Sashe 37
Joy Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Umh! Wato shi kadai ki ka zo gani ko banda ni, to kin mak'aro yarinya ya fita." Narai narai ta yi da ido ta ce "Da gaske?" Cikin dariya Fatima ta ce "Ah swear!" "Ok bari na tafi, idan ya dawo ki fara Isar min da sakon godiya, kice nace turaren yana da kamshi wai tunda nake ban ta6a jin turaren mai dadinsa, kar ki sanarwa Ummi zuwana pls zan dawo may be gobe." Fatima ta ce "Oh naso kuwa na baki wani labari mai dadi, tunda kina sauri shikenan, kuma labarin ya shafi Yaya Ameen." A d'okance ta ce "Pls ki fara fad'a min Teetee ko Kad'an ne." "A'a ki tafi kawai bana son Mom ta miki fad'a, ranar Monday zan gaya miki a School." Riketa ta yi tamau ta ce "Ban yarda ba, sai kin fad'a min." "Ok to sake ni." Sake ta yi ta ce "Oyo tell me." Shammatar ta Fatima ta yi ta kwasa da gudu tana cewa; Sai Monday."
A jigace ta yunk'ura ta mike zaune, lamarin da ya kusa zautar da Aysha tsabar mamaki, saboda rabon da ta iya mik'ewa ta zauna da kanta haka har sun manta, kullum sai dai a kwantar a tayar, bata damu da irin kallon da Aysha ke mata ba ta ce da muryarta wadda bata fita sosai saboda jigata "Da gaske ki ke Aysha Yaya Ameen ya shigo gidan nan duba jikina?" Aysha ta ce "Ya shigo mana Anty zan miki karya ne." Ga mamakinta wani Busasshen murmushi taga Amira ta saki wanda rabon da ta yi irinsa har sun manta sai kuma ga hawaye shar yana bin kumatunta,, murya ciki ciki ta ce " Tabbas ban yi farin ciki da wannan barcin da na yi ba, domin yayi mini shamaki da ganin rayuwata." "Anty mai Ki ka ce? "Ban ce komai ba Aysha." Gyada kai Aysha ta yi wani tunani na zuwar mata a kwakwalwa, da sauri ta d'ago ta kalli Amira ta ce "Yaya ina zargin wani abu, kar dai kice min soyayyace silar damuwarki?" Kura mata ido Amira ta yi, dai dai lokacin Zainabu ta yi sallama a k'ofar d'akin tare da kutso kai, gaban Aysha ta tsuguna tare da dafa kafadarta ta ce "Kwarai kuwa Aysha zarginki ingantacce ne, ranar wanka ba'a boyar cibiya." Ajiyar zuciya ta sauke, tiryan tiryan ta shiga labarta mata komai, tausayin Amira ya saka Aysha kuka kashir6an, cikin shessheka ta ce "Dama na dad'e ina zargin Anty Amira na son Yaya Ameen, amma ban ta6a tunanin shine matsalar larurarta ba, da tuni na bankad' sirrin kowa ya ji, dan bazan yarda na rasa yar uwata ba ina ji ina gani, amma ko yanzu bata 6aci ba." Ta kai karshen maganar tare da mikewa a fusace, riko hannunta Zainabu ta yi ta ce "kar ki yi haka Aysha abi komai a sannun." Komawa ta yi ta zauna tare da dafe kai ta ce "Gaskiya Yaya Ameen bashi da tausayi, ko dubata bai ta6a shigowa yi ba fa Anty Zainabu" "Kar kiga laifin shi Aysha bai san komai ba sai jiya." Nan ta kwashe yadda su ka yi da shi jiya ta fada mata. Ta daura da "Tun sa kika ga ya biyo baya ina ga akwai alamun nasara abin ba sai ya kai ga manya ba." "Allah yasa" Cewar Aysha.
kamar almara ranar a zaune Amira ta wuni sa6anin kullum da take wuni kwance, sai gata harda dan cin abinci, Tsabar farin ciki Mama da gudu ta garzaya ta sanarwa Ummi don abokin kuka da shi ake dariya.
Hamdala Ummi ta shiga yi, ranar da wannan zancen ta wuni duk wanda ya shigo gidan kuwa da maganar take fara taron shi.
Cikin sa'a karfe shidda Al'ameen ya dawo, da wannan zancen Ummi ta tare shi fuskarta a washe, murmushi yak'e ya kirkiro ya yi tare da cewa "Alhmdllh kai na yi murna Allah ya kara mata lafiya." Jiki a sanyaye ya juya ya koma d'akinsa, kimtsawa ya yi, ya tafi masallaci, daga masallaci direct gidan su Amira ya nufa, a lokacin duhu ya fara.
Sam ta ki yarda ta sake komawa barci tun bayan wanda ta yi da safe wanda ta yi mishi lakabi da barcin shamaki, tun karfe biyar take ta zuba idon ganin shi amma shiru, shidda ya yi da rabi ya wuce har magrib zuwa lokacin ta fara sarewa, silalewa ta yi ta kwanta ta lumshe idanu hawaye na bin kumatatunta. Kamar a mafarki ta tsinaka yi sallmarsa a cikin dodon kunnenta, kafin ta gama tantance a wani hali ta ke ta sake jiyo muryar Mama tana cewa "Tana d'akinsu, Aysha yi wa Aminullahi iso." Kur! Ta kurwa k'ofar dakin idanunta masu danshi ya yin da bugun zuciyarta ya tsananta..........
