← Book details Joy Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 46

Sashe 13

Joy Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

20 minute kacal ya kwashe ya fito sanye da jallabiya, dakin shi ya nufa ya shirya cikin kana nan kaya ya dawo, abincin shi Fatima ta dauko mai, ya kalleta ya ce "zauna muci tare." Ummi ta ce "yawwa kamar kasan yau ta ki cin abinci kwata kwata dama jira name ka dawo ba gaya maka." 6ata rai yayi ya ce "me yasa Fatima." Tayi narai narai da idanu, babu alamar wasa a sautinsa ya ce "oya let it." Ba musu ta dauko cokali ta saka suna ci, ganin tana wasa yasa ya Shiga bata da kanshi a baki, hakan ba sabon abu bane a wajensu dama, sai da ya tabbatar ta koshi sannan ya dauko Apple dinta ya bata, nan ta ke ta shi ga fara'a tana godiya, ya ji dadin gani yadda ya sake take farin ciki,nan ta wanko ta ba ummi daya ta dauki biyu, tana ci yana janta da hira, labarai masu ban dariya har da su tasuniyar gizo, Ummi ma ta biye musu tana saka musu baki, kan kace koba Fatima ta wartsake duk wani damuwa dake damunta ya kama gabanshi, sai lokacin take tunawa da batun Amira, kallon Ummi tayi tana gatsar Apple ta ce "dazu Anty Amira ta shigo." Ga mamakinta gani tayi Ummi ta washe baki ta ce "Allah sarki Amira yarinyar kirki, kai yarinyar nan tana da hankali wallahi, na Dade banga budurwa mai natsuwa da hankalin ta ba." Fatima ta ce "Hmmm Ummi ita fa ta share gidan nan ta cika drum da ruwa, ta zauna ta tayani hira sosai, Ummi dama ta saba zuwa ne." Ummi ta ce " ta kan shigo jefi jefi cikin kwanakin nan idan kuna makaranta da yake ita suna hutu kafin su fara zana waec, tana shigowa idan babu kowa a gidan su ta kama mini aiyuka ta tayani hira har wankin kayana tana yi min, kuma ko na ce ta bari bata bari, yarinyar ba dai hankali ba. Haka Ummi ta yi ta yabon Amira Al'ameen na jin su, bai dai tanka ba,sai gurin sha daya sauran suka ta shi.

Pls comment yan Amana, comment dinku shine karfin gwiwana wollah, idan kina comment zaku ringa samun update a kai a kai😬
[12/29, 2:34 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀

*PAGE 11*

Yau kimanin mako biyu rabon Fatima da school, a cikin wad'anan y'an kwanakin Al'ameen ya yi kokari sosai wajen ganin bai bar barta ta shiga damuwa ba, ya zaunar da ita tare da sakawa ta daukar mai alkawarin akan baza ta sake zuwa gidan su Joy, kuma daga yau babu maganar kawance a tsakanin su ya kashe har abada, da farko ta shi ga damuwa amma daga bisani ganin yadda ya nunka kulawar shi a kanta yasa cikin kwana uku ta ware ta nuna komai ya wuce ta hakura, sai dai na ciki na ciki, kusan kullum sai ta shiga toilet ta sha kuka idan ta tuna da Joy, damuwarta d'aya har yau bata san halin da take ciki ba, kewar ta take ji kamar kamar me.

A bangaren Joy ma kusan haka ne sai dai ma mu ce har gara Fatima. Sosai Mom ta saka mata matakan tsaro bata zuwa ko ina, daga school sai school, kuma shima ita take sauke ta da kanta idan an tashi ta biya ta dauko ta, duk wata kafa da zata bi ya sadata da Fatima Mom ta to she shi, ga Papa ya yi tafiya zuwa Japan tun last week dama shi ba cikakken mazauni bane da wuya yayi zaman sati biyu a k'asa ba tare da yayi tafiya ba saboda harkokin kasuwancin shi, iya damuwa ta shige shi har ta kai yanzu bata tsinana komai a class bata maida hankali kan karatu bata jan note ga shi suna daf da fara mid term test.

