Sashe 36
Joy Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zaunar da ita a bakin kafitarsa ya yi ya tsuguna a gabanta, ya ce "Fatima Menene?" Cikin shessheka ta ce "Yayana Anty Amira, da gaske ne?" Gabansa ne ya fad'i, k'ura mata idanu ya yi, kafin ya ce "Kin fad'awa Ummi ne?" Ta girgiza kai. Boyayyar ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa; Kar ki gaya mata kin ji kanwata hankali ta zai tashi sosai." Gyad'a kai ta yi alamar to, sai kuma ta hade hannayenta alamar rok'o ta ce cikin kuka; Yaya dan Allah ka so ta, dan Allah ka tausaya mata ka kaunaceta wallahi tana son ka matsanancin soyayya Yaya ina tsoron kar mu rasata ta dalilinka, idan ka yi haka ka yi ceton rai, kuma na tabbata Ummi zata fi kowa farin ciki da hakan, idan kuma ta samu labarin ciwon Amira na da alaka da kai na tabbata zata fi kowa bakin ciki, Yayana don Allah karka ce A'a, ko dan ni da Ummi ka kaunaci Anty Amira baza ka yi nadama ba.." Hannayenta dake hade ya kama ya rike gam! da hannyensa yana jin maganganunta na ratsa kwakwalwarsa take idanunsa suna karasa rinewa, cikin matsanancin kuka ta ci gaba da cewa "Don Allah Yayana, don Allah pls kar ka ce A'a, ko dan ni da Ummi, ba baka da tam karmu muma bamu da ya kai." Kalaman data yi ta maimaitawa kenan idanunta a rufe tana hawaye har sai da ta ji ya ce "Is ok Fatima, is ok naji na Amince." Cak! Ta tsayar da sambatu da kukan da take yi ta dago ta kalle shi idanu jaga-jaga da hawaye ta ce a sanyaye "Da gaske Yayana." Ya gyada mata mata kai tare da sakar mata murmushin karfin hali. Fad'awa jikinsa tayi tana sakin dariya mai sauti hawayen farin ciki da kaunar tilon dan uwanta na kwaranya a idanunta, tallefe kanta ya yi shima yana jin kamar ya yi wahayen.
Sun kusa minti goma a haka, tun tana shessheka har ta koma sauke ajiyar zuciya, jin ana shirin tayar da sallar isha'i yasa ya sake ta, ya kalleta ya ce, "Ina rokonki Fatima ki yara daren yau wajen taya ni neman za6in Allah, ni ma yau zan gabatar da istikhara akan lamarin kome ciki Allah zai dafa mana." Gyada kai ta yi ta ce "In sha Allah Yayana." Mikewa ya yi ya ce ki shiga gida nima zan ta fi masallaci.
Koda ta shiga gida bata nunawa Ummi komai ba, alwala ta yi ta gabatar da sallar magriban da batta yi ba ta daura sa ishan da ake kira.
Kamar yadda Al'ameen ya roketa ranar daga ita har shi kusan kwana suka yi a bisa sallaya suna kai kukan su ga Mahalicci.
Washegari
**************
Ajiyar zuciya Dr Abdul ya sauke bayan ya gama sauraren jawabin dan matashin yaron da bai gaza tsaran Al'ameen ba ya gama yi masa, sake kallon yaron ya yi da kyau, ya ce "Aliyu ko?" Gyada kai Aliyu ya yi, Dr ya sake cewa "Thank u Aliyu!" K'arara mamaki ya bayyana a fuskar Aliyu, shi da ya zo ban hakuri da neman taimako ana yi mishi godiya, goron ruwan faron dake kan table Dr Abdul ya dauka ya bude murfin ya kur6a kadan ya mai da murfin ya rufe, kallon Aliyu ya yi ya ce "Nasan kana mamakin dalilin da yasa na yi maka godiya ko." Aliyu ya gyada kai, Murmushi Dr ya yi yace "Saboda ka rage mini aiki, sam! Ban yi fushi da Al'ameen ba domin da baka zo ba ina daf da bin sahun shi, jira nake wa'adin dana d'aukar masa ya cika, sai ga shi kai ka fanshe shi, na jinjina maka lallia ka cika Amini na kwarai kuma ina da tabbacin zaka taimakeni a kan abin da na saka a gaba na alkhairi." Shiru ya yi kad'an kafin ya daure da " Aliyu na fi ka son na taimakama Al'ameen, amma na rasa irin taurin kan shi, sometimes na kan zauna ni kad'ai na dinga tunanin irin karfin hali da taurin zuciyar shi, ko da yake ance ma gaji ma fiyi, ada ni kad'ai na me gwagwarmayar nan yanzu gaka ka shigo ciki, don haka zamu had'a karfi da karfe! Yanzu dai abin da ya kamata mu yi, shine mu samu ya amince da maganar auren domin a yanzu shi ya fi komai mahimmanci, idan muka yi sanya, ina mai tabbatar maka daga nan zuwa ko wani irin lokaci zai iya haduwa da mummunan attack wanda idan ba'ayi da gaske ba zai iya shiga wani mummunan garari ko kuma ya rasa rayuwarsa ma baki d'aya." "Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun!" Shine Kalmar da Aliyu ya furta a baiyane cikin tsantsar tashin hankali, "Dr yanzu menene abin yi?" "Ka bi duk hanyar da zaka bi wajen ganin ka tirsasashi ya amince da batun auren yarinyar nan." Cikin tashin hankali ya ce "Zan yi Dr, zan tirsasashi ko zai amince' dole zai amince." "To shikenan Aliyu zan kar6i lamabarka saboda ina son sanin duk halin da ake ciki." Canjen lambar waya suka yi daga haka suka yi sallama Aliyu ya tafi.
