Sashe 33
Joy Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yana daga kishingide cikin damuwa, ya yi nisa cikin duniyar tunani, suka yi sallama sanye yake da singlet da short kasancewar a kwai zafi a garin ga babu wutar nefa, ga dai hadari d'ankare a sararin samniya, amma kuma rana ake kwallarawa kasancewar daminar na gaf da wucewa, ganin su yasa ya yi sauri ya ja bargon dake kan katifarsa ya rufe daga kwankwasosa zuwa k'asa, ya ta shi ya zauna da kyau fuskarsa babu walwala saboda yanayin damuwar da ya kwana ciki. Bakin katifarsa Fatima ta laluba ta zauna, Joy kuma ta zauna daga gefenta a k'asa, kallo d'aya ta mishi ta d'auke kai ganin shi sanye da singlet gaba d'aya surar mazantakarsa a bayyane ga wani kwantaccen bakin bashi luf a kirjinsa, duk sai ta ji wani iri a jikinta, hakan yasa har suka gama gaisawa bata iya d'ago kai ta sake yi masa kallo na biyu ba, sai da ta tsinci muryar Fatima na cewa; Yayana dama Joy ce ta ce na rakota tana son yin magana da kai. A zabure ta dago jin kullin sharin da Fatima ta mata, dai-dai lokacin ya mai da kaifaffun idanunsa kanta, carat idanuwansu ya sark'e da na juna, da wani irin sauri ta kawar da kai don ji ta yi gabanta ya yi wani irin fad'uwa, zuciyar ta kamar zata faso kirji ta fito, Fatima ta zungura da itama tsabar kwarjinin shi yasa ta kasa fadar bukatarsu kai tsaye. Dagowa Fatima ta yi ta kalleta, Suna hada ido ta watsa mata harara tare da yi mata kallon ya zaki mini haka, alamar ki fad'a ma shi, Fatima ta mata da ido, ta sake watsa mata harara tare da make kafad'a ta mata alamar ke ki fad'a.
Duk abin da suke yana kallonsu, ganin suna neman 6ata masa lokaci yasa ya yi gyaran muryar duk d'ogowa suka yi suna kallon shi, idanunsa a kan Joy ya ce "Uhummm! FARHAT ina jin ki." Cikin inda-inda ta ce "Daa da dama! Mun zo ne, mu rok'e ka a kan ka yi hakuri kabar Fatima ta ci gaba da zuwa school, kar ka canja mata wani' ko Fatima ai haka ne ko?" Ta fada tana kallon Fatima da sauri Fatima ta girgiza kai ta ce "E, e, Yaya haka ne don Allah ka yi hakuri ka bar ni na ci gaba da zuwa can d'in."
Duk da yanayin damuwar da yake ciki sai da suka so ba shi dariya; ji yadda suke abu kamar uban wani ya turosu, ba su suka gama tsara abinsu ba, ji adanun Fatima kamar wacce ta yi wa sarki k'arya, ita kuma kawar cin mushenta ji nata kwala-kwala kwalan idanun kamar fitulun mota.
A zuciyarsa yake musu wannan tsiyar, dakewa ya yi ya ce, to shikenan na ji kuje sai na yi shawara, har suna had'a baki wurin cewa "To Yaya mun gode."
Suna fitowa "ta zubawa Fatima dundu ta ce " Haka muka yi dake Teetee." Dariya Fatima ta saka ta ce, "To ni kasa fad'a na yi yasin kwarjini ya min." "To kema kenan ina ga ni, amma sai naga kamar bai dauki maganar mu da mahimmanci ba." Fatima ta ce "Wallahi kuwa, tunda kika ji ya ce haka, amma nasan abin da zamu yi da Ummi zamu hada shi nasan idan ta saka baki idan da yuwuwar ya bar ni zai bar ni."
Da kyar Ummi ta amince musu zata mishi magana, sai da suka yi ta magiya da bambaki! A ranar kuwa daya dawo da dare ta tuntu6e shi da zance, kallon Fatima ya yi da ta yi saurin yin k'asa da kai ya jefe mata kallon tuhuma, Ummi ta ce "Amintacce kai na ke sauraro, idan da yuwuwar hakan don Allah ka barta ta koma can d'in su k'arata tunda sun kusa kammalawa." Jim ya d'an yi kafin ya ce "To Ummi shikenan, ta shirya zuwa Monday sai na rakata da kai na Allah yawa hakan shi ya fi alkhairi ya kad'e fitina." Ummi ta amsa da "Amin ya Allah." Fatima kam washe baki ta yi tana dariyar farin ciki, Al'ameen ya jefa mata hararar wasa, sake kyalkyalewa ta yi da dariya tare da cewa; Thank u Yayana Allah ya faranta maka kai ma." A tare suka amsa da Amin shi da Ummi.
Ummi ta ce "Wai ni kam Yaran nan ko kun ji mini motsin Amiratuwana, yau idan ban yi karya ba kusan kwanan ta goma rabonta da gidan nan, Allah yasa dai lafiya."
Fatima ce ta dago da sauri tare da cewa "Yawwa Ummi tun ranar Asabar a hadda Aysha ta ce min bata da lafiya wallahi na manta na gaya miki kwata kwata na sha'afa."
