Sashe 5
Joy Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kiran waya Mom keyi amma gaba daya hankalinta na kan Joy, kukanta na matukar ta'ba mata zuciya, har ta fara daina fahimtar abin da take yi, zuciyarta ce ke azalzalarta akan ta rungume Joy ta jawota jikinta ta rarrasheta ta hanata kuka, sai da ta yi da gaske ta yakice wannan tunanin daga ranta, dan idan yayi wasa ta bari rauninta ya bayyana ta bazan ta comma burinta na taba Joy da Fatima cikin sauki ba, juyowa tayi a fusace ta kalli Joy cikin tsawa ta ce "ki fita ki bani waje Joy bana son ganin ki." Joy data kara tsorata da lamarin Mom ta dago murya na rawa ta ce "I'm sor!!!" Kafin ta karkare fadin abin da zata fad'a Mom ta sake daka mata tsawar data fi na dazu " I said get out from here." Ta karashe maganar tare da yiyowa kanta kamar idanu waje, da gudu ta fice daga d'akin tana rizgar kuka.
**********
Ko da Fatima ta isa gida, a daki ta samu Ummi, ta dan kishingid'a akan darduma da alama sallah tayi ta idar, Sallamar ta yasa Ummi da barci ya fara kwasarta ta bude idanu, ganin haka yasa Fatima cire takalmi ta karasa shiga dakin ta na cewa "Ummi sannu da gida."
"Yawwa Fatima kin dawo."
"Eh Ummi Allah ya dawo dani."
"Maza ki debi ruwa ki dauraye jikinki ki kimtsa ga abincin ki nan a kitchen ki dauka.
Bayan Fatima ta fito wanka dakin ta shiga ta kimtsa jikinta ta canza pad, wardrobe ta bude ta dauki kayan da zata saka, har ta ciro Riga da zani sai idanunta ya sauka akan wani Riga da siket na kanti da take da shi na gwanjo, ta Dade ma rabonta da sakawa, haka nan ranar taji tana sha,awar saka kayan, cirowa ta yi ta shirya cikin su, kayan sun mata kyau sai dai sun kamata tsam dai dai jikinta sabanin da da suka mata dan yawa yanzu har skirt din ya d'angale mata don iyakarsa 'kaurinta, amma dai sun bala'in yi mata kyua.
Abincinta ta dauka ta ci , ganin Ummi ta samu barci yasa ta yi kwanciyarta a daki, tare da Ciro wani story book data amsa hannun Joy ta fara karantawa, tana fara karatun itama barci ya kwashe ta nan ta yada book din ta tintsire.
Kiran sallar la'sar ne ya farkar da Ummi, ta shi ta yi ta fito tsakar gida
dan ta dauro alwala ta na cikin zuba ruwa a buta Al'ameen ya shigo cikin gidan, shima kiran sallar ne ya tada shi ya shigo don ya daura alwala ya lallaba ya tafi masallaci,
"Sannu Ummi." Cewar Al'meen kallon shi Ummi ta yi lokacin ta zuba ruwa ta tsuguna daga bakin makwarari zata fara alwala ta ce "yawwa yayan Fatima ya jikin." "Da sauki Ummi." Ya ce yana shigewa makewayi, koda ya fito Ummi ta idar da alwala ta shige daki don ba Iya kama ruwa yayi ba, sake diban wani ruwa yayi a drum ya tsuguna ya yi alwala, sannan ya fice zuwa masallacin kusa da gidan jin ana haramar tada sallah.
Sai da Ummi ta idar da sallar ta tashi Fatima, akan taje ta wura wuta ta daura ruwan tuwo tunda yau alhamis basu da islamiya.
Bayan Al'meen sun idar da sallah fitowa yayi daga masallaci, kallon yanayin garin yayi, ko'ina shar haka kawai yaji yana sha'awar yad'an zazzaga, Abokin shi Aliyu ne ya fad'o mai a rai murmushi yayi a fili ya ce "dan duniya nasan yana gida yanzu, bari na mike kafa na kai mishi ziyarar bazata." Kallon jikin shi yayi, ganin, kananan kaya ne a jikinshi wandon jins ruwan kasa da T shirt fari mai layilayi bakin, bai ciki son fita da kananan kaya ba, amma ganin rigar bai matse shi ba yasa ya kama hanyar unguwar su Aliyu a kafa kasancewar basu da nisa unguwa daya ne a tsakanin su.
Stadium junction nan ne unguwar su Ali, a kofar gidan ya tsaya ya aika aka mishi sallama da shi, Aliyu ya fito yana waige waige, daga bayan shi yaji an ce "Aliyu timekeeper." Da sauri Ali ya juyo jin muryar da bai zata ba, a d'okace ya nufe shi ya na fadin" A'a ustaz! ustaz! ustaz! ustaz!!!! namu." Hannu Al'meen ya bashi suka kashe suna dariya, Al'ameen ya ce "Babban timekeeper babban timekeeper" suka sake kwashewa da dariya.
