← Book details Joy Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 46

Sashe 22

Joy Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ranar haka Joy ta wuni cikin wahala da zagi da tsamgwama daga wannan ta shiga wannan , ba ita ta samu kanta ba sai wajajen karfe goman dare, duk wannan wahalar da gajiyar da tayi tana samun hakarkarinta ta kasa tunanin Al'ameen ya mata sallama, Babu abin da yafi tsaya mata a rai irin kyakkyawar murmushi sa, ta tuna ranar da Fatima ke ce mata duk duniya babu wanda ya kai Yayanta iya murmushi, a she da gaske ne. Ta sake tuno daddadar muryar sa lokacin da yake ce mata "I'm sorry! Ban yi don na cutar dake ba." Murmushi ta yi tare da kai hannu ta shafi goshinta dai-dai gurin daya d'an kuje har yayi jini tana sahafawa tana murmushi, bata san iya tswon lokacin data kwashe a haka ba kafin barci barawo yayi gaba da ita...

***********

Masu bukatar shiga group na joy su tuntube ni kai tsaye .

09116099486
[12/29, 2:38 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀

~FARHAT~

DAGA ALƘALAMIN👉
*AyshaNalado*

ƘARƘASHIN JAGORANCIN👉
*Mikiya Writers Association*

*PAGE 20*

Washegari wajajen bakwai da rabi na safe, Anty Esther ta fad'o mata dak'i, tana cikin barcinta mai dad'i wanda ya d'auke ta dakyar gabanin asuba cike begen Al'ameen ta ji an d'ad'a mata duka a cinya, a zabure ta farka zata zunduma ihu idanunta ya sauka akan Anty Esther, tuni ta ja bakinta ta tsuke tana zare ido.

Harara Esther ta watsa mata ta d'aura da "Sannu isasshiya, karfe bakwai da rabi kina kwance ki na barci, wa kike jira ya tashe ki. Common get up, stupid girl!" Ta karashe maganar a tsawace tare da mi'ka hannu kamar zata kai mata mari. Da gudu ta mik'e ta fad'a toilet ta rufo kofar ta murza key, jingina tayi da kofar ta fashe da kuka k'asa-k'asa don kar Anty Esther ta jiyo ta, sai da ta yi mai isarta babu mai rarrashi ta samu tayi wankan dakyar, a d'arare ta turo kofa ta lek'o, ganin Anty Esther bata d'akin yasa ta k'arasa fitowa da sauri, sharp-sharp ta shirya cikin uniform dinta ta sakko downstairs dauke da makeken school bag d'in ta mai tayoyi.

A dining ta tarar da David gaban shi shake da abincin kala-kala ya ci wannan ya ture ya janyo wannan, Harara ta watsa mishi a fakaice a ranta ta ce "Shege mayunwaci babu a hause anzo an samu na banza." Muryar Anty Esther ta jiyo daga hanyar kitchen tana tahowa,sai masifa take da hargagi da alama da kuku's take yi. Da sauri ta ja kujera ta zauna, cikin dan karkarwar jiki ta shiga kokarin had'a tea, David na kallon ta yana mata murmushin keta.

Bata wani ci abin kirki ba ta mi'ke, ganin David ya gama don kar tayi laifi, du k da haka bata tsira ba sai da Anty Esther ta zage ta tas, wai tsabar iskanci ta zuba abinci ta barshi bata ci ba. Kuka take son yi amma babu dama, Tana kallo David ya kwaso kayan kwalama dangin su cake, ice cream, chocolate, ya tula a jaka, sannan su ka fita sabon driver'n Mom ya d'auke zuwa school.

A cikin mota ta samu damar yin kukanta, kwantar da kanta a jikin kujera ta yi tana shesshekar kuka kasa-kasa, David dake gefenta ya kalleta yayi murmushi, cike da izgili ya ce "Yarinya ki kwantar da kai a gabana ki roke ni abin da kike so, zan taimaka miki." Harara ta watsa mishi ta dauke kai wani irin mugun haushin shi take ji. D'age kafad'a ya yi ya ce "kin huta."

Yau ma kamar jiya babu abin da ta tsinana a school d'in har sukayi closing.

Koda su ka koma gida yau ma bata huta ba, haka Anty Esther ta sakata a gaba kamar jiya, ko garden ta ki bari ta fita ta sha iska, wayarta take bukata ta kira Papa amma tsoro ya hana ta tambaya, tana ji a gabanta Anty Esther da Mom suka yi waya, amma Mom bata ce a bata ba, sai ma cewa ta yi wai a ci-gaba da tsareta kar a barta fita ko compound ne idan ba school zata je ba, kuma koda wasa kada a kuskura a bata waya, har sai ta dawo, daga nan kuma suka ci-gaba da wasu maganganu wanda tuni ta daina fahimtar komai saboda kukan da ya ci karfinta.

Kamar jiya tana samun kanta tuni ta manta da duk halin da take ciki, ta tsunduma tafkin begen abinda zuciyar ta ke bege.

**************

Bayan wasu kwanaki.

Sosai Amira ta dage da zuwa daukar karatu wurin Al'ameen, sai dai hakan ba abinda ya kareta da shi sai wani irin mahaukacin kaunar shi, a duk sanda zasu zauna karatu zuciyarta sake narkewa take da soyayyar shi, haka zata yi ta kallon shi wani bin sai Fatima ta ta'ba ta zata yi firgigit ta dawo hayyacinta, zuwa yanzu Ummi ta soma fahimta wani abu game da Amiran sai dai ta bar abin a zuciyar ta a tunda hasahse ne kawai take bata da tabbas. Shi kam Yaya Ameen bai fahimci komai ba, saboda kwata babu wata aba wai soyayya a gaban shi, sai dai ya kan rasa wani irin kallo ne yarinyar ke yawan bin shi da shi haka.