Haka so yake d'iba ya maida kai bawa🎶🎶🎶🎶 Allah sarki Amira. Y'an term d'in sannunku hwa 😬
[12/29, 2:46 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀
~FARHAT~
*PAGE 34*
Har ya k'arasa shigowa d'akin jikakkun idanunta na kafe a kan fuskar shi, ta kasa koda keftawa, gani take yi idan ta rintse ido ta bud'e zai 6acewa ganinta. Aysha ce ta bashi wajen zama kafin ta fice daga d'akin ta basu guri. Sai lokacin ya samu damar sauke idanunsa a kan ta, wani irin kwance-kwance gabansa ya yi ya fad'i, Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun! ya ambata a zuciya. hankalinsa ya yi k'ololuwar ganin gaba d'aya yadda ta rame ta lalace, ta fice daga hayyacinta kamar na Amiran daya sani ba, take tausayinta ya yi wa zuciyarsa kawanya.
Sassanyar Muryarta daya ratsa dodon kunnesa ya jawo hankalinsa, cikin maganarta 'kasa-k'asa irin ta majinyata take cewa; Yaya Ameen kaine da gaske! Ba gizo idanuna ke min ba, A she zan sake saka ka a idanuna kafin na amsa kiran mahaliccina, nagode sosai da ka zo gareni na yi farin ciki, nagode sosai." Ta karashe maganar tana sakin murmushi, hawayen soyayyarsa na kwaranyo mata ba tare da tasan da kwaranyarsu ba.
Jikinsa ne ya yi sanyi kalau! Gefe guda kuma wani irin kunyarta ya ji ya lullu6e shi, sai ya samu kansa da kasa ci gaba da kallon idanunta. Lallai zuciyar so makauniya ce, duk irin abin da ya aika ta mata Sam! bata ga laifinsa ba, bata yi fushi ba, wata d'aya da kwanaki ta kwashe cur! Tana jinya saboda soyayyarsa, bai ta6a koda aikowa bane yace ace mata sannu, amma take mashi godiya don yau ya shigo dubiyar da bata kai zuci ba.
Dakyar ya d'ago idanunsa da ke kyallin hawayen tausayinta ya sake kallota, da wani irin sassanyar murya ya ce " *Meerah* ya jikin ki."
Kusan suman wucin gadi ta yi, don lokacin da tattausar murya shi ya ratsa kunnenta, cak bugun zuciyarta ya tsaya, kamar sabuwar makauniya haka ta kure fuskar shi da kallo ba tare da ta amsa mishi ba.
Ganin haka yasa ya yi karfin halin sakar mata tattausar murmushi, abin da ya yi sanidiyar lumshewar idanunta a hankali ta sake budewa a kan shi, still murmushin na nan bai 6ace a fuskar ba, cikin k'asa k'asa da murya ya sake kira sunanta da cewa "My Meerah."
Gudun wahayenta ne ya ninku, la66anta ne su ka kama rawa alamar tana son furta wani abu amma ta kasa, gyada mata kai ya yi ya ce "Yess My Meerah, do u lik d name? Bata iya amsa tambayar ba, sai kawai ta tsinci kanta da rintse idanu tare da furta "Ya Allah na roke ka, kar ka farkar dani daga wannan daddadar barcin da nake yi, Ya Allah ka dauwamar dani a cinkasa." Ta karashe maganar da fashewa da kukan da ita kanta bata san na mai zata kira shi ba.
Bai san sanda ya isa gabanta ba, cike da tausayi ya shiga share mata hawaye, cikin rad'a ya ke cewa; It's reality Meerah ba mafarki bane, nine Ameen d'in ki a gabanki, bud'e idanunki ki kalleni." Samun kanta tayi da budewar kamar yadda ya umarta, suna hada idanu ta mika hannu ta kama nashi ta rike gam! Cikin kuka da fitar hayyaci ta ke cewa; Dan Allah Yaya Ameen kar ka barni, ka tsaya a tare dani ka dauwama a tare dani, kar ka gusa kusa dani na roke ka, yin hakan daidai yake da yankewar numfashi na, bazan iya rayuwa ba tare da kai ba, Ina son ka Ameen, ina son ka ina son ka, kaine rayuwata farin ciki na, idan babu kai a duniyar Amira zan zamo kamar mutum mutumi." Ta karashe da fashewa da wani irin kuka mai narka zuciyar mai sauraro.
"Shiii! ya isa Meerah, ga Ameen a gabanki, na yi miki alkawarin zan rayu dake zan zamo maji6ancin rayuwarki insha Allah." Ya fad'a cikin wani irin amo wanda yake fitowa tun daga kasan zuciyarsa.
Sun dad'e a haka hannun shi, cikin nata, dakyar ya lalla6a ya zare hannunsa tare da komawa mazauninsa ya zauna, yana ci gaba da gaya mata kamalai masu kwantar da hankali, sai ga Amira tana dariya kamar wayiya, kallonta yake cike da tausayi tare da kara tabbatar da cewa lallai shine farin cikinta.
kiran isha'i ne ya tayar da shi, kafin nan sai da ya yi mata alkawarin shigowa da safe ya dubata kuma ya jaddada mata ta tabbatar ta ci abinci da yawa.
Cikin kwana uku da faruwar haka sai ga Amira ta gyagije ta mike tsaye kan kafafunta, kamar ba itace a kwance rai a hannun Allah ba, lamarin da ya baiwa kowa matukar mamaki banda Aysha Fatima da Zainabu da su ka san abin da ke ciki.
Al'ameen yana iya kokarinsa wajen ganin ya wanzar da farin ciki a gareta, kullum yakan shiga ya dubata suyi hiran hakan ya jefawa Mama zargin wani abu a zuciyar ta, Fatima kam kusan tafi kowa farin ciki don tsakanin ta da Allah har zuciyar ta take kaunar Anty Amira, ba don warning din da Al'ameen ya mata akan kar fa fadawa Ummi ba, da tuni ta fada, duk da haka takan yi su6utar baki wani bin.