← Book details Joy Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 46

Sashe 25

Joy Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gaba daya ta koma so silent, bata da aiki sai rubuce rubucen kalaman soyayya, sai ko kuka da ya zama mata kamar ibada, tuni ta yi rama ta dishe.

kwarafniyar Anty Esther tuni sun daina gigitata, gani take hargagin Mom da anty Esther ya fiye mata sauki akan tashin hankalin dake tunkarota, zuciyar ta na daf da yi mata bore, sai dai ta lashi takobin ko zata mutu bazata ta6a bata dama ba, don tana ganin yin hakan tamkar tarwatsa rayuka ne, gara ita nata rauyuwar ya tarwatse.

Tuni anty Esther ta bata wayarta, sai dai abin mamaki tunda ta karbu wayar Papa bai taba kiranta ba itama idan ta kira shi baya dagawa, idan ya daga ma da sun gaisa sama sama zai kashe gaba daya ya dena nuna mata kulawa kamar da. Bata wani dauki abin serious ba ta mishi uzuri don a ganinta aiyuka ne suke sha kan shi.

A cikin wannan dan tsukin girgin su Mom ya yi dirar mikiya a 9ja, ko gezau bata yi, babu yabo babu fallasa a tare da ita, suka dunguma ita Anty Esther, David, zuwa airport don tarbota, babu wani karsashi ko kewa a ranta su ka iso, lokacin tuni jirgin ya sauka, da sauri Mom ta iso gareta tare da rungumeta, lamarin ya dan so ya daure mata kai, amma tuna yadda Mom dinta ke matukar kaunarta, ada kafin ta soma canzawa yasa ta saki jiki itama ta rungumeta, cikin kunnenta Mom ta rada mata "I missed u a lot daughter." "I missed u 2 my Mom." Ta amsa mata.

"Ki yafe min abubuwan da suka yi ta faruwa a dan kwanakin nan, kuskurene." Hawaye ta ci ya ciki mata idananu, "take daskararriyar soyayya ta fara narkewa." Tsaki Anty Eshart ta za a bayyane, tare da kauda kai zuciyar ta na tafasa, murmushi Mom ta yi, ta saki joy ta rungume Eshart tana cewa "Oh! I'm Sorry my dear sister. Na yi kewarta sosai ne shiyasa." Daga haka ta rungume David da shima yake mata sannu da zuwa, hannunta sarke da na Joy suka shiga mota, Joy na kwance a jikinta har su ka iso gida.

Duk da izza da dagawa irin na Mom, ma'ikatan gidan sunyi murna da dawowarta, daga yadda suka dinga zuwa kwasar gaisuwa kowanne baki har kunne zaka tabbatar da hakan, ko ba komai zasu rabu da masifar Esther.

Ranar Joy na makale jikin Mom din ta, tana lelenta kamar yar five years abinda ta dade rabonta da gani daga Mom din hakan yasa ta saki jikinta sosai ta wuni da farin ciki, koda lokacin barci yayi har daki Mom ta rakata ta tayata shirin barci ta kwantar da ita ta kashe mata wuta sannan ta barta ba yan ta yi kissing forehead din ta tare da shafa kanta.

Mom na fitowa daga d'akin Joy ta tarad da Esther tsaye tana Binta da wani irin kallo, hannunta Mom ta kama ta jata su ka bar wajen, d'akinta ta nufa da ita sunan shiga Esther ta fisge hannunta daga na Mom, tare da watsa mata wani lalatatcen kallo, ajiyar zuciya Mom ta sauke a tausashe ta ce "I'm sorry Esther. Ba abinda kike tunani ba ne." Cikin daga murya ta ce "Ta Yaya zan tabbatar da haka ba yan kina aikata sabanin abin da kika sanar min, na gani lokaci yayi da ya kamata ki cika alkawari." "Calm down Esther ki saurare ni." Daga mata hannu ta yi a zafafe ta ce "Bazan saurare ki ba, zan bar gidan nan don bazan zauna bakin ciki ya kashe niba." Daga haka ta tuya ta fice daga dakin fuuu! A fusace.

Dabass Mom ta zauna tare da rafka tagumi.

Washegari da duku duku safiya Anty Esther ta fito da jakar kayanta ta bar gidan.

**********

*Al'ameen*

Kwata kwata babu sauki a cikin lamuran sai ma kara tabarbarewa da abubuwa ke yi I zuwa yanzu tab! biyar yake sha kafin ya samu relief........

Ga mai bukatar shiga group.

09116099486.
[12/29, 2:40 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀

~FARHAT~

DAGA ALƘALAMIN👉
*AyshaNalado*

ƘARƘASHIN JAGORANCIN👉
*Mikiya Writer's Association*

*PAGE 23*

*AL'AMEEN*

Kwata-kwata babu sauk'i a cikin lamuransa, sai ma kara ta6ar6arewa da abubuwa ke yi i zuwa yanzu tables biyar yake sha kafin ya samu relief, yana cikin matsanancin damuwa, tuni ya fara rama a tsaye.

Ba Ummi ba hatta fatima sai da ta fahimci Yayanta na cikin damuwa, don gaba d'aya ya sauya mata, ko magana yanzu bai cika yi ba, haka firan dare, da ya dawo zai shiga d'aki ya kulle ya kwanta da safe ya fito da idanu jajur kamar gauta a kumbure idan ta tambaye shi ya ce babu komai, tuni duniyar ya fara mata zafi, take kewar aminiyarta ya dawo mata sabo fil dama shi ke dauke mata hankali akanta ba wai don ta manta da ita ba.

