← Book details Joy Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 46

Sashe 44

Joy Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta yi kuka sosai wanda rabonta da yin irin shi tun rasuwar marigayin mijinta, dakyar ta danne zuciyarta ta mike ta dauro alwala, a kan darduma ta karkare wayar gari ranar, Da safe haka ta wayi gari idanunta sun yi jajur sun kumbura, Fatima ta tsorata da ganinta, sai dai yadda ta tsare gida sai ta kasa tambayarta me ya same ta, hankalin Al'ameen ba karamin tashi ya yi da ganin ta ba, sai dai kamar yadda Fatima ta kasa tambayarta haka shima ya kasa,jiki babu kwari ya shirya ya fice daga gidan zuwa wajen harkokinsa.

Karfe goma da rabi ta gama shirinta tsab cikin riga da zani na atamfa ta sanya hijab dinta gogagge mai matsakaicin tsayi, fes ta fito a matashiyar mace kyakkyawar gaske mai cike da haiba da kamala, sallama ta yi wa Fatima bayan ta bar mata sallahun abubuwan da zata gudanar a gidan kafin ta dawo.

Tafiyar mintuna ashirin a cikin a daidata sahu ya isar da ita unguwar mak'era, a hankali ta dunfari babangidan mai dauke sa babbar k'ofa hadi da babban zaure.

Family hause ne mai dauke da dakuna masu yawan gaske, kai tsaye ta nufi cikin gidan gabanta na fad'uwa sai dai ta dake, don babu alamun hakan a fuskarta.

Kasancewar safiya ce yawancin matan gidan na tsakar gida kowacce na gudanar da sabgar gabanta, sallamar da ta yi ne ya janyo hankalin mafi aksarin jama'ar dake tsakar gidan.

Kamar wata sabuwar halittta haka wasu daga cikin matan suka Shiga kallonta fuskokinsu dauke da tarin mamaki, yayinda bakin fuskoki a gare ta ke binta da kallon rashin sani.

D'aya daga cikin matan ne ta kasa jurewa sai da ta maganta, cikin tu'ajjabi ta ce "Wa nake gani haka Lamar Balkisu? Na kusa da ita ce ta amsa da " Taya ni fada dai, ashe ba gizo bane. Tsaki d'aya daga cikin su ta ja tare sa cewa; Allah ya wadaran naka ya lalace, dai dai lokacin kuma d'aya daga cikin mazan gidan ya sawo kai jin kananun maganganu na tashi daga matayen nasu wadanda dama kullum basu rabo da hakan.

Turus ya yi da farko lokacin da ya yi arba da ita, sai dai daga bisani ya wani irin hade rai kamar hadarin gabas, a kausashe cikin zare jajayen idanunsa ya ce "Meya kawo ki gidan nan Balkisu, Ashe ba mun yi miki kashedi sake rabar inuwarmu ba, shin ke mayya ce, to wallahi wallahi billahillazi la'ilaha illah huwa idan kika kara, minti biyu a cikin gidan nan sai na yi miki mummunar lahani.

Wannan haniyar ta Yaya Al-hassan kamar yadda suke Kiran shi ita ta janyo hankalin kafatanin sauran muatane gidan dake dakunansu, suka Shiga firfitowa d'aya bayan d'aya.

Gyaran muryar da aka yi daga bayansu yasa duk suka maida hankali gurin, sabanin Hassan fuskarshi washe ta ke da wani irin shu'umar murmushi, ............

Oum ummretarh

09116099486
[12/29, 2:50 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀

~FARHAT~

*PAGE 42*

Mikiya Writers Association

*Masu facebook ku yi following wannan account ɗin domin samun damar cin giveaway ɗin da muke yi, da kuma tattaunawa akan yanayin rayuwa*

https://www.facebook.com/naeemerh.suleiman?mibextid=ZbWKwL

"Ka barta Hassan, ka barta mu ji da me ta ke tafe." Yaya babba ya fad'a a gadarance, cike da umarni, Al-Hassan dake huci kamar kububuwa ya juya ya kalli inda sautin muryar d'an uwan nashi ke tashi, ya ce "Yaya ka yi hakuri ka barni in ci mata mutunci, in wulakantata, kamar yadda na yi mata alkawari duk ranar da na sake ganin kafarta a cikin gidan nan zan yi mata.

