Sashe 34
Joy Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Kuka Ummi ta yi sosai, Mama na rarrashinta cikin karfin hali da danne zuciya, bayan ta tsagaita ta dago ta kalli Mama tare da cewa "Hafsatu mai ke damunta haka?" Take Mama ta kwashe komai ta gaya mata ba tare da tare da rage ta da komai ba, itama dai aljanan ta fi baiwa karfi, don ko kusa babu wanda zai kawo wani tunani makamancin soyayya a cikin lamarin. Addu'a Ummi ta sauna ta dinga tofa mata har wuraren bakwai na safe, har zuwa time din bata farka ba, sallama Ummi ta musu a kan zata je gida ta dawo..........
Dan Allah Ku yi hakuri da jina shiru kwana biyu Mamana ce bata ji dadi ba, bana samun zama bare nayi typing dan Allah Ku sakata a addu'a. Ku ci gaba da hakuri da ni littafin Joy yanzu ya fara dadi, Ku dai Ku ci gaba da bibiya.
Yan group d'ina *Joy Novel Fans* ina Godiya da addu'o'inku ga Mamana Allah ya amsa, Allah ya sake muku da alkhairi ina matukar Alfahari da ku.
Kar a manta da comment and share pls🙏🙏🙏🙏🙏🙏
09116099486.
[12/29, 2:45 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀
~FARHAT~
*PAGE 31*
No editing🙏
Ko da Ummi ta shiga gida da Al'ameen ta fara cin karo a tsakar gidan yana wanki, a kid'ime ta fara labarta masa rashin lafiyar Amira, ta k'are da, cewa; Wallahi Amintacce na tsorata da ganin yarinyar nan, hankalina ya tashi, da da k'arar kwana da sai dai na ji mutuwar ta." Ta kai karshen maganar tana matsar kwalla, sosai ya kid'ime da ganin hawaye na kwaranya a idanun ta. Ummi jaruma ce, abin da zai sakata zubar da hawaye haka lallai ya kai abin tausayi, rik'e hannunta ya yi ya kai ta falonta ya zaunar da ita, ya shiga bata baki a kan ta yi hakuri ta yi shiru cuta ba mutuwa ba ne, ta ce "Yayan Fatima dole na koka, kar kaso kaga Amira." Rarrashinta ya ci gaba da yi, har ya samu ta yi shiru, Fatima kam jikinta ne ya yi sanyi tun lokacin da ta ji Ummi na labartawa Yayanta halin da Amira ke ciki, hakan yasa ta lafe a kitchen ta kasa fitowa.
Ranar yini Ummi ta yi zirga-zirga tsakanin gidanta da gidan Maman Amira, babu irin tambayar da Ummi bata mata ba a kan damuwarta amma kamar yadda ta saba ta k'i fad'a, da Ummi ta dame ta da tambaya, sai kawai ta fad'a jikinta ta rungumeta ta fashe da kuka, hakan ya k'ara sanyayar ma Ummi da gwiwa kwarai. Fatima ma ta shiga ta duba ta, sai da ta yi kwalla itama.
Kamar yadda Al'ameen ya yi alkawarin ranar Monday zai kai Fatima makaranta hakan ko aka yi, ranar ita da aminiyarta sun yi farin ciki kamar babu gobe, dan kar Mom ta sani yasa Joy ta laftawa David kud'i, ai kam ji kake tsit! Mallam ya ci shirya.
A bangaren ciwon Al'ameen, babu abin da ya canza, sai ma sake ta6ar6arewa da lamarin ya yi, kusan kullum a cikin damuwa ya ke, sai dai koda wasa bai bari Ummi da Fatima sun fahimta ba , don baya son abin da zai d'aga musu hankali, haka ya ci gaba da shan overdose d'in maganin shi, don a halin yanzu ba shi da wata mafitar data fi wannan, abin da ya fi d'aga hankalinsa a yanzu bai wuce yadda, ciwon ke yawan tayar mishi a kowani irin lokaci ba, babu dare babu rana babu safiya, hakan na nufin ya kai stage 5 kenan a jikinsa, hakan yasa ko ina zai ce maganinsa na tare da shi saboda tsaro.
Sau biyu Ummi na kama shi yana kokarin shan maganin, hakan ya firgita shi, sai dai ya yi mamakin yadda bata tambaye shi na menene ba, itakam har ga Allah bata kawo komai a ranta ba don ta yadda da tarbiyar da ta yi ma shi d'ari bisa d'ari.
Ana cikin wannan halin Aliyu ya dawo,
A ranar ya kira Al'ameen ya sanar mi shi da shigowar shi Niger, kuma a ranar yana ajiye jaka a gidan ya yi wanka ya yi wa gidan su Al'ameen tsinke, don lamarin shi ya tsaya ma shi a rai a kulli yaumin da tunanin shi yake kwana yake tashi.
