← Book details Joy Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 46

Sashe 8

Joy Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ajiye tuwon tayi a gaban shi tare da ledar yalon da ke damke a hannunta tun dazu, murmushi yayi ganin yalo, ya dago ya kalleta itama sai ta sakar mai murmushi, ya ce "Nagode yar gidan Yaya Ameen" dariya ta saka cike da jin dadin yabawan da yayi da kyautarta, wani dadi yaji ganinta cikin farin ciki sai ya tsinci kanshi da yiwa marigayin mahaifinsu addua wanda har yau ko a hoto Ummi bata taba nuna musu shi ko wani nashi ba, kawai abinda suka sani ya rasu da dadewa.

"Yaya sai da safe." Muryarta ya katsemai tunani, ya ce "har zaki tafi baza ki zauna muyi hira ba, ko barci kike ji da wuri haka?" Ta girgiza kai, ya ce "kinci naki tuwon ne ko?" Ta ce "A'a yanzu idan na shiga zanci." "Wanko hannu kizo muci tare." Ta amsa da "to Yaya" tare da shiga cikin gidan danta wanko hannu kamar yadda ya umarceta.

Cike da nishadi suka ci tuwonsu cikin kwarya daya suna wasa da dariya, a karshe ya saka katon loma, kukan shagwaba ta saka tana dire kafa, cinyewa yayi ya kara kai hannu da sauri ta dauke kwanan ta cinye guntun daya bar mata, tana tura baki, yana mata dariya da gwalo kamar bashi ne dazu ya rufeta da fada ba, bayan ta kwashe kwanukan wanko hannu tayi ta dawo, nan shiga bata labaran ban dariya yana cin yalo yana yabawa ita kuma dadi kamar ya kasheta, daga karshe ya saurari haddarta.

Ummi na tsakar gida tana saurarensu, tsakanin Al'ameen da Fatima sai Allah,ko ita data haifesu bata ce ga tsakanin subab, a haka bata san sanda ta fara gyengyadi ba.

Ba su suka ta shi ba sai gurin goma da rabi, shima ganin tana ta hamma yasa ya ce taje ta kwanta, koda ta shigo gida ta samu Ummi tayi barci radio a kunne tashin ta ta yi, suka wuce daki bayan sunyi alwalan kwanciya.

Washegarikamar kullum ta gudanar da aiyukanta na safe tayi shirin makaranta, tana ta zuba idon ganin Joy sai dai shiru shiru har ta gama ta fito gida ta kama hanya, yana ta tunanin ko zasu hadu a hanyar amma shiru har ta isa bakin get, bata kara shiga damuwa ba sai da ta isa class ta tarad babu joy babu me kama da ita, haka ta zauna jiki a sanyaye tana tunanin mekefaruwa ne yau, iya Sanin ta Joy bata fashin makaranta, can sa'insar daya shiga tsakanin joy da David ya fado mata, take gaban ta
ya yanke ya fadi rassss..........

Me bukatar shiga group ya tuntubeni ta wannan lamabar
09116099486
[12/29, 2:32 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀

*BY*

*AYSHA NALADO*

*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*

*LITTAFI NA ƊAYA*

*PAGE 7*

*AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE*
_Jama'a kada ku bari wannan garabasa ta wuce ku,muna da nau'i magungunan gargajiya masu kyau da inganci_
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda inganci da sahihancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai-dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_nfection_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace *SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI💯☑️*_

_Muna sayar da supplement gangariya irin wadanda ba su da matsala sai da su gyara garkuwar jiki da inganta lafiya, muna bayar da sari duk wani supplement muna da shi, kuma muna sayar da daya muna bada sari akan farashi mai sauki, muna tura kayanmu ko wane gari domin neman karin bayani a tuntunbi wannan lambobinmu dake kasa._
*08089965176*
*07084653262*

Ranar haka Fatima ta wuni a school babu walwala, sboda rashin zuwan Joy, gaba ɗaya jin school ɗin take yi babu daɗi a haka har suka yi closing, jiki a sanyaye ta kamo hanyar gida cike da tunanin abin da ya hana joy zuwa school, fatan ta Allah yasa dai lafiya.

A kulle ta iske gida alamar babu kowa, sai lokacin ta tuna Ummi ta ce mata zata dan fita idan ta dawo ta karɓi key a maƙota.

Gidan da ke kallon gidan su ta shiga, shima dai kamar nasun ne, na y'ay'an mallam shehu, sai dai yafi nasu girma da yalwar ɗakuna, sallama ta yi a ƙofar ɗakin Maman Amira kamar yadda suke kiran matar gidan, Amira ce ta fito daga ɗakin tana amsa sallamar, ganin Fatima yasa ta fad'ad'a fara'ar fuskarta, budurwace yar kimanin shekara goma sha bakwai, sanye da wandon uniform dinta na girls day, ta cire rigar ta bar farin singlet da alamar itama dawowarta kenan.

