← Book details Joy Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 46

Sashe 27

Joy Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fashewa ta yi da wani irin kuka, da gudu ta k'arasa gare shi, a gaban shi ta tsaya cikin kuka da kid'ima ta ke cewa "Na shiga uku na lalace! Yaya Alamen ka yi hakuri, Peter mu kai shi asibiti, Yaya Alamen ka zo muje asibiti pls jini yana zuba a jikinka." Riko hannun shi ta yi ta soma kokarin jan shi, gaba d'aya ta rud'e bata cikin hayyacinta.

Duk da yana cikin halin ciwo, sai da ya ji Yarrrr!!! A jikinsa lokacin da hannunta ya sauka a kan nasa, da sauri ya saka hannusa d'ayan ya 6an6are hannunta daga nasa.

Jin haka yasa ta dago da jikakkun idanuta ta sauke a fuskar shi, karaf! Suka su ka sauka cikin na shi kaifaffun idanun da suke rine, tuni zuciyarta ta shiga wani irin dokawa da wani irin speed,wasu irin sinadarai masu kama da surkulle ke fitowa daga idanun shi suna shiga na ta direct ba tare da wani shamaki ba, kasa janye idanu ta yi daga cikin na shi, duk da irin kaifin da suka mata.

Kayataccen murmushinsa ya sakar mata, ya girgiza mata kai, murya kasa-kasa ya ce "I'm ok' ba sai kin kai ni hospital ba thank yhu for Ur care." Daga haka ya juya ya ci gaba tafiya yana d'ingisa kafarsa ta hagu.

Kamar a sume kuma ba a sume ba, haka ta dinga jin kanta, bata farga da ya bar wajen ba sai da ta tsinkayi muryar Peter yana cewa "Miss ar u ok." Firgigit ta yi ta kalle shi, ta sake kallon hanyar da al'ameen ya bi, ji ta yi wani kuka mai karfi ya taho mata from no where, da gudu ta wuce shi ta bude motarta ta fada tare sa fashewa da kuka.

Jiki a matukar sanyaye Peter ya bude motar ya shiga mazauninsa, ya tada motar suka bar wajen, zuciyarsa cike da tausayin uwar dakinsa.

*************

Karfin hali da jarumta ce kawai da kuma taimakon Allah suka karasa da shi gida, zuwa lokacin tuni kafar ta kumbura, baya son ya tadawa su Ummi hankali hakan yasa bai nufi cikin gida ba ya tsaya dakin shi.

Karar taba kofar dakin ne ya jawo hankalin Fatima dake tsakar gida, da sauri ta leko don ganin ko waye tunda dai ta riga ta san yayanta ya fita, kuma muddin ya dawo sai ya shigo cikin gida kafin ya nufi dakinshi, sai dai ga mamakinta shi din ta gani tsaye idanun shi a rintse ya cike lips yana kici kicin soka key a jikin padlock.

"Yayana." Ta furta tana karasawa gaban shi, sai lokacin idanunta suka kai ga kujewar dake gefen fuskar shi da gwiwar hannun shi da ke zubar jini, zaro idanu ta yi a rude ta ce "Subhanallahi! Yaya me ya sameka?" Kafin ya bata amsa ta hango kumburan da kafar shi ta hagu ta yi, "Innalillahi wa inna ilaihi rajiun! Na shiga uku!" Da sauri ya bude rinannun idanunsa jin zata yi masa kwarmato, cikin karfin hali ya yi mata alamar shiii! Da hannu, girgiza mishi kai ta yi tana hawaye sai kuma ta juya ta runtuma da gudu, "Ya Salam!" Ya furta akan labbanasa, ya fahimci gaba daya ta rude ne kuma yasan Ummi zata je ta gayawa, sam baiso ba sanin da ya yi Ummi bata jin dadi yau.

Allah sarki uwa! A kwance take amma jin abin da Fatima ke fada tuni ta mike zaune, kafin Fatima ta kai aya, ta mike kan kafafunta, ta yo gaba, Fatima ta rufo mata baya.

