← Book details Joy Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 46

Sashe 41

Joy Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*NOTE*
Jiya na yi mistake wajen saka number, instead of 37 na sake maimaita 36, so yanzu zamu je 38 da fatan kun fahimta👌

A kwana a tashi ba wuya, musamman a wannan zamanin da muke ciki ta karshen duniya yadda lokaci ke gudu kawai ya ishi bawa tsoron Allah. Tsakanin Al'ameen da Amira komai ya k'ara daidaita soyayya suke gudanarwa mai tsabta, kyautatawa tare da kulawa had'i da girmamawa sune manyan makaman da Amira ta yi amfani da shi wajen kafa kanta a zuciyar Al'ameen, bugu da k'ari yadda take nunawa Ummi da Fatima tsantsar soyayya da kulawa ya k'ara mata kima a idanunsa, wani babban matsayi na musamman ya ware mata a zuciyarsa, da fari ya k'arbi, soyayyar ta ne saboda Fatima sai kuma tausayinta da yake ji, sai dai da tafiya tayi fatiya rashe ya juye da mujiya, don a halin yanzu idan ya ce baya sonta to tabbas ya yi babban karya.

Ya zuwa yanzu babu wanda ya kamata yasan da maganar soyayyar su da ya rage bai sani ba, kama daga dangi, makota, y‘an uwa, da abokan arziki, tuni kawunan Amira suka fara maganar cewa Al'ameen ya turo magabatansa idan da gaske yake, lamarin da ya yi masifar d'aga masa hankali, bashi da kud'in aure yanzu bai ajiye ba bai baiwa wani ajiya ba, hasalima d'akin da zai sakata kango ne bai kai ga k'ark'are ginawa ba.

Cikin kwana biyu kacal da samun wannan sak'on duk ya gigice ya shiga damuwa, tabbas yana buk'atar mace a rayuwarsa, musamman a halin yanzu da ya kai gargarar da tablet d'in da yake sha sam! ya daina yi masa aiki, ko da kuwa zai shanye sachet biyu ne a take, k'arfi da ya ji ya koyi, istimna'i, (Biyawa kai bukata) wanda a duk lokacin da hakan ya kasance yakan kwana ne yana kuka tare da neman gafarar Ubangijinsa, sarai ya san abinda yake aikatawa sa6o ne babba haramun ne , kuma cuta ne ga lafiyarsa, sai dai shi hakan ya fiye masa a kan ya aikata zina, yana kyamar zina, haka yana tsananin tsoron aikatawa domin ya dad'e da sanin bashi ne, idan kaci sai ka biya, shiyasa yakan yi taka tsantsan wajen ke6ewarsa da Amira, saboda kasancewar ta ma'abociya son gayu da kamshi, a cikin yan kwanakin nan, hirasu ta waya ya fiye masa alkahiri bisa ga ace sun ke6e, domin a duk sanda hakan ta kansance ya kan shiga wahala da garari.

Misalin karfe biyu na sulisin dare, zaune yake a bakin kafifarsa, ya rafka taguma da duka hannayensa biyu, idanunsa ya yi jajur, hankalinsa a tashe nadama da kaico kwance k'arara akan fuskarsa,ya tabbata idan mutuwa ta riskesa a wannan halin la shakka zai gamu da fishi da azabar Allah, take wani irin tsoron Allah ya dirar masa, zuciyarsa ce ta karye, take hawaye ya shiga kwaranya daga idanunsa, ya dad'e yana kuka, banda "Astagfirullah Allah na tuba Allah ka yafe mini." Babu abinda yake maimatawa a zuciyarsa, ganin zaman da yake yi da najasa a jikinsa bashi da amfani yasa ya tsagaita da kyar, ya mik'e yana layi tamkar wanda ya yi tatul, daga shi sai gajeran wando a jikinsa, sif ya bude ya dauki, wani wandon wankakke, ya kuma dauki babbar butarsa dake ajiye a gefe cike da ruwa ya fito, kamar yadda ya saba kullum cikin sand'a da taka tsantsan ya nufi toilet.

Cikin takaitaccen lokaci ya tsarkake jikinsa ya fito sanye da wankakken wandonsa yayinda ya riko daya wandon da hannu hagu cike da kyamkyami, gabansa ne ya yi wani irin yankewa ya fad'i lokacin da idanunsa ya hadu dana Ummi da ke rike da buta wanda ta gama zuba ma ruwa a ciki yanzu yanzu, da sauri ya yi kasa da kansa gabansa na ci gaba da wani irin dokawa, take ya ji wani irin sanyi na kada shi, da yana da hali a lokacin da babu abin da zai hana yace kasa ta bud'e ya shige tsabar kunya.

Kur! Ta kure shi da kallo zuciyar ta na tsinkewa, ba yaune karo na farko da ta ta6a kamashi yana wanka ba musamman ma a cikin yan kwanakin nan da abin a shi ke neman shallake tunaninta, sai dai basu ta6a yin gaba da gaba ba sai yau, ita kanta bata san yana tailet d'in ba da batta yarda ta fito alwalan ba, ta bari har sai ya gama ya shige d'aki.

Yi tayi kamar bata gane komai ba, ta ce "A' a Amintacce hala kaima zafin nan ya dame ka, da sauri ya ce "E wallahi Ummi, na kasa barci sai da na fito na watsa ruwan sanyi." Tana nufar toilet d'in tace "Hmmm! Allah dai ya saukaka mana." Daga haka ta shige toilet, da sauri ya bar tsakar gidan.

