Sashe 3
Joy Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ba tare da ya dago kanshi ba ya ce "Ba koma Ummi jiya da zazzabin mura na kwana da ciwon kai amma Alhamdulillah zuwa yanzu ya sauka na ji sauki dan nasha maganin tun cikin daren." Cikin da nazarin yanayin shi ta ce "Ka tabbata." Ya gyada kai tare da ce wa "Eh Ummi." Ta ce "Allah ya kara sauki." Ya amsa da "Amin Ummi." "Kazo ka juye ruwa kayi wanka zaka ji karfin jikinka sai ka sha kunu ka kara shan maganin." "Toh Ummi."ya ce tare da juyawa ya nufi inda botikin wanka yake ranshi duk a ɓace.
*********
Suna fitowa Fatima riko hannunta tare da maka mata harara cikin harshen nasara Wanda shine yaren da Joy ta fi iyawa ta ce "why Bestie me yasa kike son saka kanki cikin damuwa ne sabo da ni." Kallonta Joy tayi ta sakar mata murmushi Wanda har sai da dimple dinta ya loza, cikin jin haushi Fatima ta ce "OK dariya ma na bakin ko." Fari ta mata da idanu ba tare da ta amsa ba hakan ya ƙara hassala Fatima, take ta hade rai kamar bata taɓa dariya ba sake hannun Joy tayi ta kama hanya zata wuce ta barta, ganin haka yasa Joy saurin shan gabanta rike kunnayenta tayi cikin marairaice fuska ta ce "sorry my Teetee." Jin sunan da ta kira ne yasa Fatima kwashewa da dariya tare da kai mata dundun wasa, itama dariyar ta kwashe da shi, tana kaucema dundun Fatima, sai da suka natsa, Fatima ta ce "kin san dai mun makara, sai ki shirya amsan punishment." Ba tare da wani damuwa ba ta ce "Ai na shirya." Fatima ta ce "OK I see." Da haka suka kama hanyar school hannunsu rike dana juna suna fira suna kwasar dariya cike da nishadi hankali kwance, duk da ita Joy tsoron al'ameen bawai ya gama sakin ta bane, da ka gansu zaka hango yadda suke tsananin kaunar juna.
Kamar yadda suka tsammata kuwa sun tarar ana kama late comer a bakin get ana musu bulala, sosai Fatima taji babu dadi a ranta dama abin sa take gujewa Joy kenan, amma ta lura ita Joy din babu alamar damuwa ko nadama a fuskarta.
Koda suka Isa class har teachern da zai dauke su first period ya shiga class kasancewar sa ba mai tsauri ba yasa excuse kawai suka dauka ya basu izini suka shiga ciki.
Suna shiga idanun Joy ya sauka akan na David daya zubo musu ido yana kallo yana gyada kai, harara ta maka mai tare da dauke kai daga kallon shi, sit din su suka nufa Wanda yake a layin gaba suka zauna su biyu, dama bibbiyu ake zama a kowane sit.
Haka sukai ta daukan karatu cike da himma da kwazo don dukan su ba baya ba wajen kokari, wannan malamin ya shiga wannan ya fita har har zuwa break time, Joy ta fito musu da su chocolate da biscuit din da ta zuba a jaka suka zauna a class suna ci suna hiran karatu, sai jin tsayuwar mutum sukayi a kansu, kusan tare suka dago suka kalle shi, harara ya fara watsama Fatima wanda itama bata yi kasa a gwuiwa ba wajen ramawa kafin cikin wani yare wanda Fatima bata ji ya fara ce wa "dama nasan gidan su wannan matsiyaciyar zakije kuma ki rubuta ki ajiye daga wannan karan kinyi na farko kinyi na karshe don sai na gayawa papa halin da kike ciki a makarantar nan kin san kuma abin da zai biyo baya, wannan ai zubar mana da Kimar family kike yi." A harzuke ta ce da harshen turanci don shi tayi ji fiye da yaren su da David ke mata magana da shi "David ka fita harkata babu ruwanka dani kayi harkan ka nayi nawa a cikin makarantar nan." Ya ce "bazan fita a harkar taki ba, kiyi abin da zakiyi." Kwafa tayi ta ce "to ka ci gaba da shiga zan yi maganin ka." "Ni dai ne zan yi maganin ki, wawiya kawai Mara kishin kanta da addininta." Yana gama fadin haka ya juya ya fice daga class din, joy taji zafin zagin ta da yayi hakan yasa a zafafe ta mike zata bishi don ta rama, da sauri Fatima ta rikota tana bata hakuri, batasan takamaimai abin da suka faɗa ba tunda da yare ne amma ta fahimci a kanta ne suke wannan cacar bakin, kamar yadda ta bangarenta Joy ke fuskantar barazana da kiyayya a wajen yayanta, haka take fuskantar kiyayya da kyamata daga wajen duk wani ahlin Joy uwa uba iyayenta.
David dan uwan Joy ne cousin dinta ne, mahaifiyar shi kanwar papa ne uwa daya uba daya.
Rarrashinta Fatima ta shiga yi tana bata hakuri, da kyar ta hakura ta koma ta zauna don Joy akwai zafin zuciya idan ta fusata, basu fita ko ina ba har aka dawo break aka ci gaba da lesson, har kuma akayi closing bata daina hararan David tana kwafa ba, Fatima dai sai aikin rarrashi take kasancewar tasan halin kayarta.