" Ka bari na ce Hassan" cewar Yaya babba, bayan ya k'araso kusa da Al-hassan d'in, daga haka ya juya ya nufi falon shi ba tare da sake cewa komai ba, wani irin huci Al-hassan ya dinga furzarwa yana bin Ummi da wani irin wulakantaccen kallo mai dauke da tsantsar tsana, daga bisani ya juya ya bi bayan dan uwansa a fusace.

Jiki babu kwari Ummi ta k'arasa madaidaicin falon mai d'auke da satin kujeru da k'aramar TV, guri ta nema ta zauna daga can gefe bayan tayi musu sallamar da cikinsu babu wanda ya amsa mata.

Shiru ya ratsa falon na y'an wasu dak'ik'ai, Yaya babba ne ya katse shirun ta hanyar cewa; Ke muke saurare Balkisu me ya kawo ki garemu, bayan mun riga mun gaya miki babumu babu ke har abadan da'ima."

Dagowa ta yi ta kalle shi idanunsa kem a kan ta, yana binta da wani irin mayen kallo kamar zai cinyeta da ido, da sauri ta d'auke kanta a zuciyarta tana neman tsari daga sharrin shi, domin bata manta waye Yaya babba duk da shekaru sun ja.

Cike da fargaba da tsananin fad'uwar gaba, ta samo gabatar musu da abin da ke tafe da ita, tun kafin ta k'arasa Al-hassan dake binta da mugun harara ya daka mata tsawa, a kausashe ya ci gaba da cewa "Ban ta6a sanin ke dabba ba ce, a cikin dabbobin ma tunkiya marar hankali ba sai yau Balki! Kina nufin ni ko d'aya daga cikin ahlina ne za mujelup nemar wa shegun y'ay'anki aure? Lallai kwakwalwar kan ki iri d'aya ne sak dana jaka shiyasa ta baki wannan shawaran na ki tunkare mu da wannan maganar. To ki sani har gaban abada babu gamin mu da shegun y'ay'anki, y'ay'an zina tsintattun y'ay'an kwararo........

" Ya isa Hassan ya isashe haka!!!" Ummi ta fada da wani irin murya mai kaushin gaske, tuni idanunta sun juye sun yi jajur, ga hawaye da tuni ya gama wanke mata fuska, Mikewa tsaye ta yi ta ci gaba da cewa a tswace "Kada ka kuskura ka sake sheganta mini y'ay'a, kada ka kuskura na ce maka, y'ay'ana ba shegu ba ne ina ji a jikina y'ay'ana y'ay'an halak ne tsarkakku!!! Ta k'arashe maganar tana nuna shi da yatsa idonta kem! Cikin nasa babu alamar tsoro ko shakkarsa a ciki sai ma tsagwaron tsana a cikinsu.

Mikewa ya yi a fusace ya iso gabanta yana cewa " Ni kike nunawa yatsa, ni kike yiwa ihu Balki! To na sake fad'a cewa y'ay'anki y'ay'an zina ne shegune me zaki yi??? Saukar miyan bakinta a fuskarta ya dakatar da shi daga hargagin da yake yi, a fusace ya daga hannu zai wanke mata fuska da mari, caraf! Yaya babba ya rike hannayensa ta baya, "koma ka zauna Hassan." Yaya babba ya ba shi umarni, bai zauna d'in ba sai kawai ya fice daga d'akin yana kwafa, zuciyarsa na tafarfasa

Bayan fitar Hassan, Yaya babba ya maida kallonsa ga Ummi data durkushe a wajen tana kuka mai tsuma zuciya, shu'umar murmushi ya saki, kafin ya bita ya tsuguna shima , cikin kasa-kasa da murya kamar me rada, ya fara cewa "Duk da shekaru sun ja, kina nan a balkisunki kyakkyawar mace fara kal, d'anya sharaf mai dauke da tarin baiwarwaki, kwata kwata baki tsufa ba balki, har yanzu ina nan da kudirina a kan ki, ki amincemin koda sau d'aya ne na cimma muradina a kan ki ni kuma na miki alkawarin zan tsaya miki da ke da y'ay'anki har duniya ta nad'e muddin ina numfashi.