***************
Washegari ya kama asabar babu school, misalin karfe tara na safe Al'ameen ya shiga d'akin Ummi cikin shirin shi na tafiya wajen neman halalinsa ya sha kyau cikin wani yadi milk, dinkin karamin riga mai guntun hannu da wando babu hula akansa don ba abocin sakawa bane, duk suna falo Ummi ta maida hankali tana sauraren wa'azin Dr jabir mai hula a tashar Afrika TV 3, yayin da Fatima ke zaune daga can sak'on kujera, kallo daya zaka san tana tattare da damuwa, idanunta sun yi luhu luhu alamar rashin barci, sallamar sa ne ya dawo dasu duk hayyacinsu. Ummi ta ce cikin fara'a bayan ta amsa sallamarshi, "Amintacce har an fito." Murmushi ya yi ya ce "E Ummi na fito a yi mini addu'a." Ya karashe maganar yana rage tsawo a gabanta.
Kan shi ta dafa ta ce "Ubangiji ya tsare gabanka sa bayanka ya yi maka albarka ya saka maka Albarka cikin neman ka ya jikan mahaifinka." Cikin wani irin yanayi ya amsa da "Amin Ummi." Tare da mikewa tsaye, ya kalli Fatima da itama shi take kallo ya ce "Kanwata muje ki min iso na shiga na dubo jikin Amira." Daga yadda fara'a ta fadada a fuskar Ummi ya tabbata ta ji dadin lamarin sai ya tsinci Kansas cikin farin ciki shima, Fatima kam wuf! Ta yi ta mike fuskarta dauke da madaukakin farin ciki........
Oum ummeetarh
09116090468
[12/29, 2:45 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀
~FARHAT~
*PAGE 33*
No editing 😤
Cike da zumud'i Fatima ta zura dogon hijabinta, bakinta washe kamar gonar auduga ta ce "Yayana muje." Ya gyada mata kai tare da k'ara yin sallama da Ummi suka fito. Tana gaba yana biye da ita har k'ofar gidan, a nan ya dakata ita kuma ta k'arasa ciki bakinta d'auke da sallama, a tsakar gida ta tarad da Maman Amira da Aysha da sauran k'annen Amira, Mama ta fara gaisarwa tare da tambayar mai jiki, sannan suka gaisa da Aysha wacce suke kusan sa'anni, sauran yaran suka gaisheta.
Wuri ta samu ta zauna a dakali, ta kalli Mama ta ce "Mama Yaya Ameen ne yace na mashi iso yana son ya shigo ya duba Anty Amira da jiki." Mama ta ce "Assha! Aminullahi ne da neman iso dan zai shigo gidan nan, jeki maza ki ce ya shigo, ke kuma Aysha gayawa Amiran zuwan Aminullahi." Kusan a tare Fatima da Aysha suka amsa mata da to Mama.
Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya bi bayan Fatima, da ta juya bayan ta isar masa da sa'kon Mama, Bakin sa dauke da cikakkiyar sallama ya saka kansa cikin dan madaidaicin tsakar gidan, dai dai lokacin Aysha ta fito daga d'akin Mama tana cewa; "Mama Anty Amira fa ta samu barci." "Barci kuma? ikon Allah! Yanzu fa na barota ido biyu." Cewar Mama tana kallon Fatima da ke tsaye tana jiran k'arasowar Al'ameen.
Sallamarsa ne ya karad'e musu kunnuwa kusan a tare duk suka amsa, gefen Mama ya risina cike tsantsar ladabi da kamun kai ya ce "Mama ina kwana." Da fara'a ta amsa da "Ina gajiya Aminullahi, ya harkoki ya karatu." "Alhmdllh Mama ya jikin Amira." "Hmmm! Jiki da sauk'i Aminu sai hamdala." Ta fad'a muryarta cike da rauni. "Allah Ubangiji ya bata lafiya." "Amin ya rabbi, Mai jikin ma ta samu barci, idan ta farka zan sanar da ita zuwan ka." Ya amsa da " Ayya ba komai Mama, a gaisheta idan ta farka, idan na dawo da wuri zuwa dare zan sake shigowa in sha Allah." "To to!! Aminullahi Allah ya kaimu daren an gode sosai, Allah ya yi Albarka." Da Amin ya amsa tare da mik'ewa ya fice.
Fatima ma bata dad'e ba ta yi musu sallama ta tafi tare da Alkawarin sake shigowa anjima. Kamar almara tana fitowa daga gidan ta yi kicibis da Joy.
Da fara'a suka tari juna, Fatima ta ce "ya akayi kika fito da sassafen nan, yau Saturday." Murmushi ta yi kafin ta kai bakinta dai dai saitin kunne Fatima cikin rad'a ta ce "Na zo ganin Handsome Yayana ne, na yi masa godiya a kan, turaren da ya siya mana, yanzu zan koma kafin Mom ta nemi ni." Dariya Fatima ta yi, Idan da sabo ta sabo da jin ire iren sunayen nan kala kala daga bakin kawar tata da take kiran Al'ameen da su, sai dai bata ta6a daukarsu da wata manufa ba, ta bar hakan a matsayi kirkin da yake gwada mata shima, yana kula da ita sosai ya daukesu duk daya, sometimes har tsaraba yake musu a tare, tun bayan da hargitsin nan ya lafa ta lura da irin yadda Joy din ke matukar girmama lamarin da ya shafe shi, ko fira suke idan na shi ne ta fi maida hankali, kullum zancen ta Yaya Ameen kaza Yaya Ameen kaza, takan yi mamakin yadda lamarinsu ya juye daga kiyayya da kushe juna zuwa yabo da girmamawa hadi da tsantsar kulawa.