Sashe 4
Joy Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Gaban shi ne ya fad'i ganin yadda lokacin d'aya manyan fararen idanunta suka rine zuwa launin jaa, take yaji wani shakkarta da tsoronta ya kama shi duk da kuwa ya girme mata don ya bata kusan shekara daya a haihuwa.
Bai gama fita daga wannan yanayin ba ya tsinkayi muryarta a kunnayenshi, a kausashe ta ce "David!!! Burin ka ya cika yau ka hadani da iyayena ko, nasan kaji dadi ranka yayi maka fari ko? To ka rubuta ka ajiye na rantse da wanda ya busa min rai da numfashi sai kayi nadamar wannan abin da ka aikata." Mikewa tayi ta kama hanyar hawa upstairs.
Ji yayi duk ya muzanta ida ta wuce bai mayar mata da martani ba zata ga kamar ya tsorata da furucinta ne haka yasa ya danne zuciyar shi tare da ce wa "Joy James." Da karfi, dakatawa tayi tare da juyowa suka hada idanu, takowa yayi ya iso gabanta ya tsaya, kamar zai fadi wani magana, sai kawai ya barke da wani mahaukacin dariya mai ban haushi, wani irin yawun takaici Joy ke hadiya a jejjere, ganin kuka na shirin kwace mata yasa ta juya a guje ta karkare hayewa saman bata zame ko ina ba sai dakinta kan gado ta fada tare da fashewa da kuka da iya karfinta.
Mom koda ta shiga dakin ta kasa zama tayi safa da marwa kawai ta shiga yi ta kai gwouro ta kai mari, hankalinta a matukar tashe, girgiza kai tayi a bayyane cikin irin yaren da David yama Joy magana d'azu a school ta shiga ce wa " meke shirin faruwa da ni ne ni Alice, kardai asirin da na rufe tsayin shekaru goma sha biyar ke shirin tonuwa, tabbas ya kusa tonuwa." Bango ta kai ma duka kafin kamar zararriya ta ce "Ina!!! Ba zan taba bari hakan ya faru ba indai na haifu cikin pastor Samuel da Mrs Deborah." Da sauri ta rarumi wayarta ta danna ma wani lamba kira, ringing wayar keyi amma ba'a daga sake kira tayi still ba,a daga ba jife tayi da wayar a kan gado tare da zama da'bas tana tafa hannaye, can wayar ta dake kan gado daga bayanta ya fara ringing da sauri ta raruma don duk a tunanin wanda take ne ya biyo bayan kiran, ganin sunan me kiran ne yasa gabanta yankewa ya fadi, *Dr Hassan* ta ambaci sunan a bayyane tana zare ido lallai bata ga ta zama ba wai an saci san barawo.
Tafi awa d'aya tana kuka kamar ranta zai fita, gaba daya ta hargitsa suman kanta ko takalmin school bata jire ba jakar ma jifa da shi tayi da shi can gurin kofar toilet, jinta take yi wani iri ji takeyi kamar ta aikata baban zunubi tunda take da Mom bata taba koda dungurinta bane, bata taba fushi mai tsanani da ita haka ba duk kuwa iya girman laifin da zata mata, amma yau ita ce Mom ke hankadewa lallai ta san ba karamin fushi Mom ta yi da ita ba, bata ga laifin Mom ba domin tun ba yau ba ta riga ta san yadda Mom ta kasance mace mai kishin addininta, tana tsananin kyamar addinin musulci, bata shan inuwa daya da musulmi, tana kyamarsu kamar me, ji tayi baza ta iya jurar fushin Mom, hakan yasa ta mike dakyar ta nufi dakinta.
*******
KANO STATE
*Dr Hassan special hospital Amenity word room number 5*
Wani farin dattijo ne me kimanin shekaru 65 a duniya ke kishingide akan gadon marasa lafiyar dake madaidaicin haddadden dakin wanda kwata kwata baiyi kama da dakin asibiti ba, hannun shi sakale da karin ruwa, saman roofing dakin fuskar shi ke fuskanta idanunshi a lumshe, idan ba ka kula da yadda yake motsa bakin shi a hankali da kuma yadda yake danna caunter dake sakale a daya hannun shi da babu Karin ruwa ba zaka dauka barci ya ke yi.
Daga gaban gadon wata dattijuwar mata ce zaune a kan daya daga cikin kujeru biyu dake dakin, a kalla zata kai shekaru hamshin da haihuwa amma tsabar hutu jin dadi jin iya kula da kai da yadda naira suka zauna zaka dauka batafi 38 to 40 ba, kallon dattijon mutumin nan take yi fuskarta cike da matsanancin damuwa, hannunta plate ne mai dauke da tuwon almaka da miyar alayyahu da nama, kasa ta yi da muryar a karo na barkatai cikin sanyi ta ce "Alhaji ka tashi kaci abincin mana gashi na zuba maka tun dazu yana hucewa." Bude lumsassun idanunahi yayi kafin a hankali ya ce "bana jin yunwa bazan ci ba." Shiru ta yi tana ci gaba da kallon shi tana tuna rabon shi da abinci tunda asuba da Dr yasa shi yasha tea lokacin da za'a daura mishi drip, kallon agogon dake manne a bangon dakin tayi karfe biyar harda mintuna biyu, ajiyar zuciya ta sauke, cikin son jaraba sa'arta ta sake ce wa "alhaji kayi hakuri ka tashi ka ci abincin nan, lafiya bazai samu ba idan har haka cin abinci." Wannan karan bai bude idanunnashi daya mayar ya lumshe ba kuma bai amsa ta ba, sai ci gaba da yayi da motsa bakin shi alamar yana ci gaba da lazumin shi, ganin haka yasa ta cigaba da yi mai magiya, jin ta dame shi yasa ya bude idanu tare da daka mata tsawa "keee! Nace bazan ci ba dole ne wai." Ta ke alhini da tausayin dake kan fuskarta ya bace bat lokaci daya bacin rai da bakin ciki suka maye gurbin su, ranta ya kai kololuwar baci , a hassale ta ce "wai har sai yaushe ne zaka cire wannan damuwar daga ranka? sai yaushe ne zaka dangana ka fawwalawa Allah lamuranka?, yau fa kimanin shekara goma sha biyar kenan, sai yaushe ne, iyeee alhaji na ce wai yaushe ne?" Ta karshe maganar cikin karaji tare da fashewa da kuka.
