← Book details Joy Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 46

Sashe 11

Joy Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali sautin kukanta ya fara raguwa, daga bisani kuma ya dauke gaba ɗaya, sai shessheƙa da ajiyar zuciya, ganin ta ɗan samu nutsuwa, ya raba ta da jikinshi tare da kama hannunta suka bar ƙofar gidan ba tare da ya ƙara yi ma gidan kallo ɗaya ba.

A bangaren Fatima mari da hankadar da Mom ta mata bai daga mata hankali ba, kamar yadda kalamanta suka daga mata hankali, tana jin Joy a jikin jinin jikinta da bargonta, jinta take yi kamar wata bangaren na jikinta, kwatankwacin yadda take jin Yaya Ameen haka ta ke jin Joy a zuciyar ta, shin me yasa Mom take son raba su, ta karashe tunanin sabbin hawaye na silalowa daga idanuwanta.

A haka suke iso ƙofar gidan su ba tare da Al'ameen ya iya buɗe baki ya ce mata ƙala ba, domin ran shi a maruƙar ɓace ya ke idan ya ce zai yi magana a lokacin bazai faɗi alkhairi ba.

A zaure ya dakatar da ita, ya shiga ciki ba jimawa sai gashi da dayan hijabin haddanta a hannunta shi, buta ya dauko ya bata ta wanke fuskarta, sannan ya bata hijabin ta saka, ya sake jan hannunta, bai tsaya da ita ko ina ba sai haddarsu, hakuri ya baiwa malamin su akan lattin da ta yi, sannan ya juya ya tafi ba tare da ya kalli Inda take ba, sai lokacin shirun na shi ya fara daga mata hankali, ta san sarai shirun nan na yayanta ba alkhairi bane akwai abin a yake shiryawa, magantuwan shi yafi alkhairi sau da yawa fiye da shirun shi.

*********

A bangaren Joy dakyar Mom ta samu ta turata cikin gidan ta maida get ta rufe, zubewa ta yi a wajen ta fashe da wani irin kuka, cikin kukan take cewa "why Mom me yasa zaki yi mata haka, me yasa kika koreta Mom, me yasa kika daketa." Mom dake wani irin huci ta dago ta watsawa ma'aikan gidan da suka yi cirko -cirko suna kallonsu wani mugun kallo take duk suka dare kowa ya kama gaban shi, tsugunawa ta yi gaban Joy a tausashe ta riko hannayenta ta ce "Ki daina kuma daughter ban yi haka don na bata miki rai ba nayi ne dan kare martabarki data addininmu, na mata haka ne saboda ta rabu dake don ke ba sa'ar kawancenta bane," katseta ta yi da cewa "Amma ai na miki alkawarin ni da kaina zan rabu da ita, me yasa zaki wulakantata." Mom ta ce "To naji kiyi hakuri ki share hawayen ki, kinga baki da isasshen lafiya." Mikewa ta yi ba tare da ta kula Mom ba ta wuceta fuuu ta shige plat din su haurawa sama ta yi ta fada dakinta ta bugo kofa ta murza key. Nan ta silale bakin kofar ta ci gaba da rera kukanta ji take kamar ta yi tsunstuwa ta ganta a gaban Fatima, me zata ce mata da wani ido zata kalle ta, uwa uba Yayanta shin da wani baki zata fahimtar da su ce wa bata laifi.

Biyo bayanta Mom ta yi ta tura kofar dakin ta ji shi a rufe, knocking ta shi ga yi tana kiran sunanta, tana ji taki tankawa, babu irin magiyar da Mom bata mata ba, karshe dole ta kyale ta, gajiya ta yi da kukan ta mike ta shi ga toilet ta wanke fuska ta dawo kan bed dinta ta kwanta, wuraren karfe goman dare ta jiyo muryar Papa a bakin kofarta yana kiran sunanta, ta shi tayi ta bude tare da fadawa jikin sa ta fashe da sabon kuka, rarrashinata ya shiga yi, cikin sigar nasiha ya ce "Akan me zata damu kanta dan kawai wata Muslim kanwar ta tazo Mom dinta ta ce bata nan, ai wannan ba abin damuwa bane Mom tayi haka ne don ta kareta daga sharrin terrorism.

Daga yanayin kalaman shi ta fahimci bai san ainahin abin da ya faru ba, kawai karya da gaskiya da son rai Mom ta sanar mishi. Shi ya lallabta har ta dan sake ta samu ta ci abinci.

A haka weekend days suka tafi duk bata cikin walwala, duk da irin kokarin da Papa yayi na fitar da ita shopping da wuraren shakatawa a ranar Sunday ya kashe mata makudan kukade hakan bai rage ta da komai ba, Allah Allah ta dinga yi gayi ya waye ta je school ta hadu da Fatima ta bata hakuri, washegari kuwa 6am ya gama komai har ta da breakfast ranar bata jira su Mom ba, daki ta bisu ta yi musu sallama direbanta ya wuce da ita.