"Subhanallahi! Yayan Fatima me ya faru haka, innalillahi wa inna ilaihi rajiun!" Ta fada cikin tashin hankali ganin yadda kafar shi ta kumbura, "Fatima amshi makullin ki bude kofar." Fatima dake sharar kwalla ta amsa key a hannun Al'ameen ta bude kofar, dakyar ya iya daga kafa ya shiga ciki, Ummi da Fatima suka rufa masa baya, kwanciya yayi, don bazai iya zama ba, Ummi ta sake cewa "Ko dai asibiti zamu je Al'ameen?" Dakyar ya girgiza mata kai yana cike lips Cike da azaba, sannu suka shiga rige-rigen yi masa.

Sake kallon kafar Ummi ta yi dakyau ta ce "Wannan kafar taka akwai targade, Yayan Fatima. Binta yi maza ki je gidan Mallam Surajo mai dori ko yana nan"

Da gudu Fatima ta fice, Ummi kuma ta zauna tana yi masa sannu, daurewa kawai ta ke yi kar ta zubar da hawaye.

Minti sha biyar Fatima ta yi sallama, Mallam Surajo biye da ita, fitowa Ummi ta yi a dakin suka gaisa sama-sama ta ce "Mallam yaro ne ya shigo yanzu da kafa a kumbure, shine nace ta kira ka ka duba ina ganin kamar targade ne." Ya ce "Assshha! To bari a duba, Allah kiyaye gaba." Daga haka ya shiga dakin Al'ameen din.

Kamar yadda Ummi ta yi hasashe targaden ne kuwa. Babu bata lokaci Mallam Surajo ya hau aikinsa, duk da cewa kafar bata yi mugum tsami ba, Al'ameen yaji jiki, rintse idanu kawai yayi yana ambaton sunaye Allah.

Ummi kasa tsahuwa ta yi a baki kofar jin hawaye na shirin zubo mata da sauri tayi cikin gida, Fatima kam kuka take wiwi ta aza hannu aka.

Bayan wasu mintuna Mallam Surajo ya kammala aikinsa, fitowa yayi ya tarad da Fatima, ya ce "Yan mata ki gayawa innarku an gama." Ta amsa da to , ta shiga ciki, tare suka dawo da Ummi.

"Mallam ashe har an kammala, to mungode Allah ya saka da alkhairi, ga wannan ayi hakuri." Cewar Ummi tana mai mika mishi naira dubun dake hannunta, amsa ya yi, ya ce "Nagode Hajiya, an kammala an daure kafar nan da kwana hudu zan zo a kwance, an ma yi sa'a baiyi tsami sosai ba ku ka kira ni, Allah ya bashi lafiya." Da "Amin ya Rabbi!." Ummi ta amsa mishi, suka yi sallama ya tafi.

Jiki a sanyaye Ummi ta tura kofar dakin ta shiga, cikin hukuncin Ubangiji barci ya dauke shi, sai dai kallo daya zakasan barcin azaba ne, duk ya hada uban gumi.

Labulen window ta dage ma shi don ya samu iska, daga haka ta fice daga dakin.

Awa biyu ya kwashe yana barci kafin ya farka, zuwa lokacin zafin da bacin ran dake tattare da zuciyarsa game da abinda Dr Abdul ya yi masa ya ragu kaso hamsin cikin dari. Shiru ya yi yana tunanin abinda ya faru da shi yadda accident din ya afku da abinda ya biyo bayan afkuwarsa, bai san dalili ba sai ya samu Kansa da sakin tattausar murmurshi a fila ya furta "Matsociya." Sallamar Fatima ya katse ma shi tunani, ganin shi a farke yasa ta saurin karasowa cikin dakin, a gabashi ta zauna tare da cewa "Sannu Yayana ka farka ya jikin?" Murmushi ya yi mata a hankali ya ce "Alhmdllh kanwata." Mikewa ta yi tana cewa bari na gayawa "Ummi ka farka." Tare suka dawo da Ummi, gefen katifar shi ta zauna, cike da tausayawa ta ce "Amintacce ka farka, yaya jikin?" Ya ce "Ummina da sauki." Ajiyar zuciya ta sauke ta ce "Garin yaya kaji ciwo haka?" Shiru ya dan yi kafin ya ce "Accident na samu mota ce ta kade ni, amma ba wani mugun kadewa ba kawai dai abin yazo da tsautsayi ne." Girgiza kai ta yi cike da alhini, ta ce "A ina ne?" "A cikin unguwa ne, na kamo anya ina dawowa gida." "Asshha!Ubangiji ya kara kiyayewa."