Ita kam a bangaren ta sosai lamarin ke damunta, duk wani salo da iyayi da zata yi don Al'ameen ya gane halin da take ciki ta yi amma a banza, hakan yasa ta sake tarar Zainabu da maganar, zee ta bata shawara kamar yadda ta saba, ta yi na'am da shawarar don a yanzu yadda take jin soyayyar shi, bata ki kowa ya sani ba don ta k'una bata tsoron kauri.

Yau ma kamar kullum ta shigo gidan bayan sallar isha'i, kasancewar an wuni ruwan sama gari yayi sanyi, yasa Ummi basu zauna a tsakar gida kamar yadda suka saba ba, a falo ta same su gaba dayan su harda Al'ameen d'in da dawowar shi gidan kenan, ya mutsa fuska ya yi lokacin da ya ji sallmarta, baya jin dadin jikin shi tunda rana karfin halin kawai yake yi, ga wani sanyi-sanyi da yake ji yana shigar shi.

gaban Ummi ta zube ta kwashi gaisuwa, sannan ta juyo bangaren sa, cikin wata irin narkakkiyar muryar ta ce "Ina wuni Yaya Ameen." Ya amsa da "Lafiya kalau." Yana dauke kai daga gareta don take kamshin wannan mayataccen turaren nata na ran nan ya mashi sallama, dafe kanshi daya fara Sara mishi ya yi.

Fatima ce ta gaisheta, ta amsa cike da kulawa kafin ta samu waje kusa da ita ta zauna, ta saitin shi yadda zata samu damar satar kallon shi hankali kwance.

Ya fi minti uku a haka kafin ya dago, carat idanunsu ya sarke dana juna ba tare da ta ankara da zai dago ba, da sauri ta kawar da kanta don bazata iya jurar hada idanu da shi ba, muryar shi ne ya dawo da ita hayyacinta "Amm! Amira ki yi hakuri kike gida yau baza mu saka yin karatu ba, Bana jin dadin jikina."

Jin haka yasa Ummi kallon shi da sauri, ta katse shi da cewa "A'a yayan Fatima baza ayi haka ba, tunda ta riga ta zo, ka koya mata ko kadan ne."

Shiru ya dan yi kafin ya amsa da "To Ummi." Baya iya mata musu matukar akan abinda bai fi karfin shi ba ne.

Mikewa yayi ya kalli Fatima ya ce "Ku muje dakin zaure taskar gida a kwai sanyi." Daga haka ya fice, Ummi ta so tsayar da shi suyi karatun a falonta ganin ya riga ya fice yasa ta kyale shi.

Fatima ce a gaba Amira na biya da ita suka shiga dakin bayan ya amsa musu sallama, lumshe idanu Amira tayi lokacin data shaki daddadar kamshin turarensa da take maitar son ji kullum. Dakin tsab da shi a tsabtace kamar ba dakin saurayi ba.

Cike da karfin hali da jarumta ya fara koyar da su, sai dai ko minti goma basu dauka ba ya fara neman fita hayycinsa, rintse idanu ya yi, yana jin yanayin shi na canjawa, gefe daya ga wani shu'umin kamshin turaren da yake shaka na neman hallaka shi.

Babu shiri ya dakata, ya kalli Amira da kyar ya ce "Amira kije kawai gobe ki dawo, bana jin zan iya karatu yau, na so na koyar da ke kamar yadda Ummi ta saka ni amma bana jin zan iya."

Cike da matsanancin tausayin shi ganin yadda idanun shi suka rine, ta ce "Toh Yaya, Allah ya saukawake." Da kai ya amsa mata don baya jin zai iya bude baki ya yi magana, a rude Fatima ta shiga jeromai sannu, da kai ya ke amsa mata, tuni idanunta ya ciki da kwalla, da hannu yayi musu alamar su tafi kawai, jiki duk a sanyaye suka mike, har sun kai kofa, cikin wata irin wahalalliyar murya ya kira sunan Fatima, duk dakatawa suka yi, ya ce "Kar ki gayawa Ummi halin da nake ciki bana son hankali ta ya tashin, kin ji ko. " ta gyada kai tana sharar kwalla, cikin shesheka ta ce "Yayana to kasha magani." Ya ce "zan sha yanzu nan." Ta amsa da "Toh ."suka fice.

Da kyar Amira ta tafi gida ranar, barci kuwa kaurace mata ya yi juyi ta dinga yi, tana ji kamar ta koma ta kara duba shi duk da dare ya tsala, karshe dai ta lallaba tayi alwala ta yi nafila ta shiga nema mishi sauki a wajen Allah, tare da mika nata kokon baran.

Kwanar wahala Al'ameen ya yi a wannan dare, tunda yake ciwon shi bai taba tashi da karfi irin na yau ba,ya sha maganin shi amma a banza, jarumta ce kawai ta hana shi sumewa a cikin daren nan.....

*Jama'a masoya masu bibiyar littafin JOY, pls Ku kara hakuri da ni, wallahi kwana biyu nan nayi busy da yawa, amma insha Allah zuwa ranar Monday komai zai daidaita daga ranar zaku dinga samun update kullum, harda weekend bi iznillah na muku alkawari ni dai kawai comment dinku da addu'ar Ku nake bukata, sai kuma shearing fisabilillah* 🙏
[12/29, 2:39 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀

~FARHAT~

DAGA ALƘALAMIN
*AyshaNalado*👉

ƘARƘASHIN JAGORANCIN👉
*Mikiya Writers Association*

*PAGE 21*
Chapter 22 · 0% Book details