Ummi kam damuwar da ta shiga ba'a magana, matsayinta na uwa lamarin ya shigeta matuk'a gaya, tsoranta Allah kar ace shaye shayen nan na zamani Al'ameen d'in ta ya fara, a duk sanda ta yi wannan tunanin, takan shiga kololuwar ta shin hankali, har ta zubar da hawaye, ta zauna da shi ba sau daya ba ba sau biyu ba cikin lalama da dabara ta naimi jin damuwarsa, amma ya ki fad'a mata, sai dai ya girgiza kai ya ce mata "Babu komai Ummi, kawai gajiyan aiki da karatu ne, sai mura da ta saka ni gaba a yan kwanakin nan ki taya ni da addu'a." Ba dan ta yarda ba, dole take hakura, ta san tunda ya nace a haka bazai fada mata ba ne, ta fi kowa sanin halin zurfin cikin shi tun yana dan kankanin yaro.

Da misalin karfe takwas na dare ya shigo gida kamar yadda ya saba, sunan zaune jigum jigum a tsakar gida, duk yadda Ummi take da son sauraren redi'o yau rediyon nata a kashe yake carbi ne rike a hannunta tana ja, Fatima kam notebook din ta ne a gabanta data dauko zata yi karatu amma ta kasa, ta ajiye ta rafka tagumi.

Kallo daya Ummi ta mishi ta kauda kai gefe, sai ga hawaye shaaa! Duk yadda taso ta kauce kar ya gani abin ya ci turo.

Da sauri ya kara sa shigowa, zubewa yayi a gabanta hankali tashe, ya ce "Subhanallah! Ummi." Daga mai hannu ta yi ta ce "Karka kira sunana Al'ameen ni ba Umminka ba ce, ka tashi a gabana." Ta karashe maganar tare da fashewa da kuka mai karfi, Fatima da maganar Ummi ya dawo da ita hayyacinta, rarrafowa tayi ta fada jikin Ummi ta fashe da kuka itama, cikin kuka ta ke cewa "ki yi hakuri Ummi, ki yi hakuri ki yi shiru." Rungumeta Ummi ta yi su ka ci gaba da rera kukan a tare.

Kololuwar tashin hankali Al'ameen ya shige shi, zuciyar sa tuni ta shiga wani irin tsalle kamar zata faso kirgi ta fito, rasa abin yi yasa shi fara zubar da zazzafar hawaye da , sai kawai ya rungume su gaba daya, cikin zubar hawaye da kunar rai ya ce "Ki yi hakuri mahaifiyata ki dena zubar da hawayenki a kaina, na tuba nabi Allah na bi ki." Kalmomin da ya dinga maimaitawa ke nan kamar karatu.

Sun dauki tsawon lokaci a haka, kafin Ummi ta tattare d'an jarumtarta ta danne zuciyarta, ta zame su daga jikinta ta dago ta kalle shi cikin ido ta ce "Al'ameen shaye shaye ka fara?"da wani irin sauri ya kalle ta yana girgiza kai, ta ce "Karya ka ke yi, idan ba haka ba kuma ka sanar dani damuwar ka, don na tabbata a kwai abin da ke damunki ji yadda ka koma gaba daya ka lalace cikin yan watanni, bazan jura ganin ka haka ba Aminullah."

Shiru ya yi yana kallonta bazai iya yi mata karya ba, kuma bazai iya fitowa kai tsaye ya sanar da ita damuwar shi ba, duk da yasan bashi da kamar ta duk duniya, yana matukar jin nauyinta, kasa ya yi da kai ya ce "Ki yi hakuri Ummi, bazan iya yi miki karya ba, kuma bazan iya sanar miki damuwata ba, amma wallahi tallahi bana shaye shaye, ki taya ni da uddu'a Ummina."

Boyayyar ajiyar zuciya ta sauke ko babu komai ta samu saukin kaso ashirin cikin damuwarta kashi dari.

Sai dai ko da wasa bata nuna a fuska ba, mikewa ta yi ba tare da ta kalli gefen da yake ba ta shige daki.

Fatima ma mikewa ta yi zata bi bayanta, har lokacin kuka take yi, da wani irin raunatacciyar murya wanda basu san shi da shi ba ya kira sunan ta "Fatima." Dakatawa ta yi da tafiyar ta juyo tana kallon shi tana shesheka, girgiza mata kai ya yi tare da cewa "Shiiiiii!" Alamar ta yi shiru, sai kuma ya yi mata alamar ta zo da hannu, da sauri ta karasa gareshi ta fada jikin shi, ta sake fashewa da kukan da dama ba wai ta dai na ba ne. Rumgumeta ya yi, wani irin rauni na kara kaiwa zuciyarsa farmaki.

A yau ya kara tabbatarwa, shine cikin farin cikin yar uwarsa tilo, da kuma mahaifiyarsa wacce itace komai na shi a rayuwa.

Muryarta ne ya katse masa tunani, cikin shesheka take cewa "Yayana ka canza, yayana ka dawo kamar yadda ka ke da don Allah, da ni da Ummi muna cikin damuwa kai ne haske ka jagoran rayuwar mu." Bubbuga bayanta ya shiga yi, ba tare da ya iya bude baki ya amsa mata ba, sun dauki tsawon lokaci a haka, kafin ya samu ta yi shiru, sai ajiyar zuciya da take saukewa jefi jefi.

Dagota ya yi daga jikinsa ya shiga share mata hawaye, yana yi yana cewa "Kar ki sake yin kuka My luv na miki alkawarin zan dawo muku da farin cikin ku ke da Ummi. Al'ameen din Ku zai dawo Yaya Ameen din ki zai dawo kin ji ko." Ta gyada kai ya ce oya wuce kije ki kwanta,

Babu musu ta wuce shi jiki a sanyaye, sai da yaga shigewarta daki sannan ya kwashe tabarman ya jingine, kamar mara laka haka ya nufi dakinsa.
Chapter 25 · 0% Book details