*********

Har akaci ranakun karshen mako aka sid'e Yaya Ameen bai ce komai game da abin da ya faru ba, Fatima ta yi ta zuba ido ko zai mata fada amma bai yi ba kuma bai canza mata a komai ba sannan bai gaya Ummi abin da ya faru ba, ganin haka yasa ta dan saki jiki, safiyar litinin cike da wani irin shauki da zakuwa ta gama shirin makaranta, duk da a ɓangare ɗaya zuciyarta cike take da fargaba amma hakan bai hata ta sauri ba, tsab ta shirya da wuri tana cikin sallama da Ummi dake zaune a tsakar gida Yayanta ya shigo, da fara'a ta kalleshi ta ce "Yaya barka da safiya." Duk da kuwa sun gaisa ɗazu bayan asuba, kallon ta yayi ya na jin wani irin a zuciyar shi game da hukuncin daya yanke ganin yadda take cike da farin ciki, dakewa yayi ya ce "Ya ce Fatima ki je ki cire uniform din jikinki daga yau na cireki daga challenge international school, zan canza miki wata makaranta." Wani irin zaro ido Fatima ta yi ta sauke a fuskar shi, hankaɗinta a tashe gabanta na wani irin dokawa, Ummi ma da sauri ta dago ka ta kalle shi, suka hada ido yayi saurin dauke kai, daga kallon da take mishi, kafin ta ce wani Abu yayi saurin cewa "ki yi hakuri Ummi hakan shine abin da zaifi mana kwanciyar hankali baki ɗaya." Ta san ɗanta yana da kaifin hankali da zurfin tunani bata jin zai aikata abin da ba dai dai ba, amma duk da haka zata so sanin dalilin shi, kallon Fatima da tuni hawaye sun game wanke mata fuska tayi ta ce "Binta bamu guri, koma ɗaki ki cire uniform ɗin kamar yadda ya fada." Da gudu ta wuce tana fashewa da kukan da tun ɗazu take kokawar rikewa, da kallo duk suka rakata har ta kule.

Dawo da kallon ta kan shi ta yi, tare da yin gyaran murya, zama yayi a gefenta a tausahe ya ce "Ummi kiyi hakuri da hukuncin dana yanke ba tare da neman shawarar ki ba." Dakatar da shi yayi da cewa "Ba wannan nake son ji ba shin menene dalilinka na canja mata makaranta, duk da nasan makarantar kuɗi ne ya fi ƙarfin mu amma ai ba mu muke biya mata ba." Ya ce "Ummi dalili na mai karfi ne kuma shine kwanciyar hankalin ta da nawa da kema baki gaba daya." Tsare shi tayi da ido ganin yana son mata kwana kwana ta ce a dake cikin yananyi na rashin wasa "Dalilin naka na ke son ji ko bankai matsayin da zan sani ba ne?" "Ki yi hakuri Ummi." Ya fada ganin kamar ta dau zafi, kafin ya kwashe komai akan abin da ya faru ranar ya sanar mata, ya daura da cewa "Ummi tarayyar mu da su ta ko,ina bai kyautu ba, na yanke shawaran canzawa Fatima makaranta saboda rage karfin alakar dake tsakanin su, na san idan ba ta hakan ba babu ta yadda zamu Iya rabasu." Shiru Ummi ta yi labarin ya girgiza ta kuma ya bakanta mata, sai dai ita abin da ta dade da hangen a alakar Fatima da Joy ba kowa ne zai iya hango shi ba, ajiyar zuciya ta sauke ta ce "Amintacce wannan lamari baiyi dadi ba, sai dai har kullum ina kara sanar maka tsakanin yaran nan akwai wani boyayyen sirri wanda ni kaina bansan shi ba, mu bi komai a sannu don ina ji a jikina wata rana wannan alakar tasu zata fitar dani daga kangin rayuwar kadaicin da nake ciki na tsawon shekara da shekaru, duk da mafarki ba gaskiya bane, ba abin yadda bane ni naga hakan a cikin mafarkina yafi sai shurin masaki, Allah ya sani da fari nafi mahaifiyar Joy kiyayar tarayyarsu, kuma kai shaida ne babu ta yadda banyi don na raba su ba, sai dai daga baya na fahimci cewa tsakanin su hadin Allah ne, bazan hanaka canzawa kanwarka makaranta ba idan kaga hakan yafi maka kwanciyar hankali shi kenan."
A ajiyar zuciya ya sauke dama fatan shi Allah yasa kar Ummi ta ki amincewa da hukuncin shi.

Zamu dinga tsallaken rana daya idan nayi posting yau bazan yi gobe na sai jibi insha Allah.

Ga me bukatar shiga group ya tuntubeni ta wannan lambar.
09116099486
[12/29, 2:33 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY*🌀🌀

*PAGE 10*

Miƙewa yayi daga gaban Ummi ba tare ya sake cewa komai ba ya bi bayan Fatima, bata falo dama baiyi tsammanin ganinta a nan ba, bed room ya nufa kai tsaye , a kwance ya same ta kan gado tana ta risgan kuka , jin motsin shigowar mutum yasa tayi sauri ta juya baya ta fuskanci bango, yadda mai shigowan bazai iya ganin fuskarta ba ta yi tsit! kamar mai bacci. Daga bakin ƙofar ɗakin ya tsaya ya rungume hannayen shi a ƙirji yana ƙare mata kallo yana jin wani rauni na son ziyartar zuciyar shi, dakewa yayi ya ce "Fatima kuka kike yi???" Da sauri ta girgiza kai, wasu sabbin hawaye na sake wanke mata fuska. Ajiyar zuciya ya sauke ya cigaba da cewa "Kiyi haƙuri Fatima idan hukunci na yayi tsauri da yawa a gareki, amma ki sani bazan iya jurar ganin ana wulakanta ki ba, ya zama dole ki yanke alaƙa tsakanin ki da yarinyar nan tunda iyayen ta itama basa so, bamu da ƙarfin ja da su ta kowanne fanni, shiyasa na yanke hukuncin canja miki makaranta, duk da nasan zakiji babu daɗi, kiyi haƙuri ni mai kare martabarki ne a koda yaushe." yana gama faɗin haka ya juya ya fice don bazai iya jurar ci gaba da ganin kukanta ba.
Chapter 11 · 0% Book details