An yi ta babu dad'i sosai a gidan, domin sun yi musayen maganganu a tsakanin su,Ummi ta kauda ido ta wanke Yaya babba tas ta kira shi da fasiki dan akuya, kasancewar Tana cikin bakin ciki da bacin an sheganta mata y'ay'a da Hassan ya yi.

Sosai ran Yaya babba ya 6aci, Inda ya dauke mummunan kudiri akanta idea da shegun y'ay'anta, ita kuma ta kalli cikin idanunsa ta sanar masa ta Allah ba yasa ba da Allah ta dogara, da su nemarwa yayanta aure da kar su nemar musu duk daya a gareta Allah yana nan kuma bazai ta6a bari su wulakanta ba, a karshe haka Ummi ta kamo hanya gida, babu nasara sai tarin bakin ciki da ta k'unso tare da tayar mata da tsohon mikin da ta dad'e da lullu6eshi a can karkashin zuciyarta.

Su hudu ne y'an uwan marigayi mijinta Al-husssain. Mata biyu maza uku Yaya Tanimu wanda suke kira da yaya babba kasancewar shine babba a cikin su, sai Hassan sai hussain da yake mijinta, sai mata biyu wadanda ke gidajen mazajensu kowacce ta tara nata iyalin.

Kaddarace ta jeho ta cikin ahlinsu ba tare da ta san sanda ta giffa a gare ta ba, ta yi gwagwarmaya sosai a lokacin duk da karancin shekarunta, ta kowane bangare ta fuskanci kalubale rayuwa, duk don kasancewarta tsintacciya mara galihu, Mara gaba Mara baya wacce bata san inda ta dosa ba.

Tanimu mutuncinta yake nema ido rufe yake so ya keta mata haddi tun kafin su yi aure da marigayi, ta dauka aurenta da dan uwansa zai sa, ya rabu da ita , sai dai hakan babu abinda ya rage a kan irin bibiyar da yake yi wa mutuncinta saboda rashin tsoron Allah har da igiyar aurenta, igiyar aurenma na dan uwansa, sai dai har mijinta ya kwanta dama bai samu galaba akanta ba hakan ya haifar mata da mummuna tsana da tsamgwama daga gareshi, zata iya cewa shine ya fara hura wutar kiyayya tsakanin sauran kannensa da marigayi wanda suka dauki karan tsana suka dora mata acewarsu itace silar mutuwar dan uwansu, yayinda kiri-kiri suka sheganta mata y'ay'a, y'ay'an da bata san daga ina suke ba, kawai ta bud'e ido ne ta ganta a tare da su.

Ta dauka zuwa yanzu Tanimu ya saduda, tunda shekaru sunja, bata ta6a tunani ko hasashen cewa zai kuma tayar da wannan maganar ba, sai gashi yana sake baiyana mata har yau yana nan da muradin tarayya da ita, wa'iyazubilla.

Ta yi kuka ta yi bakin cikin wannan lamarin don sai da ta kwashe kwana uku tana zazzabi a tsaye saboda jimamin wannan lamari, bata cewa Al'ameen komai a kan lamarin, haka shima bai ce mata ba, sai dai shirun shi ba yana nufin bai damu bane, daurewa kawai ya ke, kullum suna tare da Aliyu shine ya ke don karfafa masa gwiwa da bashi baki, a bangare daya kuma suna nan suna wani shiri shi da Dr Abdul wanda Al'ameen din bai san da shi ba, don tun ranar da Aliyun ya mishi maganar shi suka rabu baran-baran bai kuma ambaton sunan shi ba, wannan kuma umarnin Dr din ne.
Chapter 44 · 0% Book details