Murmushi Fatima ta sakar mata tare da cewa "Yaya Amira ina wuni." Cikin sakin fuska ta amsa da "Ina gajiya Fatima kin dawo ya school." Fatima ta ce "Alhmdllh." "Shigo mana tana ciki." Amira ta faɗa tana kauce mata a hanya, "A'a dama Ummi ce idan na dawo na karbi key gurin Mama." "Ok bari na karbo miki." Ta koma ciki ba jimawa ta fito da key din ta mikawa Fatima, amsa tayi ta fice, bayan tayi godiya, da kallo Amira ta bi ta fuskarta dauke da murmushi a fili ta ce "kamar su daya sak! komai nasu iri daya hatta murmushin, ya Allah ka mallakamin Yaya Ameen kasa ya zama majibancin rayuwata, jin Mama kwala mata kira yasa ta amsa tare da komawa dakin da sauri.

Ta tarar da gidan tsab kamar kullum, dakinsu ta bud'e ta shiga ta canza kayan jikinta, ganin Ummi bata nan yasa bata tsaya watsa ruwa ba, don idan tana nan bata yarda ta ci abinci sai ta watsa ruwa tayi sallah.

Kitchen ta bude ta dauko Kular abincinta, shinkafa ce garau garau da yaji, a nan tsakar gida ta zauna ta ci abincin, tana gama ci ta mike ta kai kular kitchen, tana fitowa Al'ameen na shigowa bakin shi dauke da sallama, amsa mishi tayi tana mishi sannu da zuwa, murmushi ya sakar mata yana amsawa.

Idanunshi duk sun zurma kafafunta shi futufutu, takardun hannun shi ya ajiye kan windon d'akin Ummi, ya ja kujerar ummi yar tsuguno ya zauna yana ce wa "Fatima bani ruwa a buta." Da sauri ta dauki buta ta kai mishi bayan ta zuba ruwa, kafafunshi ya shiga wankewa, Fatima dake tsaye daga gefe ta ce "Yaya tracking kayi ne?" Ya ce "Eh kuma A'a kusan dai haka." Ya karashe maganar yana miƙewa don ya riga ya gama dauraye kafar nashi.

Kofar dakin Ummi ya nufa, ganin haka yasa Fatima ta ce "Bata nan Yaya." Juyowa yayi ya kalleta a mamakance ya ce "Bata nan, ina taje?" "Wlh ban sani ba ta dai ce min zata dan fita da safe kafin na tafi school." Gyada ka yayi bai, kara cewa komai ba ya nufi dakin shi, Fatima kuma ta nufi kitchen ta dauki abincin shi tabi bayan shi da shi.

Abincin ya ci ya koshi, bayan ya gama yasha ruwan sama, kishingid'a yayi a katifar shi ya lumshe idanu, da ace shi wani dan gata ne da kwanciya zaiyi ya huce gajiyar daya kwaso na tafiya, amma yasan haka ba Abu ne mai yuwuwa ba, idan ya kwanta wa zai basu su ci,wa zai kula da mahaifiyar shi da kanwar shi, wa zai dauki dawainiyar rayuwar su, wa zai biya musu bukatunsu na yau da kullum???, "Babu." Ya ba kan shi amsa a bayyane, shine gatan su da shi suka dogora da Allah suka dogora, tunanin yadda yasha gwgwarmayar zuwa da dawowa school yau ya shiga yi, zai Iya cewa daga zuwan har dawowar kusan da kafa yayi saboda halin babu, duk abin da ya roro ba ta kan shi yake yi ba, ta Ummi da Fatima yake yi, sune a gaban shi, da wannan tunanin ya yunkura ya mike ya canja kayan jikin shi ya fice daga dakin.

Cikin gidan ya shiga ya ma Fatima sallama sannan ya fice, daga gidan, direct unguwar Sayako ya nufa gidan Alhaji bala baka shot, in da yake zuwa daukar keke napep, ya na fatan Allah yasa akwai keken a kasa, cikin sa'a ya samu har biyu a kasa, take aka bashi wani form yayi singing, singing din da kulli yaumin idan zai yi sai gaban shi ya fadi ya rasa dalili, amma haka yake daurewa domin bashi da wata hanyar da zai samu kudi a saukeke sai wannan, yana dan tana sana'ar hannu, amma aikin nashi ne ba ko wani lokaci yake samu ba, haka ya dauki keke daya ya kama aiki da bismillah.

Tafiyar Al'ameen babu dadewa Ummi ta dawo,dauke da buhun bakko, Fatima ta tare ta ta amsar mata kayan, tana mata sannu da dawowa "yawwa Fatima sannu da gida," ta karashe maganar tana zama a kan kujera, " matso da bakkon nan Fatima mu gani."
Chapter 8 · 0% Book details