jiyo ta, Fatima kam bata ji, a kan labbansa ya amsa, haka kurum ya samu kan shi da da faduwar gaba. tsoron shi daya kar ace ta fesa wannan shu'umun turaren na ta.

Minti biyu ta kuma kwashewa kafin ta sake yin wata sallamar ta karo na biyu, wannan karon da dan karfi, sai a lokacin Fatima ta ji, amsawa tayi , tare da ce wa "Anty Amira ce Bismillah! Shigo mana."

Kamar wata munafuka haka ta bude kofar net din ta shigo, daga dan nisa da shi ta samu waje ta zauna, idanunta na kan kafafun shi dake daure, wani irin tausayi shi ne ya lullu6eta, ji take kamar ta zubar da hawaye, a sanyaye ta dago ta saci kallon fuskar shi, cikin sa'a su ka hada ido, da sauri ta dauke idanunta daga cikin na shi, ta mayar kan kujewar dake gefen fuskar shi, don baza ta iya jurar ci gaba da kallon kwayar idanun shi ba, a haka ta bude baki dakyar ta ce "Ina wuni Yaya Ameen, ya jiki, ashe abin da ya faru kenan Allah ya sauwake yasa kaffara ne." A jere ta yi gaisuwar ba tare da ta jira sai ya amsa ba.

Kusan hada baki suka yi shida Fatima wajen amsa mata da "Amin ya Allah." Daga haka su ka gaisa da Fatima, tana kara tambayarta ya mai jikin, ta amsa mata da "Alhmdllh."

Zaman shiru na yan sakanni ya gifta, Fatima ce ta katse shirun ta hanyar jan Amira da hirar islamiyya, kasa sakin jiki ta yi su yi hira kamar yadda su ka saba.

Al'ameen na jin su, amma ya lumshe idanu kamar mai barci, a zuciyarsa kuwa hamdala ga Allah yake da bata feso wannan bakin turaren na ta ba.

Hirar bai yi wani tsayi ba ta mike ta ce zata wuce, Fatima tace "Kai Anty Amira tun yanzu, ki dan kara zama mana yanzu fa 8:30 ta yi." Kin zaman ta yi don jin ta take duk a takure.

Ba don Fatima ta so ba su ka yi sallama, sake satar kallon shi ta yi ganin idanu I a lumshe ta samu karewa kyakkyawar fuskarsa kallo, har da dan sakin ajiyar zuciya irin mutum ya samu relief din nan, sai da tayi ma'ishi sannan ta mike tana cewa "Fati ya samu barci in ya farka kya kara gaishe shi, sai da safe."

Duk abin da take yana kallon ta ta kasan ido har ta fice daga dakin.

Bayan tafiyarta Fatima kimtsa mi shi dakin ta yi ta kashe mishi wuta ta fice don duk a tunanin ta barcin gaske yake.

Ya dade yana tunane-tunane kafin barci gasken ya yi awon gaba da shi, koda ummi ta zo sake duba shi itama ta tarar ya na barci ne, gyara mishi rufa tayi ta yi addua'a ta tofa mishi sannan ta fice ta kulle kofar gidan tunda yau me kullewar na kwance babu kafa.

Daga nan itama ta wuce ta naimi makwanci asuba ta gari.

********

*JOY*

Daga wurin da accident din nan ya faru direct gida su ka wuce don dama akan hanya komawa suke, ta je shopping ne.

Har su ka iso gida kuka ta ke yi, Peter duk ya rude sai hakuri yake bata, zama tayi a mota dakyar ta samu ta tsaya da hawayenta, ta goge fuskarta sannan ta fito ta nufi Cikin gida, tuni kayan shopping dinta sun isa ciki, daki ta ta yi niyar shigewa ba tare da ta bari sun hadu da Mom ba, sai dai hakan bai su ba, don a main parlor ta tarad da Mom, a rude mom da yanzu take nuna mata wani irin soyayya mai karfi, ta tare ta ganin yadda manyan fararen idanunta su ka rune su ka kankance, sai dai tambayar duniya ta mata ba amsa data takura mata sai hawaye, a rude Mom ta sama aka kira mata Peter, a bakin shi take jin abinda ya faru, amma bai gaya mata cewa Al'ameen ba ne, ba tare da nuna alhini ko tausayi ba take tambayar ina wanda su ka bige din, nan ya kwashe yadda su ka yi da mutumin ya gaya mata, kuma ya tabbatar mata dan unguwar nan don ya san gidan su. Cike da jin haushi Mom ta ja tsaki ta ce "Mitsiyacin banza shi ya sani ai, ya yi wa kansa" daga haka ta ci gaba da rarrashin yarta.

Wani irin yini ta yi ranar mai matukar azabtuwa ga ruhinta, a duk sanda ta tuno lamarin kukanta saboda fil yake komawa, hakan ya haifar mata da ciwon barin kai, sai dai ta yi ta dauriya bata bari Mom ta sani ba gudun kar ta saka mata ayar tambaya, dakyar da rarrashi ta iya tsakarar abinci haka ta wuni a kwace kamar ruwa.

