← Book details Joy Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 46

Sashe 35

Joy Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallo d'aya ta ma shi zuciyar ta ya bata cewa shine, tabbas bata ta6a gaskata zantukan Amira ba sai yau da ta yi arba da shi, gaba daya duk wani karsashinta sai ya nemi arcewa ya barta, dakewa ta yi ta karfafa zuciyarta, tuna halin data baro Amira a ciki, duk da haka ta kasa kallon shi cikin ido , sai Aliyu ta kalla ta ce "Barkan mu da yamma." Kamar yadda shi take kallo take magana haka zalika shi ya amsa mata da cewa "Yawwa barkan ki dai." Ta ce "Sunana Zainabu, kaqar Amira, idan babu damuwa ina son yin magana da Al'ameen." Sai lokacin ya sake kai kallonsa gareta gabansa ne ya shiga faduwa jin ta ambaci Amira, kallon shi Aliyu ya yi, yana jira ya ji ta bakin shi, ganin bai tanka ba yasa ya ce "Bismillah! Yana saurarenki bari na baku wuri" ya fada yana kokarin mikewa, da sauri Zainabu ta ce "A'a ka zauna zan yi maganar a gabanka ka zama sheda don naga kamar kai abokin shi ne." Ya ce "Ya ce OK to shikenan." Shiru ta yi na yan sakanni kafin ta yi karfin halin d'agowa ta sauke kallon ta a kan shi shima ita yake kallo har lokacin ta ce, "Shin kasan cewa wannan ciwon da amira ke yi ciwon sonka ke ne? Kasan cewa idan ba ka kawo dauki gaggawa a gareta ba tabbas soyyarka zata zama ajalinta? Nasan duk baka sani ba, to yanzu na sanar maka, Wallahi Al'ameen idan ka rasa Amira ka yi asarar masoyiya, ka dubi girman Allah ka amshi soyayyar ta kodon ceton rai, wallahi muna gaf da rasata kuma idan ka bari hakan ta kasance sai munyi Sharia da kai a kotun Allah." Ta karashe maganar tare da fashewa da matsancin kuka, kasa tsaywa ta yi da gudu ta bar wajen ta shige gidan su Amira, Fatima da ta yi suman tsaye ne tun da ta kunnayenta suka jiyo mata maganganun Zainabu ta fito zata shige gida ne, ta karaso gaba su da sauri cikin kidima da rawar muryar ta ce "Ya Yaya da gaske ne ciwon soyayarka ne ya mai kwantar da Anty Amira? " Kallon ta yake yi kamar mutum mutumi ya kasa koda gyada kai ne, hawaye ne suka Shiga gudu a fuskarta, da sauri ta mike tana girgiza kai sani kuma ta juya da gudu ta shige gida tana kwala kiran sunan Ummi, sai lokacin ya Ankara da tashin ta "Fatimahhhh!" Ya kwala mata kira amma ina! Tuni ta shige "Innalillahi wa inna ilaihinr rajiun." Ya fada yana dafe kanshi dake Sara mishi kamar zai rabe biyu..........

09116099486.
[12/29, 2:45 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀

~FARHAT~

*PAGE 32*

Tana kaiwa dai dai tsakiyar zauren gidansu ta jiyo muryar shi cikin wani irin sauti kwala kiran sunanta, cak! Ta tsaya ta kasa ci gaba da gudun, sai dai kuma ta kasa dawowa gare shi, sai samun kanta tayi da durkushewa a zauren ta sake fashewa da wani irin kuka mara amon sauti, kukan tausayin Amira, dama ta dad'e tana zargin wani abu a tattare da Amira game da Yayanta sai dai bata ta6a tunanin lamarin har ya kai haka ba, take ranar da ta ga Amira ta fito daga d'akin Al'ameen tana kuka ya shiga dawo mata.

A can kofar gida kuwa, dafa kafad'ar shi Aliyu ya yi, a hankali ya d'ago kaifafun idanunsa da lokaci guda su ka canza launi ya watsa ma shi,kallon cikin idanun juna su ka yi na y'an sakanni, Kafin Aliyu ya lumshe ido ya bud'e tare da cewa a sanyaye "It's time 4 prayer, muje masallaci." Bai amsa shi ba, don baya jin zai iya bud'e baki ya yi magana, mik'ewa ya yi jikinsa a matuk'ar sanyaye, su ka nufi masallacin kusa da gidan.

Bayan sun idar da sallah, hannaye Al'ameen ya d'aga sama ya shiga kai kukan shi ga mahalici, ya dad'a yana kwararo addu'o'i har sai da kusan kowa ya watse a masallacin, bai sauke hannayensa ba. Aliyu na daga gefen shi yana amsawa da amin duk da ba jin abin da yake fad'a yake yi ba don a zuciya yake yi.

A tare suka shafa addu'ar, shi ya fara mik'ewa ganin haka yasa Aliyu ya biyo bayan shi. Tafiya suke yi a jere sai dai babu wanda ya ce wa d'an uwansa kanzil, daurewa kawai Aliyu yake yi ya hana kansa magantuwa ganin halin da abokin nasa ke ciki, amma bakinsa fal! yake da tarin tambayoyi, Kansa gaba d'aya a k'ulle ya ke.