Bude lumsassun idanun shi yayi ya kalleta kika take yi bil hakki, guntun murmushin karfin hali ya saki, cikin muryar shi ta marasa lafiya ya ce " ya isa haka Lubabatu kina son kisan sai yaushe ne ko?" Da sauri ta gyada kai tana sharar kwallah, idanun shi ya saka cikin nata kafin yace a kausashe "sai ranar da asirin wad'anda suka kashe ta ita da abinda ta haifa Tonu...."
Yau ba yawa kuma ba editing🙏
Me bukatar shiga group ya tuntubeni ta wannan lambar
09116099486
[12/29, 2:20 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀
*BY*
*AYSHA NALADO*
*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
*LITTAFI NA ƊAYA*
*PAGE 4*
Mom na kallo har kiran Dr Hassan ya katse bata iya d'agawa, gaba d'aya a tsorace ta ke, banda zufa babu abin da ke tsatsafo mata, ajiye wayar ta yi a gefen bed ta rafka tagumi da hannu bibbiyu, wayarta ce ta sake d'aukar ringing kallon wayar ta yi bata d'auka ba don duk daukarta Dr Hassan ne again sai dai ganin me kira yasa ta zabura ta mi'ke, hannu na rawa ta yi received, tun kafin ta kai ga cewa komai ta ji ya kece da wata irin mahaukaciyar dariya wanda sai da ta tsorata, kusan minti uku ya kwashe sai da yayi mai isar sa kafin lokaci d'aya gimtse fuska.
Jin yayi shiru yasa Mom cikin rawar baki ta shiga kokarin yi ma shi bayani, wani tsawa ya daka mata Wanda saura kadan ta saki wayar, cikin amon sautinsa mara dad'in ji ya fara magana cikin irin yaren su ba ibo "kin yi sake! Kin yi sake! Na ce kin yi sa ke Alice, tabbas abin da kike 'boyewa tsayin shekaru sha biyar zai bayyana matukar baki raba alakar *jini da jini* ba." Kan Mom ya kulle take ta 'kara tsorata jin ya ce asirin data binne tsayin shekaru zai bayyana, bata gane me yake nufi da Kalmar *jini da jini* ba, sanin hakan da yayi ne yasa ya ce "kiyi gaggawan raba Joy da ra'bar wadan nan ahlin musulman idan kuma ba haka ba." Sai kawai ya kara kecewa da dariya kit ya kashe wayar ba tare daya mata cikakken baya ni ba ya barta tana zare ido.
Hakan yasa da sauri ta sake dialing number shi, daga wa yayi bai bata damar yin magana ya ce, "babu taimakon da zan miki idan har baki rabata da wadannan ahlil ba, dama na gaya miki tun farko ai karkiyi sake, idan kuma kika yi sake tabbas jini da jini ba karya bane." Daga haka ya sake kashe wayar bayan ya kwashe da dariya kamar mahaukaci.
lallai bata ga ta zama ba, dole ta yi duk yadda zata yi domin taraba Joy da wadan nan tsinannun talakawan musulman, tana son jin cikakken bayani tana son sanin me Kalmar jini da jini yake nufi dan baza ta yi sake wani dan kankanin abu ya bata mata aikinta na kimani shekaru goma sha biyar ba.
Saga da marwa ta tashi yana yi tare da tunanin me ya kamata ta yi, wasl zai taimaka mata, cak ta tsaya lokacin da kwkwalwa ya hasaso mata mafita.
Kamar zararra haka ta rarumi wayarta ta fara dialing lambar Papa.
Daidai nan kuma Joy ta karaso dakin, tana tangad'i kamar yar maye tsabar bata cikin hayyacinta, motsinta yasa Mom saurin dagowa ta kalli kofar, gabanta ne ya fadi ganin yadda Joy ta fita hayyacinta idanunta sukayi luhu luhu cikin kasa da awa daya, kwarai rauninta yaso ya bayyana a lokacin, saboda ba karamin so take ma Joy ba, a duniya Joy ce kadararta Joy ce arzikinta Joy ce rufin asirinta, dakewa ta yi ta dauke kai daga kallonta ta mayar kan wayarta,
Halin da joy ke ciki yasa bata kula da yanayin yadda Mom din ke rude ba, zubewa ta yi akan gwuiwowinta daga bakin kofar don tana jin tsoron karasawa kusa da Mom, ta hade hannayenta alamar roko sannan ta sake fashewa da kuka Wanda dama cikin sa take, ba ta ce ko mai ba sai kuka da takeyi ba saurarawa.