← Book details Joy Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 46

Sashe 20

Joy Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki ta fara takowa, ta gaban shi ta bi ta fice daga zauren, minti biyar ya dauka kafin bayanta yabi bayanta, tunanin shi zuwa lokacin ta dan yi nisa da gidan, sai dai ga mamakin shi yana fitowa, ya tarar da ita durkushe a kofar gidan tana sharar kwalla, ranshi yaji yayi mugun baci, wato bata tafi ba kenan don rainin hankali, a hasale ya daka mata tsawa " keeee!" A zarane ta dago ta watsa mai idanunta da suka fara sauya launi, take ya ji duk wani karsashinsa ya tafi, kasancewar sa dakkaken namiji mai dakakkiyar zuciya yasa ya dake ya ce "Me ya kawo ki gidanmu." Shiru ba amsa sai sabbin hawaye dake sake shatata akan dakalin fuskarta, ya ce "Ok na gane yau ma kin biyota har gida ne ki sake ci mata mutunci kamar yadda rannan kuka ci mata matunci a gidan Ku keda mahaifiyar ki ko?" Da sauri ta shiga girgiza kai cikin shirin fashewa da kuka, ya ce "Kul! Kar ki min kuka a nan. Kuma ki bud'e kunnuwar ki da kyau ki saurereni, daga yau sai yau idan na sake ganin wadan nan kazaman kafafunta naki a gidan nan, hmmmm! Sai na lahira ya ciki jin dadi. Oya kafin in bude idanuna ki 6ace daga kofar gidan nan, daga yau babu ke babu Fatima har abada." Rushewa ta yi da kukan da take ta kokarin rikewa tun dazu, cikin magagi ta ce "Pls Yaya Alemin karka raba ni da Fatima wallahi ba laifi na bane laifin Mom dina ne idan ka raba mu, zan shiga tasananin damuwa ku yi hakuri da abinda ya faru rannan Ku yafe min." Ya ce "Ok baza ki tafi ba ko? Ina zuwa." Ya fad'a yana shirin juyawa zuwa cikin Zaure, caraf ya ji ta riko kafafun shi, wani irin shock ya ji a jikin shi wanda tunda yake bai taba jin irin shi ba, hakan yasa yayi wani irin fusgar k'afunshi da mugun karfi, har saida Joy ta fad'i tare da bige goshi da wani dutse.............

Na gode da addu'o inku gareni, na j sauki sosai hannu ma da sauki alhmdllh ngd kwarai da kulawa.

Me bukatar shiga group din joy ya tuntubeni ta wannan Layin.
09116099486.
[12/29, 2:37 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀

~FARHAT~

*PAGE 18*

Yauma ba editing a tai ta hakuri🙏

Ba tare da ya kula da fad'uwar da tayi ba ya shige zaure da sauri ya bugo k'ofa. Zafin buguwar da taji yasa ta saki yar k'ara "Acchh!" da siririyar muryarta , hannu ta kai ta dafe goshinta dai dai gurin da ta bige, danshi da ta ji a wajen yasa ta dubawa da sauri, zaro ido tayi a tsorace ta ce "Jini! wayyo my Dad." Sai kuma ta fashe da kuka tana yarfa hannaye, rabon da jini ya fita a jikinta irin haka har ta manta, ji tayi ranta ya mugun baci da abinda Al'ameen ya mata sosai ta kullace shi, dama tun farko bata ta6a mishi kallon mai saukin kai ba, kallon wani irin murd'add'en mutum mugu mara fara'a take mishi, sai gashi yau ya tabbatar mata da hakan, mikewa tayi ta kakkab'e jikinta ta na hawaye ta kama hanyar barin kofar gidan.

Duk abin da take yi yana tsaye daga cikin duhun zaure yana kallo, ji yayi zuciyar shi ya sosu, haka kurum kukanta ke ta6a mishi zuciya, irin abinda yake ji a duk sanda ya ji Fatima na kuka ya dinga ji, gaba d'aya tausayinta ya ji ya kama shi, idan ya barta ta fice haka, anya ya kyauta kuwa, Annbin Rahama ya hane mu rama sharri da sharri, ya gamsu da irin soyayyar da ta ke yiwa yar uwar shi kodan wannan ya kamata ya raga mata, da sauri ya fito ya biyo bayanta, lokacin har ta riga ta bar kwanar gidan, sunanta yake son ya kira amma ya kasa, sau uku yana gwada bude baki sai dai ya mayar ya rufe, hakan yasa ya k'arasa da dan gudu gudu ya isa gareta, jin karan gudu daga bayanta yasa ta juyowa da sauri har zuwa lokacin kuka take, daai dai nan shi kuma ya iso inda take, kasancewar tana cike da haushin sa yasa ko d'ar bata ji ba sai dai ta kasa kallon fuskar shi ko da gigin wasa, a gabanta ya tsaya sai kuma ya rasa me zai ce mata, samun kanshi yayi da zaro handkerchief daga aljihun shi ya mika mata, kin Karba tayi sai ta samu kanta da dan zumbura baki.
Zaro ido yayi ganin abin da tayi, sai kuma ya samu kanshi da sakin murmushi wanda shi karan kanshi bai san ta su6uto ma shi ba, yarintarta yake gani karara idan tayi wani abin San Fatima yake ganinta.

A hankali ya kai hannun shi fuskarta da nufin ya share mata hawayen, a razane ta dago idanunta ta karaf! Ya sauka cikin nashi, wani irin lamari ne wanda tunda take a rayuwarta bata taba tsintar kanta cikin shi ba ya afku da ita cikin abinda bai fi kiftawar ido ba, sakone na zuciya wanda ke shiga ba tare da neman shawaran mamallakinta ba bare izini.