Mazaunin su na da suka koma suka zauna, shiru ne ya gifta a tsakanin na wasu mintuna, Aliyu dauriyarsa ya k'are don gabansa fad'uwa kawai yake, har ya bud'e baki da nufin magantuwa, Ya tsinkayi muryar Al'ameen cikin wani irin amo mai nuni da cewar tabbas maganar da zai fad'a mai girma ce, ya ce"Aliyu! Banda Allah mahaliccina, bayan ni kaina da kuma likitan daya d'aurani a kan magani, Kai ne mutum na uku da na za6a kasan sirrina, hakan kuma zai faru ne saboda na yarda da kai, na dauke ka d'an uwa amini abokin kuka wanda hausawa kan ce ba'a boye masa mutuwa." Gyada kai Aliyu ya yi cike da gamsuwa da bayanansa, shiru Al'ameen ya yi na wani dan lokaci, kafin daga bisani ya sauke kakkarfar ajiyar zuciya a hankali ya bud'e baki tiryan-tiryan ya shiga bawa Aliyu labarin ciwonsa tun daga lokacin daya fara fuskantan matsalar har zuwa kan yanzu da larurar ke mataki na biyar a jikinsa.

Dagowa Ali ya yi idanunsa jajur yace "Wacece Amira? Menene alakar ka da ita." Nan ma bai yi k'asa a gwiwa ba wajen zayyanewa Aliyu wacece Amira da alak'arsu tun daga farko har zuwa yau , ya daura da cewa "Aliyu ban sani ba cewa akan soyayyata ne ta ke wannan ciwon, ban yi zaton lamarin ya kai girman haka ba, abin da na sani kawai bana son ta."

Shiru ne ya biyo baya, gaba d'aya jikin Aliyu ya yi la'asar, lamarin ya sosa ransa fiye da zaton mai zato, gaba d'aya tausayin Al'ameen da ahlinsa harma da Amira ya gama cika masa zuciya, a iya hasashensa babu wata mafita data wuce wacce Dr Abdul ya fad'a, to amma ta yaya hakan zai kasance.

Ajiyar zuciya Aliyu ya sauke ya d'ago ya ce "Abokina na tausaya maka kwarai, sai dai naga zallar wautarka, shin me yasa ka za6i ka kassara rayuwarka akan ka yi Aure, kula da Ummi da Fatima kadai bai isa hujja ba, ka gwammace ka mutu a tsaye a kan ka yara sunnar ma'aiki, wallahi na tabbata idan Ummi ta ji wannan maganar sai ta zubar da hawayen bakin ciki da takaici, kana fa da ilmin addini daidai gwargwado, kana da tabbacin zaka iya rike kanka har zuwa lokacin da ka yanke wa kan ka yin aure, kana da tabbacin kwayoyin maganin da kake sha zasu ci gaba da rike ka har zuwa lokacin da ka d'ibarwa kan ka?" Girgiza kai Al'ameen ya yi ya ce "Ba ni da tabbas abokina yanzu menene mafita." Aliyu ya ce "Da gaske ka dauke ni amini abokin shawara kamar yadda ka fada?" Gyada mashi kai Al'ameen ya yi ba tare da ya iya bud'e baki ya amsa shi ba, "To mafita shi ne ka jefi tsuntsu biyu da dutse d'aya." " Kamar yaya?" Ya tambaya cikin rashin fahimtar inda maganar Aliyu ya nufa, kallon shi ciki ido ya yi ya ce "Ka Auri Amira." "Na auri Amira?" Ya maimaita maganar cikin sigar tambaya, Aliyu ya ce "E ." girgiza kai ya yi ya ce "Bazan iya ba zan dai taimaka mata ta wata hanyar." A harzuk'e Aliyu ya ce "Ya zama dole ka iya, dole ka auri yarinyar nan Ameen." "Akan me zan aureta ba bayan bana son ta, ita fa zuciya ba a yi mata tilas." Ya amsawa Aliyu shima a fusace, mikewa Aliyu ya yi ya ce "Na sani Ameen zuciya ba'ayi mata tilas, amma ka sani a wannan ga6ar ba maganar so ko kiyayya ake yi ba, magana ake ta ceton rai da rai " Yana gama fad'in haka ya juya ya kama tafiya ba tare da ya sake kallon Al'ameen ba.

Da kallo Al'ameen ya bi shi, zuciyarsa na harbawa, shin ya tsayar da shi ne ko ya k'ale shi? Ya fi minti goma yana bin haryar sa Aliyu ya bi sa kallo, a zuciyarsa yana taraddadin mai Aliyu zai yi? Ya fi kowa sanin Aliyu, ya san dai tunda ya ce dole yana nufin dolen ne, sai dai komai zai faru ya faru, fatan shi dai kar Ummi ta ji wannan batu, Rass! Gabansa ya fad'i lokacin da ya tuno da Fatima, a hargitse ya mike, shaf! Ya manta cewa ta ji, ya tabbata ya zuwa yanzu Ummi ta san da maganar, da sauri ya nufi cikin gidansu, sai dai tuntu6en da ya yi da abu a zaure ya dakatar da shi, kafin ya gama tantance da mai ya yi tuntu6e shesshekar kukanta ya cika mishi kunne, "Fatima!!!" Ya ambata a tsorace, yana kokarin haska tocilar wayarsa, itan ce kuwa kamar yadda ya yi hasashe, da sauri ya d'ago ta yana cewa; Menenen Fatima me ya faru, ina Ummi?" A rud'e ya shiga jero mata wad'annan tambayoyin. jikinsa ta fad'a tare da sake rushewa da kuka, k'ofar d'akinsa ya bud'e ya ja hannunta a su ka shiga, ya mai da k'ofar net d'in ya rufe.
Chapter 35 · 0% Book details