Ranar Al'ameen a gida ya wuni Ummi da Fatima na jinyar shi ko kwakkwarar tari ya yi su yi ta rige -rigen tambayar shi lafiya me yake bukata, tausayinsu ya kara lullube zuciyarsa, ya kara tabbatarwa duk duniya bashi da kamar su.

***********

*Amira*

Yinin ranar haka ta yi cikin rashin walwala da faduwar gaba, kullum da tunanin shi ta ke wuni, sai dai yau duk sanda ta tuno shi sai gabanta ya yanke ya fadi, yau kimanin kwana uku kenan rabon da ta saka shi a idanunta, takan shiga gidan kullum kamar yadda ta saba sai dai ta lura kamar yana kaucewa haduwar su da gangan ne, yau kam tana jin idan bata saka shi a idanunta ba baza ta iya rintsawa, hakan ya sa ta shirya abin da zata fada a gida don a barta fitowa.

Misalin karfe takwas na dare ta yi sallama a tsakar gidan, Fatima na wajen Al'ameen don haka Ummi kadai ta tarar a daki, zama ta yi a saman dardumar da ke shimfide a tsakar dakin, a mutunce kamar ko da yaushe ta ce "Barka da dare Ummi mun wuni lafiya." "Lafiya kalau Amira, ya dare ya exam." "Alhmdllh Ummi, an gode Allah." "To Allah ya dafa ya bada nasara." "Amin Ummi nagode." "Ya su Maman Amira, da sauyan yan uwa." "Duk suna nan kalau." "Ma sha Allah kya isar min da gaisuwa." Daga haka su ka zauna shiru na dan mintoci, Ummi ta yanke shirun ta hanyar cewa "Ya akayi ne Amira naga kamar ki na son yin magana." Kasa ta yi da kai ta ce "E Ummi dama wajen Fatima na zo kuma naga kamar bata nan." "Ayyo Fatima na wajen Yayanta, da yake dazu ya samu tsautsayi a kafa." Rass! Rass! Haka gabanta ya yanke ya fadi, bata san sanda ta dafe girji da sauri ba, cikin rudewa ta ce "Subhanllahi! Na shiga uku! Meya same shi, Allah yasa ba mummunar rauni ya ji ba?" Shaf ta mance da Ummi take magana.

Ganin yadda Ummi ta zuba mata idanu yasa ta ji wani kunya ya lullu6eta, da sauri ta yi kasa da kai don gani ta yi kamar Ummi taga abinda ke zuciyarta, basarwa Ummi ta yi ta ce "Wallahi d'azu ne yana dawowa gida mota ta kade shi har ya samu targade a kafa, amma da sauki an gyara an daure kafar."

Dakyar ta iya ce wa "Allah sarki! Ubangiji ya ba shi lafiya." Ummi ta amsa da "Amin." Daga haka shiru tayi zuciyar ta ya raunata ji take kamar ta zubar da kwalla amma ta daurw saboda a gaban Ummi take, ranar kasa sakin jiki ta yi suyi hira da Ummi kamar yadda su ka saba ta yi,duk da yadda Ummin ta dinga kokarin jan ta da hira, ita kanta Ummi ta fahimci tana cikin tashin hankali.
Chapter 27 · 0% Book details