Tare suka fito daga cikin school din kamar yadda suka saba hannun sakale da juna, sarai Joy taga driventa peter yazo daukarta amma ta yi fuska ko kallon inda yake bata yi ba saboda tana so ta jera da Fatima ,sau da yawa takance Fatima tazo su Shiga mota su sauke ta amsa ƙememe take ƙi saboda gargadin ummi.
Peter bai damu ba don Inda sabo ya saba da hakan, rana daddaya ne idan yazo daukan ta take yarda ta bishi.
A hanyar su sai da Fatima ta san yadda ta yi, ta mantar da Joy ɓacin ran da take ciki na David, sai gata tana dariya har da kyakyatawa.
Wani me sai da yalo ne ya zo wucewa yana talla a bairo, har sun gifta shi Fatima ta ce "laaa Joy bari na sai ma yayana yalo." Kafin Joy ta amsata har ta juya ta isa gare shi, hamsin din da ummi ta bata ta mika mishi ya bata na hamsin.
Dawowa Inda Joy take tsaye tana jiranta tayi cike da farin ciki ta ce "nasan yayana zaiji dadi sosai don yana son yalo kamar me." Taɓe baki Joy tayi tare da cewa "Wanna yayan naki dabe dariya bashi da fara'a ko dan murmushi ni ban taba gani yayi ba kullum yayita yiwa mutane muzurai, shine zaiyi wani farin ciki don kin sai mai yalo, ni fa shi yasa yaya ko kani basa burgeni." Wani kallo Fatima ta mata kafin ta ce "waya gaya miki yayana baya dariya, waya gaya yayana baya fara'a ina jin duk unguwar nan babu wanda ya kai yayana iya murmushi." Joy ta ce "Au haka ne fa."ta fadi maganar cikin sigar tsokana, fon ita bata yarda ba gani tke yi fatina wasa take yi, Fatima ta ce "koma me zaki ce kice, kuma da kike cewa yaya ko ƙani bass burgeki wlh don bakin hadu da irin yayana bane, ganin kamar fa da gaske take yi, yasa Joy cewa "wai da gaake kike yi ko wasa." murmushi Fatima ta yi tana girgiza kai, nan kuma ta shiga ba Joy labarin yayanta yadda yake kula da ita yadda yake sonta da yadda baya kaunar bacin ranta, tun Joy na jinta sama sama har kuma labarin ya fara shigar ta, nutsuwa tayi ya maida dukkan hankalinta tana sauraren Fatima a ranta tana mamakin abubuwan da fatima tace al'ameen nayi, ji tayi a ranta koda so ɗaya ne zata so taga murmushinsa,a haka suka iso kwanan gidan su Fatima Wanda sai an wuce shi kafin a isa na su joy, ji tayi bata son su ru don bata gaji da jin labarin ba, har kofar gida ta raka fatima sannan suka yi sallama ta kama hanyar nasu gidan.
Tana tafe tana murmushi ita kaɗai tana tuna labarin yayan Fatima, da haka ta ƙarasa nasu katafaren gidan, knocking tayi, jiki na bari me gari ya bude mata yana mata sannu da dawowa, bata da wulakanci da girman kai ko kadan ita dai barta da tabara da shagwaba, hakan yasa ta sakar mai murmushi tana amsawa ta sa kai ta nufi entrance din gidan.
Fuskarta cike da murmushi ta turo ƙofar falon ta shiga, a bakin ƙofa ta taka birki murmushin fuskarta na ɓacewa, lokacin da idanunta ya sauka akan mom da David da ke zaune a falo, duk ido suka zubo mata, shaf ta manta da wani David da alwashin daya dauka yau a kanta, ganin iron kallon da mom ke jifanta da shi yasa taji gabanta ya fadi, a ranta ta ce shike nan na Shiga uku David ya gama dani......
Me bukatar Shiva group ya tuntubeni ta wannan lambar
09116099486
[12/29, 2:20 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀
*BY*
*AYSHA NALADO*
*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
*LITTAFI NA ƊAYA*
*PAGE 3*
Fuskarta cike murmushi ta tura ƙofar falon ta shiga, ta na kwalama Mom kira, a bakin ƙofa ta taka birki murmushin fuskarta na ɓacewa, lokacin da idanunta ya sauka akan Mom da David da ke zaune a falo, duk ido suka zubo mata, shaf ta manta da wani David da alwashin daya dauka yau a kanta, ganin irin kallon da Mom ke jifanta da shi yasa taji gabanta ya fadi, a ranta ta ce shike nan na Shiga uku David ya gama dani.
Sai da ta hadiyi miyau mukut! Kafin ta kirkiro murmushin dole ta sakar musu , cike da fargaba ta nufi Mom don ta rungumeta kamar yadda Mom d'in ta sabar mata, hankad'e ta Mom tayi saura kad'an ta fad'i Allah ya taimaketa ta dafa kujera, cikin tsananin bacin rai ta ce "kar ki kuskura ki ta'ba ni Joy!!!" Ta karashe maganar a kausashe.
A razane ta sauke manyan idanunta da lokaci d'aya suka tara kwalla a fuskar Mom, cikin karaji Mom taci gaba da ce wa "kije na yafe musu ke,tunda sun fini a ajenki kije kqai tunda ke kince baza kiji magana ba."daga haka ta mike a fusace ta bar falon ba tare da kara kallon gefen da Joy take ba.
Lumshe manyan idanunta zuciyarta na wani irin tsinkewa, hakan da tayi ne yaba hawayen dake kwance a idanunta daman zubawo, minti biyu ta dauka a haka kafin ta waresu akan David dake kallonta yana sakin murmushin mugunta.