Da yammaci ne misalin karfe biyar da rabi, Aliyu ya iso unguwar Abayi, bai tsaya an yi mai iso ba, ya yi sallama ya shiga don yana son gaisawa da Ummi, babu kowa a tsakar gidan Fatima na islamiyya, Ummi na d'aki.
Sake rafka sallama ya yi, daga cikin daki Ummi ta amsa mashi, tare da mikewa ta fito tana cewa; Muryar wa nake ji haka kamar Ali gadanga." Ta karashe maganar tana rike ha6a lokacin data yi arba da shi, risinawa ya yi yana murmushi ya yi ya ce "E Ummi ni ne, Ina wuni." Cike da fara'a ta ce "ina gajiya Aliyu muatanen kano saukar yaushe?." Ba tare da ya mike ba ya amsa da "D'azu Ummi." Ta ce "Masha Allah shine barka zauna ka huta ba ka kamo hanya, to ya ka bari yan cen, fatan an iske mutanen gida lafiya." "Lafiya kalau Ummi duk suna gaishe ki." "To madallah! Ina amsawa, ina yawan samun sak’on gaisuwarka wajen Yayan Fatima, har ya ce zai had’a mu a waya Allah ba nufa ba." Ya ce “Allah sarki! Haka ne dama komai sai Allah ya so” "mik’e Aliyu ga kujera ka zauna, d’aki zafi sun dauke wutar su." Ta karashe maganar tana nuna mashi kujera y’ar tsuguno. Zama ya yi, itama ta d’auko tabarma ta shimfid’a ta zauna tana cewa; ga shi Fatima bata dawo makaranta ba da tsoro maka ruwan sanyi amma nasan tana hanya.” murmushi ya yi ya ce " Ba komai Ummi yanzu ma masha ruwa kafin na shigo." Hira suka shiga yi da Ummi cikin sakin jiki da sabo, da alamar a kwai shakuwa a tsakanin tun ba yanzu na, kusan rabin hirar ta Amira ce, Ummi ke mashi, duk da baisan yarinyar ba ya tausaya mata sosai, ya yi mata addu'a da fatan samun sauk'i.
Fatima ce ta yi sallama ta shigo ganin Aliyu yasa ta sakin fara'a ta ce "Laaa! Yaya Aliyu Kaine a gidan namu yau." Murmushi ya saki a ransa yana mamakin girmanta ya ce " Ni ne Zahra, kin dawo ya makaranta?" "Alhmdllh Yaya ya su Umma da su Aziza, da sauran y’an uwa?" "Duk suna gida na baro su k'alau." "Madallah! A gaishe su." "Insha Allah zasu ji."
"Maza ki ajiye jaka ki amso mi shi ruwan sanyi." Cewar Ummi bayan sun gama gaisawa da Fatima, jakarta ajiye a d'aki, ta amshi kud’in ta je ta siyo pure water mai sanyi a shago ta kawo, ajiye ma shi ta yi, ta ce "Ummi bari na dubo Anty Amira." "Yawwa Binta maza je ki, ni ma naso shiga da dazu sai ga Aliyu, amma idan na yi isha kafin na kwanta zan dubota nima."
A zaure ta ci karo da Al'ameen, "Yayana oyoyoo." Ta fad'a tana amsar ledar hannunsa, godiya ya mata, tare su ka shigo cikin gidan, d'akin ummi ta kai ledar ta ajiye ta fice zuwa gidan su Amira.
Cike da d'okin ganin juna, suka yi musabaha, "Timekeeper kanawan dabo, gaskiya kano ta kar6e ka abokina, kaga yadda ka yi wani k'ato." Cewar Al'ameen cikin sigar zaulaya, dariya Aliyu ya yi ya ce "Na gode da zagi, kana ga duk na kanjame sai kashin wuya kamar kai, ka ce wani na yi kato." "Allah ba sharri na ka yi dan gwa6i, me ye sirrin." "Kai dai ka sani ni babu wani gwa6in da na yi, kowa cewa ya ke ba rame na yi katon kai." Haka suka yi ta zaulayar juna, Ummi na yi musu dariya daga bisani suka fito kafar gida suka zauna a dakalin gidan su Amira dake kallon nasu.
Jiki a sanyaye Aliyu ya dafa kafadar Al'ameen, juyowa ya yi suka kalli juna cikin ido, damuwa da tsantar so da kulawa Al'ameen ya hango kwance a kwayar idanun Aliyu, "Abokina mekefaruwa, ka rame Ustaz kamar ba kai ba ka taimake ni ka gaya mini halin da ka ke ciki." Ajiyar zuciya Al'ameen ya sauke, ya ce " Ina cikin matsanancin damuwa Aliyu! Damuwar da take neman ruguza mini rayuwa, ta hanani farin ciki da kaanciyar hankali dani da ahlina." Ya karashe maganar a sanyaye, agogon hannunshi ya kalla ganin lokacin sallah ya kusa ya ce , "maganar da yawa bari mu yi sallah tukun na." Kafin Aliyu ya amsa suka ji sallama a kansu, a tare suka mai sallamar jin muryar mace.