Sunaye ne da suke kiran junan su tun a makaranta, hakan yasa koda aka gama karatun aka rabu ba'a bari ba, haka suke kiran junan su dama sunan makaranta ya gaji haka, hakan dabi'a ce ta dalibai duk Inda aka had'u komi tswon zamani kuma duk komin munin suna haka za'a kira juna, Ali ya ce "gaskiya ka shammaceni ustaz ban taba zaton kai ba ne." Al'meen ya ce "Ai baka da mutunci Ali, baka da kirki baka zumunci." Ali ya ce "Wai talle ne zai ma Audi gori ba gara ni ba ma ina kira a waya a kai a kai kuma ko last time na haduwar mu ni naje gidanku ko ka manta ne na tuna maka." "A'a fa Ali ka dai sake tunawa." Cewar Al'ameen, haka dai bayan sun gama yar musu as ka gaisa da tambayar ahalin juna daga na suka nemi waje suka zauna kan dakalin kofar gidan su Ali suka shiga hira suna kwasan dariya.
Al'ameen bashi da aboki sama da Ali don shi ba mai yawan kwashe kwashe bane , tare suka yi makarantar primary nan IBB Inda bayan sun gama suka wuce maitunbi secondary school tun jss 1 ajin su daya har suka kammla gasu kuma yan unguwar kusan daya, hatta iyayensu sun san da zaman juna, yanzu da aka gama secondary kowa ya kama gaban shi shine zumuncin yayi wuya duk da suna tare a waya Bini Bini saduwace dai sai a hankali.
Fira ce ta barke sosai, Aliyu ya siya musu awaran waken auya da pure water suka ci, sun sha fira sosai suna ba juna labarin makarnata da karatu, shi shi Aliyu direct university ya tafi yanzu haka FUTmin yake zuwa yana 200 level yana karanta languages, inda Al'ameen ke juwa JEFLA yana karantar bangaren Islamic low shima yana year 2 ne kamar dai Aliyu, sun Dade suna hira kafin Al'ameen ya mike yace zai wuce ganin biyar da Rabi ake nema.
Taka mishi Ali yayi suna tafe suna ci gaba da hira, sunzo dai dai get din stadium wasu yan mata su uku suka fito daga cikin wajen kowaccenau cikin matsatsen JC kai ba dankwali daya da jakar baya goye a bayan ta dayar kuma hannunta kwallo ne suna tafe tana buga shi fa titi tana cabewa, da ka musu kallo daya zaka san yayan arna ne.
Tsaki Al'ameen yayi tare da dauke kanshi a zuciya yana ambaton Allah da neman tsari daga shaidan, kallon shi Aliyu yayi ya ce "Ustaz namu har yanzu kanan nan da tsantsenin ka akan irin wadan nan matan." Al'meen yace "To ina amfanin wannan Abu haka don suna yayan arna sai su rika yawo haka suna fidda tsiraicin su, kamar wasu awaki, ya kamata gamnati ta dauki mataki don naga abin masgaba yake kara yi."
Aliyu ya ce "waya gaya maka a zamanin yanzu yayan arna ne kawai suke irin wannan dressing, yanzu ai abin babu arna babu musulmai, don idan kaga wata yar musulman sai ka zubar da hawayen takaici yanzu haka wadan nan ma in ka bibiya musulmai ne." Da sauri Al'ameen ya ce "kai haba Allah ya sauwake, wadannan yayan arna ne babu hasken musulumci ko kadan a tare da su." Kafin Aliyu ya kai ga amsa musa suka jiyo muryar d'aya daga cikin yan matan bahaushiya rass tana cewa "Aisha, maryam pls Ku jirani na sai ruwa." Dariya Ali yayi yana cewa "you see ustaz me na gaya maka." Takaici da bakin ciki ya hana Al'meen amsawa, Aliyu ya ce "Hmmm alamarin yanzu duk sai a hankali fa kalli wasu ma." Ya Nuna mishi wasu yan mata dake sanye da atamfa amma ya matukar matsesu kamar in suka yi kwakwaran nishi zai barke, girgiza kai Al'meen yayi cikin takaici da wannan yanayin suka rabu da Aliyu ya kama hanyar gida.
*****
Tunda Joy ta bar dakin Mom ta komawa dakin ta kan bed ta fada yana kuka ga ba ci ba sha, har kusan karfe biyar na yamma hakan ya saukar mata da zazzafan zazzabi mai hade da ciwon kai kafin shidda na gamma ta gama fita hayyacinci dkyar take sauke numfashi, Abu ne da bai taba faruwa da it's ba run tasowarta jinshi take yi sabo a gareta ,bata saba da hakan ba a kullum tsakanin vta Mom kulawace na musamman da Nina kauna haka ma Papa shiyasa duk ta wahala ta kasa sukuni......
Share pls kuma a dan ringa taba comment ko babu yawa, ta hakan ne zan gane kuma bite dani ko A'a
Me bukatar shiga group a tuntubeni ta wannan lambar
09116099486
[12/29, 2:30 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀
*BY*
*AYSHA NALADO*
*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
*LITTAFI NA ƊAYA*
*PAGE 5*
Da takaicin wad'annan y'an matan Al'ameen ya kamo hanyar gida, daf magriba ya iso k'ofar gidan su, ganin ana shirye shiryen yin salla yasa bai shiga ba ya nufi masallaci, koda suka idar bai tashi ba zama yayi a cikin masallacin yana addu'o'i tare da neman Allah ya kareshi daga sharrin ta'bar'barewar zamani, bai fito daga masallacin ba sai da aka idar da isha'i, daga nan kuma bai zame ko ina ba sai gida.