← Book details Joy Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 46

Sashe 38

Joy Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Yanzu damuwar Al'ameen bai wuce Aliyu ba, tun daga ranar da wannan abin ya faru basu sake haduwa ba ranar da damuwa yadda su ka rabu ya kwana, a zuciyar sa yaji bai kyauta ma shi ba, ya je gidan su sau biyu baya samun shi, kiran waya kam ya mishi ya fi sau shurin masaki amma baya d'agawa.

*********

Tun da Joy taje gida take ta tunanin albishirin da Fatima ta ce , zata mata a kan Yaya Ameen, kasa juriya tayi don akan duk abin da ya shafe shi zuciyar ta azalzala take, babu yadda bata so ba ta samu hanyar fita ran Sunday zuwa gidan sai dai babu dama, don Mom tasata tayi a gaba tunda sassafe suke wuce church ranar acen suna kusa wuni, haka ta kwana da daukin wayewar garin Monday, sai dai cikin rashin sa'a ranar karatu ta yi musu zafi, kuma da aka yi closing Mom ce da kanta ta zo daukarta, ba don ta so ba ta bita suka wuce gida da kudirin koma menene gobe baza ta rabu da Teetee ba sai ta gaya mata......
[12/29, 2:46 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀

~FARHAT~

*PAGE 35*

Washegari tun six thirty ta gama shirin school saboda gand'oki, a gaggauce ta sauko dining, a shirye ta same shi tsab! Kamar yadda ta tsammata, sai dai tea da cake kadai ta iya sha shima kad'an, sake kallon agogon dake daure a tsintsiyar hannunta ta yi, ganin bakwai saura yasa ta naima waje a parlour ta zauna tana kallon cartoon a tv duk da kallon kawai take amma hankalinta baya gurin, karfe bakwai dai-dai ta nufi upstairs, direct d'akin Mom ta nufa, tura kofar ta yi ta shiga ba tare da knocking ko excuse ba. Mom bata falo dama bata yi zaton ganinta a nan ba, kai tsaye ta nufi bedroom, muryar Mom da ya daki dodo kunnenta ne, ya dakatar da ita daga karasawa cikin d'akin.

Cike da tabbatarwa ta ke cewa "Kar ki damu Esther bani da kowa a duniyar nan bayan ke, ke kad'ai ne iyayenmu suna haifemu tare mu biyu kuma a yanzu basa raye, ki sani ita d'in ba komai bace a gareni fa ce tsanin cikar burina, lokacin dana dibar mana na daf da k'aratowa, sai na tabbatar da ya mallaka mata komai nasa daidai da tsinke bai bari ba, zan kashe shi, sannan daga baya ita......" Sauran zancen ne ya mak'ale lokacin da idanunta suka sauka a kan Joy rik'e da k'ofa, da alamar ta ji me take cewa' Jikinta ne yaso daukar rawa, amma tuna wacece Joy yasa ta dake rainonta ce, ta fi kowa sanin halinta bata da shiga sabgar da bai shafeta ba. "Excuse me." Ta fad'a tare da sauke wayar daga kunnenta, sakar mata murmushi ta yi, cike da wayancewa ta ware mata hannayenta tare da cewa; "Come to me my dearest princess." Martanin murmushi ta mayar mata ta k'arasa ta fad'a jikinta suka jungume juna, "Morning my lovely Mom." Joy ta fad'a tana zare jikinta daga na Mom, rike hanayenta Mom ta yi ta na kallon ta cikin ido don son karantar yanayinta ta ce "Morning my Happiness, har kin shirya? "Yes Mom har ma na yi breakfast." "Auh! Shine babu jira ko gud." Dariya ta kyalkyale da shi, "I'm sorry Mom na tashi da yunwa ne." "Ok no prblm." Mikewa ta yi tana cewa; "Bye bye! Mom till I came back." "Ok princess nima yanzu zan shirya na tafi gidan antynki Esther, tana can tana rigima da Mr Moses wai sai ya sake ta, yanzu ma da ita nake waya kika shigo Esther bata jin magana lamarinta ya fara isa na." Ta karashe maganar tare da dafe kai cike da takaici, "Ki yi hakuri Mom ki ci gaba da abin da kike yi na alkhairi zaki samu lada." Tana gama fad'in haka ta fice, a parlour n k'asa ta dauk'i jakarta ta fito compound, already Peter na jiranta basu 6ata lokaci ba, ta shiga ya tukata zuwa school.

Da biyu Mom ta fad'i wannan magana, don ta kauda hankalin joy daga zargi ne, hakan kuwa ya yi tasiri, da farko kalmar kisan da ta ji a cikin maganganun Mom sun saka ta a shakku, sai dai jin zancen Esther yasa ta yi watsi da lamarin don bata kaunar abin da zai had,a ta da tilon kanwar uwartata, tun a bedroom d'in Mom ta watsar da batun, ko kafin su isa school ta shafe babin batun a ranta.