Bata gane lamarin ya girmama a gareta ba sai da dare ya yi, kememe barci ya kauracwa idanunta, don a duk sanda ta rintse idanu shi take gani,cikin raunika da yadda yake dingisa kafa cike da azaba, haka ta kusa raba dare tana hawaye, dakyar barci barawo ya saceta, sai dai ko awa biyu bata cika ba ta farka a firgice ta yi mafarki wai Al'ameen ya mutu, ta shi ta yi daga kwance ta zauna da duwawunta a tsakiyar gadon ta rafka tagumi tana ta tsiyayar hawaye ji take kamar ta yi tsuntsuwa ta je taga halin da yake ciki, ya zama dole gobe ta je ta duba ba shi idan ba haka ba hankali ta bazai taba kwanciya ba.............

Gashi nan harda na jiya😬

Gamai bukatar shiga group ya tu tubeni kai tsaye.
09116099486.
[12/29, 2:42 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀

~FARHAT~

DAGA ALƘALAMIN👉
*AyshaNalado*

ƘARƘASHIN JAGORANCIN👉
*Mikiya Writer's Association*

*PAGE 26*

No editing ayi ta hakuri🙏

Washegari haka Ummi da Fatima su ka tashi da hidamar Al'ameen, abin ma yazo musu da d'an sauk'i ne saboda shi d'in jarumi ne, bai sakar musu ragamar komai ba, yakan yi iya k'ok'arinsa, idan ya kasa sannan ya naimi taimako, yanzu ma Fatima ce ta yi sallama d'auke da abincin karin kumallon shi a hannu, ga mamakinta a tsaye ta same shi yana bin bango zai fito waje har ya kai bakin k'ofa.

"Subhanallah! Yaya ina zaka je?" Murmushi ya sakar mata, ya ce "Na gaji da zaman d'aki ne k'anwata zan fita tsakar gida in sha iska." Kwa'be fuska ta yi ta ce "Shine baka kirani in taimaka maka ba, idan ka fama ciwon ka fa?." Ta karashe maganar tana k'ok'arin rik'e shi, ya ce "No Barshi Fatima zan iya, ki je ki shimfid'a mini tabarma a tsakar gida." Cike da mamakin karfin halinsa ta ce "To Yaya." Ta fi ce.

Kici kicin shimfid'a tabarman da ta ke yi ne yasa Ummi dake kitchen lek'owa "A'a Fatima ya haka kuma?" Cewar Ummi sanin ba wai sun saba zaman tsakar gida da safe bane.

"Yaya ne ya ce na shimfid'a mi shi zai fito yasha iska wai ya gaji da zaman d'aki." Kafin Ummi ta ce komai sai gashi ya shigo da bin bango da dabara ya ke lalla6awa, da sauri Ummi ta zo ta rik'e shi, ta na cewa "haba Amintacce, ai da ka yi magana sai a taimaka maka." Da murmushi ya ce "A'a Ummi zan iya ai."
Ita dai bata yarda ba sai da ta rik'e har kan tabarman da Fatima ta gama shimfid'awa ya lalla6a ya zauna, yana rintse ido lamar yana jin azaba, cike da tausayawa Ummi ta ce "Sannu Yayan Fatima Allah ya sauwak'e, ka yi k'o'kari ma wallahi zaman da'ki babu dad'i ga namiji, zaman dak'i ai sai mata, Allah dai ya ta shi kafad'a yasa kaffara ne." Ya amsa da "Amin Ummi."

Kayan tea Fatima ta jera a gaban shi da flask d'in ruwan zafi ta shiga had'a mi shi, kallon ta ya yi ya kalli Ummi ya ce "Ummi yau kuma tea zamu sha, babu kamun ne." Ta ce "A kwai naga baka da lafiya ne, kamar zaka fi son shayin shiyasa na bada kudi ta siyo buredi da sauran kayan hadin tunda shi kokon naga kayan fitsari ne." Yamutsa fuska ya yi alamar baiso ba, amma bai ce komai ba, sai kallon Fatima da ya yi ya ce "Sister ka d'an za ki hada shayin." Ganin yanayin shi yasa Ummi cewa "ko a dama maka kunun ne? Naga kamar baka son shayin." Baya son bata wahala , sai kawai ya ce "A'a Ummi ki barshi kawai zan sha." Kafin Ummi ta ce wani abu Aysha kanuwar Amira, ta yi sallama a tsakar gidan.

A tare suka amsa mata, ummi ta ce "Aysha ke ce tafe." Ta ce "E ni ce, ina kwana ummi ya mai jiki. " "Alhmdllh da sauki." Juyawa ta yi bangaren Al'ameen shima ta gaishe shi tare da yi masa ya jiki, ya amsa da "
Alhmdllh."

Basket mai dan girma dauke da kuloli da flask ta fito da shi daga hijabinta, ta ajiye gaban Al'ameen tare da ce wa "Yaya Ameen wai gashi, in ji Anty Amira ta ce na kawo maka wai tana gaishe ka da jiki."

Share Aysha ya yi kamar bai ji abinda ta ce ba, wani banbarakwai ya ke jin lamarin, amma yarinyar nan bata da hankali mai take tunanin Ummi da Maman Amira zasu zata idan suka ga haka.

Ummi kam murmushi ta yi ta ce "Lallai an gaida Amira harda hidima haka ki ce mata Amintacce yana godiya." Fatima murmushi take yi a ranta tana lallai Anty Amira kin zurma da yawa Allah dai ya tabbatar da wannan lamarin.

Sallama Aysha ta yi musu Ummi ta ce "Tsaya ki amshi tukwuici." Tana kwance habar zani da sauri Aysha ta yi hanyar waje ta na cewa "A'a Ummi wallahi ki barshi nagode."
Chapter 28 · 0% Book details