Ta dad'e a kan darduma tana kai kukanta gurin Allah tana hawaye, tun jiya da maganar cewa Al'ameen ya turo magabatansa ya risketa take cikin matsanancin tashin hankali, shin wa zai wakilci lamarin auren nan, shin wa zata nuna musu a matsayin dangin mahaifinsu, tabbas lokaci yayi da zata waiwayi wadancen azzaluman Ahlin, lamarin Al'ameen ya fara bata tsoro ita kanta zata so ya kasance da mace a kusa, domin dai ta riga ta gama fahimtar shi din mai tsananin bukata ne.

Da safiya kasa hada ido ya yi da ita, duk da yadda ta yi iya kokarinta wajen ganin ta nuna mishi bata fahimci komai, shi yasan ta fahimta d'in domin dai ita ba yarinya bace duk da babu wanda zai ganta ya ce ita ta haife shi Indai ba wanda ya sani ba, haka jiki a sanyaye ya shirya ya fice daga gidan.

School ya nufa don yana da lecture, karfe goma ya fito daga school, jikinsa duk a mace kansa ne ke masa matsanin ciwo kamar zai rabe biyu baya jin yana da kuzarin iya fita aiki yau, hakan yasa ya kira Aliyu ya ya ji ko yana gida, samun tabbacin yana gida yasa kai tsaye ya tari dan acaba ya nufi gidan su Aliyu.

Ganin shi a sanyaye yasa Aliyu tarar shi da cewa; Lafiya Ameen mekefaruwa." Zama ya yi a kan kujera 2 sita dake d'akin Aliyu ya dafe kai, yana sauke numfashi.

Ajiyar zuciya Aliyu ya sauke, ya zauna kusa da shi, sun fi minti biyar a haka, Al'ameen bai ce komai ba shima Aliyu bai matsanta mashi ba, sai da ya gaji don kan shi ya dago idanun da suka kara rinewa ya kalli Aliyu. Ya ce "Aliyu ya zan yi? Nutsuwa Ali ya kara yi ya maida dukkan hankalinsa garesa, ya ci gaba da cewa; "Iyayen Amira sunce na turo, Aliyu bani da halin aure ban ajiye ba ban ba wani ajiya, kuma ina bukatar aure Aliyu ya zan yi? Murmushi mai sauti Aliyu ya yi a zuciyarsa ya ce anzo wajen.

Wani irin kallo Al'ameen ya shiga bin Aliyu da shi ganin yana murmushin, ganin irin kallon da yake masa yasa ya dafa kafadar shi, ya ce " Abokina a kwai mafita." Tamkar wani soko ya ke bin Aliyu da kallo kafin ya ce "Akwai mafita kace Aboki?" Gyada kai Aliyu ya yi ya ce "kwarai kuwa a kwai mafita."..............

Oum ummeetarh
09116099486
[12/29, 2:48 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀

~FARHAT~

*PAGE 39*

Mikiya Writer's Association.

"Menene mafitar?" Al'ameen ya tambaya idanunsa cikin na Aliyu. Nannauyar ajiyar zuciya Aliyu ya sauke, cike da kwarin gwiwa ya ce "Dr Abdul Hafiz ." Wani irin k'ank'ance ido Al'ameen ya yi, a hankali ya maimaita sunan da sigar tambaya "Dr Abdul Hafiz S Alto?" "Kwarai shi nake nufi." Aliyu ya fad'a shima yana kafe Al'ameen da ido.

Bacin rai ne ya bayyana k'arara a fuskarsa take, a kausashe ya ce "Menene had'in ka da shi?" Dakewa Aliyu ya yi daman yasan hakan zai iya kasancewa, ba tare da shayin komai ba ya ce "Zumunci." Gyada kai Al'ameen ya yi, ya ce "Zumunci ko? Very gud." Daga haka ya mik'e bai kalli side d'in da Aliyu yake ba ya fice daga d'akin jiri na kwasarsa.

Murmushi Aliyu ya saki a yayin da ya raka bayan shi, da kallo, taurin kan Al'ameen ya wuce tunanin mai tunani, idan ya riga ya kau da kai a kan mutum da wuya ya k'ara waiwayarsa ko shi waye, sai dai ya lashi takobi zai yi iya 'kokarinsa wajen ganin komai ya daidaita.

*********

*JOY*

Tun daga ranar da Fatima ta sanar da ita batun soyayyar Yaya Ameen da Amira, bata sake yarda wani hira makamancin wannan ya sake shiga tsananinsu ba domin ta san baza ta iya jurar ji ba, zuciyar ta baza ta iya d'auka ba. Haka suka ci gaba da harkokinsu ba tare da ta bari Fatima ta fahimci komai game da abin da ke lullu6e a zuciyarta ba, ta bi ta toshe duk hanyar da Fatima zata fahimci a kwai wani abu a zuciyarta game da Ameen, tun da ta fahimci kamar Fatin na zargin hakan, sai dai duk wani walwala da kuzarinta ya ragu, sam! ta daina tambayar Fatima game da Al'ameen kamar yadda take yi ada, idan ma Fatima ta dauko hirar shi, da dabara za ta dakatar da ita ta hanyar sako wani hirar dabam ta shashantar da wancen hakan ya saka zuciyar Fatima a wa si wasi a kan zarginta, har ta samu kwanciyar hankali, don ta yi imanin cewa; Joy baza ta ta6a boye mata wani sirri na rayuwarta ba, sai ta watsar da zargin da ta ke yi suka ci gaba da sabgarsu na yau da kullum babu wani sauyi.
Chapter 41 · 0% Book details