Samun kanta tayi da Kasa janye idanunta daga cikin nashi duk da irin duguden da zuciyarta keyi, shima bai dauke idanun shi ba a haka kuma bai fasa goge mata hawayen da yayi niyya ba. Murmushin daya Dakar mata ne ya fargar da ita yanayin da da ta shiga, da sauri ta kawar da fuskarta daga gareshi, tana jan numfashi da karfi don ji ta yi numfashinta na shirin daukewa, bata dawo hayyacinta ba ta tsinci muryar shi a kunnenta cikin shigar rarrashi yana cewa "I'm sorry! Ban yi don na cutar dake ba." Maimakon ta amsa mishi sai kawai ta juya da gudu gudu ta bar shi a tsaye rike da handkerchief.

Ya fi minti goma yana bin inda ta bi da kallo, shi karan kan shi bazai ce ga abinda yake kallo ba, Me yasa ta wuce ta barshi ba tare da amsa mishi ba, ko dai bata hakura ba ne, "Ya ilahi!" Ya ambata a baiyane. Ajiyar zuciya ya sauke kafin yayi amfani da dakakkiyar zuciyar shi wajen yi fatali da abinda raunatacciyar zuciyar shi ke shirin ingiza shi a kai.

********

Lokacin da Amira ta samu sakon Al'ameen, ruwa ne kawai bata zuba a kasa ta sha ba saboda farin ciki abin har saida da ya ba Fatima mamaki, duk da karancin Shekarunta sai da ta diga mata ayar tambaya.

A daren ranar kuwa bata ko daga kafa ba tana idar da sallar isha sai gata dauke da tarin littafanta, Al'ameen din ma shigowar shi kenan daga masallaci yana dakin sa ko abinci bai kai ga ci ba. Yana jin sallamarta ya bata rai shi har ga Allah zata takura mashi.

A gaban Ummi dake zaune a tsakar gida ta zube cike da girmamawa ta ce "Barka da dare Ummi."Fuska a sake Ummi ta ce "Yawwa Amira maraba, har kin shigo karatun ne?"Eh wallahi Ummi." "To madallah! Allah yayi jagora, shima Yayan Fatiman yanzu ya shigo gidan."
"Allah sarki, to ko na koma in dawo anjima kafin ya gama kimtswa." "A'a yi zamanki yar nan idan ya ganki zaune zaifi maida hankali ya kimtsa da wuri."Ta amsa da "To Ummi."dadi fall ranta don dama ta dai fada ne kawai ba don ya kai zuci ba.Dan waige² tayi, kafin ta ce "Ummi Fatima bata nan ne.". "Tana daki ina ganin sallah take."

Hira su ka shiga ta6awa da Ummi, a haka Fatima ta fito ta same su. Da fara'a ta ce "Laaa! Anty Amira har kin shigo." Ta ce "wallahi Fatima ba shigo." "To bari na sanarwa Yayan yana dakin shi." Duk yana jiyo su a ranshi ya ja karamin tsaki, ya rasa me yarinyar ta taka da suke rawan jiki da ita dhi shiga harga Allah bata kwanta mashi a rai ba.

Sallamarta Fatima ya katse mai tunani, a dakile ya amsa mata don haushin Amira ya shafe ta, tura net door din tayi ta shiga, ta same shi zaune yana latsa waya, da zumudi a muryarta ta ce "Yaya Anty Amira ta zo karatu." bai dago yakalleta ba ya ce "Na sani, ki kwaso littafanki kema Ku jirani tare zaki dinga karatun." Ta amsa da " To Yaya." Yana jin ta tana gaya musu sakon shi. Said da ya kwashe minti sha biyar kafin ya taso. Ummi ya gaisar, kafin ya samu guri ya zauna, a sanyaye Amira ta ce "Ina yini Yaya Ameen." Sai lokacin ya kalli side din da take, ya amsa mata da "Lafiya." Ummi ta ce "Fatima kawo mishi abincin shi yaci tukunna kafin Ku fara karatun." Da sauri ya ce "A'a Ummi bari mu gama tukunna." Bata ce komai ba, ya kalli Fatima da Amira ya ce "Ku matso" Matsowa sukayi ya kunna fitilar wayar shi ya haska, ya dauki daya daga cikin papers na past question da Amira ta zo da shi ya bude ya dan dudduba sannan ya dan kalleta ya ce "Bismillah ko." Da kyar ta iya dagowa ta saci kallon shi, ta re da gyada kai.

A tsanake cike da baiwa da basida ya shiga yi mata bayanin kowani question dalla dalla, duk da kasancewarta ba mai kaifaffan brain ba, tsaka tsakiya take, hakan bai hanata dan ganewa ba, wai damma ta fi maida hankali ta akan kallon kyakkyawar fuskar shi, tana sakin murmushi tare da kiyasto abubuwa da dama a ranta.

Sai gurin goma saura ya dakata, tare da rufe paper ya dago ya kalleta ya ce "Zamu dakata a nan said Allah ya kaimu gobe, idan kina da tambaya kiyi akan abinda baki gane ba." Da sauri ta girgiza kai, ya ce "ok shike nan gobe idan muka karkare subject din ni zan miki tambayoyi tunda kince kin gane ko?" Ya karashe maganar da tambaya da sauri ta sake gyada ka ya ce "To sai da safe." Ba don ranta ya so ba ta amsa da "To sai da safe Yaya Ameen nagode sosai Allah ya saka mata da alkhaiti ya baka mata ta gari." Ummi da Fatima ne suka amshi, shi kuwa kasa amsawa yayi don jin addu'an yayi banbara kwai.
Chapter 20 · 0% Book details