Shiganta aji da mintuna kad'an Fatima ta iso, kasancewar babu teacher a ajin yasa ta tashi da gudu ta tare ta suka rungume juna, dakyar suka saki juna suka k'arasa sit suka zauna, sauran student na masu dariya masu jin haushin kawancensu kuma na ta6e baki da zund'en su.

"Teetee tell me about him, ki gaya min mana sai ja min rai kike yi." Dariya Fatima ta saka ta ce "Sai during break." Fushi Joy ta yi ta juya mata baya, magana Fatima ta dinga mata amma ta share da gaske fushi ta yi sosai don harda guntun kwallah ta share ba tare da sanin Fatin ba.

Abin da ya ba Fatima mamaki da kuma dariya ana ringing bell, Joy ta kalleta tare da cewa; "Oya tell me." Dariya Fatima ke son yi, amma sanin halin Joy na saurin fushi yasa ta danne, ta yi abinta a ciki, narai-narai Fatima ta yi da ido ta koma kalar tausayi kafin ta ce "Zan gaya miki amma sai kin saki fuskarki, kinji my beautiful friend." Murmushi ta saki, Fatima na dariya ta ce "Ba irin wannan ba gaskiya, idan ba haka ba kuma bazan fad'a ba." Ga mamakinta sai ji ta yi Joy ta kyalkyale da dariya. Gimtse nata dariyar ta yi tana binta da kallon mamaki, gira Joy ta d'age ta ce "A kan Yaya Ameen komai zan iya yi domin nima a yanzu shine komai nawa." Rass gaban Fatima ya fad'i da sauri ta kauda tunanin da yazo mata zuciya, jin Joy din ta ci gaba da cewa; "Shine ya bani matsayin kanwa, ya zame mina Yaya dan uwa abin da na nake tsananin kewa shekara da shekaru, ina jinsa har cikin bangon zuciyata." Murmushi Fatima ta yi ta ce "Umm! Kaji masu yayyi muma Allah ya bamu." "Amin!" Joy ta amsa mata a gatsile. Fatima ta ce tana murmushi, "To albishirinki." "Goro fari kal!" Ta amsa mata, "kawo kunnenki kiji." Matso da kunnenta ta yi fuskarta a washe yau dai finally zata ji abin da Teetee ke ja mata rai a kai kwana da kwanaki, Fatima ta kama kunnen ta matsa da bakinta cikin rad'a ta ce "Yaya Ameen ya yi budurwa very soon zai yi Aure, zai auriAnty Amira....." 6at tattausar murmushin dake kwance a kan fuskarta ya ba ce within second, kamar saukar gudumar wuta haka kalaman Fatima suka daki zuciyarta take idanunta suka fara juyawa, wani irin dunkulallen abu ya tokare mata kirji, take numfashinta ya shiga sama da kasa kamar mai cutar Asthma.

Jin shiru yasa Fatima kallon ta, a tsorace ta zaro idanu tare da furta "Na shiga uku." A bayyane "Joyyy!"ta kira sunanta da karfi tana jijjigata, suuu! Ta ta tafi zata fad'i, da sauri Fatima ta rikota cikin tashin hankali take kiran sunanta da karfi tana jijjigata, lamarin daya jawo hankalin yan tsirarun student d'in dake ajin, da gudu wasu suka yo kansu suna tambayar menene, ya yin da wasu suka tafi kiran class teacher d'in su. Wata cikin yan ajin ne tayi dabarar fasa pure water mai sanyi da ke hannunta ta shiga antaya mata daga kai zuwa fuskarta, wani irin ajiyar zuciya mai karfi ta shiga saukewa tana kokawa da numfashinta tare da kokarin hadiye kululun daya tokare mata wuya amma ina! Abin ya ci tura. Tuni Fatima ta dad'e da fara kuka, hannayenta bisa kai, ta ke cewa; "Na shigo uku! Joy dan Allah kar ki mutu ki barni, wasa nake yi miki." Ana cikin haka class teacher ya shigo bayan shi nurs na school d'in ne cikin uniform d'in su, d'auke da first aid box.....

Kishin balbal😱

***********

A karo na babu adadi ya sake trying lambar, yana kallo har kiran ya katse kamar koda yaushe ba'a d'aga ba, text ya shiga rubuta ma shi na ban hakuri, tare da tabbatar mashi a kan lallai yana so su had'u a kwai story.

Ajiyar zuciya Aliyu ya sauke lokacin da ya gama duba sak'on, ya tabbatar ya zuwa yanzu abokin nasa ya yi laushi, zai jaraba sa'ar shi wata kila ya dace. Replay ya yi ma shi cewa; Zai shigo after magrib.
Chapter 38 · 0% Book details