Duk halin da take ciki Mom ta sani, tun cikin last week ta yi bincike ta gane Fatima ta bar school din, hakan ya mata dadi kamar ta zuba ruwa a kasa ta sha don murna, da gangan ta hanata duk wata dama na fita ita kadai don kar ta samu damar zuwa gidan su Fatima, uwa uba kuma security da ta saka Papa ya zuba musu a bakin get, har guda hudu babu mai ikon shiga ko fita daga gidan sai da sanin Mom.

A haka makonni suka sake shud'ewa, ana sauran 1 week su fara test, Joy ta rasa yadda zata yi, saga da marwa ta ringa yi a dakin ta, duk wani dabara da zata yi don ta bar gidan ta gwada babu sa'a , wani tunani ne ya fad'o mata a rai, ta ke wani farin ciki ya lullu6eta, da sauri ta dauko note book dinta da biro ta zauna a kan bed ta shiga rubutawa Fatima letter, kalamai ne kad'an na ban hakauri tare da nuna yadda take tsakanin kewa da kaunar ta, ta k'ara da batun fara test din su next week tare da rokonta akan ta daure ta yi mata replay, a kasan tayi drowning din hearts guda biyu daya cikin daya kasancewarta gwanar drowning take ya fito share kaar ba hannu ya zana ba, a ciki ta rubuta sunayen su, a kasan hearts din kuma ta rubuta friends forever cikin wani salo mai kyayatarwa.

Ninkewa tayi ta bude Jakarta ta dauki kudi kimanin dubu goma, ta boye a cikin aljihun pencil wandonta ta sake rigarta mai hannu bes wanda ya kai mata gwiwa ta fice daga dakin, sai da ta fara leka Mom ganin ta maida hankali tana danna system yasa ta fice da sauri direct counpuond ta fito, ma'aika nata gaisheta, da fara'a take amsawa tare da kiran sunan kowannen su, hakan na musu dadi, suna son Miss Joy sosai kasancewarta mai fara'a da sakin fuska bata da wulakanci da izza ko kadan sabanin mahaifiyarta da take ji kamar ita ce ma mai dukiyar ba Papa ba. In da ta hango drivernta Peter zaune shida gardener na gidan ta nufa, da fara'arta, ganin ta yasa Peter tasowa da sauri ya tare ta bayan ya kwashi gaisuwa ya shiga tambayarta za'a fito da mota ne. Girgiza kai ta yi ta ce "Peter wani taimako nake nema a wajenka, idan babu damuwa zan dan aikeka nan babu nisa amma bana son Mom ta san da maganar." Washe baki yayi yana kallonta, saukin kanta na kara mata kima a wajen shi, ji yadda take mai maganar don zata aike shi kamar ba zamanta yake yi a gidan ba a yau idan ta ce ta sallame shi a aikin nan ya zaunu. A dan ladabce ya ce " ki aike ni duk Inda kike bukata daga nan har abuja ni driven ki ne, kuma na miki alkawain madam bazata san da wannan maganar ba." Cikin jin dadi ta ce "Ngd Peter," ya ce "never mind your Majesty." Waige waige ta danyi kafin ta fito da pepan daga aljihunta ta mika mishi. Ta ce "Wannan nake son ka kaiwa kawata Fatima, nasan kasanta ai?." Ya gyada kai cike da mamaki, don ranar a gaban idanunsu komai ya faru, ta ce "Kasan gidan su?" Dan Jim yayi alamar tunani, ya ce "eh kamar na sani ba gidansu na a wancen layin ba ne." Ta ce "yes." Tare da sake yi mai kwatance sai da ta tabbatar ya gane sosai, sannan ta Ciro dubu goman nan data dauko ta mika mishi, godiya ya shiga kwasa cike da farin ciki, ta ce "Pls ka kiyaye ka san me zaka fadawa Mom idan zaka fita, sannan ka tabbatar ka amso min replay daga gareta kar ka dawo kin ba tare da amsa ba, sannan ka tabbatar ita ka damkawa hannu da hannu kar ka ba kowa idan ba ita ba." Ya ce "Am gama your Majesty." Daga haka juyawa ta yi ta koma ciki, dakin ta ta haura ta dage labulayen window, tana kallon sanda Peter ya isa bakin get a moto, sai da securities din nan suka kira Mom ta yi magana da Peter ko mai ya gama mata oho ta dai ga an bude mishi get ya fice ajiyar zuciya ta sauke ta koma da baya ta zauna a bakin bed ta rafka tagumi.
Chapter 13 · 0% Book details