Tafa hannanye Ummi ta shiga yi tare da sakin salati. "Haba Fatima, yanzu tun ranar Asabar aka gaya miki amira babu lafiya amma ki ce wai kin manta, Haba haba Fatima amana bai ce haka ba, Amira ai ta wuce haka a gareki, don komin lalacewar giwa ta fi karfin kwandon goro, wato yanzu kin samu Joy shikenan kin rabu da kowa ko? Gaskiya banji dadi ba baki Kyauta min ba, ai hausawa sun ce ka gaida mai gaisheka ko ba zai amsa ba." Haka Ummi ta yi ta mita tare da yi wa Fatima fad'a, can kuma ta ce "Amintacce duba min karfe nawa idan dare bai yi nisa ba yanzu zan shiga na dubo ta yarinyar kirki, ai ko iyayenta ma sai su zageni ba don Allah yasa mutanen arziki ba ne."
Shikam Al'ameen shaf ya manta da batun wata Amira, zai iya cewa tun daga ranar da wannan maganar ya shiga tsakanin su bai kuma saka ta a ido ba, agogon ya duba kamar yadda Ummi ta umarta jin tana ta sake tambayar shi karfe nawa ya ce "Ummi goma da rabi ta gota nasan yanzu sun kulle kofar gida ki bari da safe."
Badan ta so ba dole ta hakura, amma fa ranar Fatima taga fushin Ummi, itama duk ta yi laushi jikinta ya yi sanyi tabbas bata Kyauta ba, gaba daya cikin yan kwanakin nan Joy ta d'auke mata hankali ita ce kadai a rai da zuciyarta.
************
*AMIRA*
Tun daga ranar da Al'ameen ya nuna baya da ra'ayinta ta shiga matsanancin damuwa, a ranar ta yi kuka kamar baza ta daina ba, har sai da ta kwanta zazza6i na kwana uku, tun da ta tashi daga wannan zazza6in gaba d'aya ta canza, a hankali aka fara rasa gane kanta, bata da aiki sai kuka sai tunani, kurmar karfi da yaji ta naimi komawa, don tana iya wayar gari ta wuni ta kwana ba tare da ta cewa kowa uffan ba, lamarin da ya fara d'aga hankalin ahlinta, wa'ec d'in da suka fara bada ita aka kark'are ba, sosai Maman Amira ta shiga damuwa duk a tunaninta iskokai ne suka shigeta, hakan yasa kullum cikin tofa mata addu'o'i take da amso mata taimako a wurin malamai, amma a banza lamarin sai dad'a gaba ya ke yi, wani irin rama da mugun haske ta yi cikin abin da bai fi wata guda ba, kusan sau uku suna zuwa asibiti ganin likita maganar daya ce kullum; damuwa ce ke damunta." tambayar duniyar nan ta k'i fad'awa kowa damuwar, sai dai ta ce ita babu wani damuwar da ke damunta, har kuka mahaifiyarta ta yi mata ta yi magiyar ta yi nasihar ta yi fad'an akan ta gaya mata matsalarta amma a banza, hakan yasa Maman ta k'ara gaskata zarginta na cewa; Iskokai ne suka shigeta.
Da farar safiya Ummi ta yi wa gidan su Amira dirar mikiya, lokacin ko Al'ameen bai dawo daga masallaci ba, wasu masallatan ma ba'a idar da sallah ba, itama tana sallame nata ko tasbihi bata yi ba ta tashi, don jiya dakyar ta yi barci saboda damuwa da tunanin halin da Amiranta ke ciki, yarinyar kirki, babban abin da ya k'ara d'aga mata hankali bai wu ce mummunar mafarkin da ta yi a kan ciwon Amiran ba, kwarai ta tsorata da lamarin, don ita kanta tana tsoron mafarke mafarken da take yawan yi a cikin yan kwanakin nan.
Tsakar gidan babu kowa, duk su na d'aki, a k'ofar d'akin Maman Amira ta yi sallama, Aysha ce ta fito tana amsawa, ganin Ummi yasa ta yi saurin risinawa ta gaisheta, ummi ta ce "Ina gajiya Aysha ya mai jiki." "Alhmdllh Ummi tana samun sauk'i."
Kafin Ummi ta ce wani abu Maman amira ta fito daga d'akin sanye da hijabi hannunta r'ike da carbi, murmushi ta sakar wa Ummi tare da cewa "Maraba da Ummi ke ce da farar safiyar nan, ina kwananmu ya kwanan iyalai." Ummi ta ce "Ni ce Maman Amira, ya mai jiki, wallahi ban ji sai jiya da dare, da nake cewa yara nikam kwana biyu banga Amira ba, shine Fatima ke ce min wai bata da lafiya, wallahi hankalina ya ta shi, ba dadon dare ya yi ba da a daren zan shigo na duba ta, a addafe na yi barci jiya wallahi." Ta karashe maganar cike da alhini da tausayawa. Maman Amira ta yi murmushin karfin hali ta ce "Allah sarki Ummi Kiyi hakuri wallahi nima harda laifi na da ban aika miki ba lamarin ne da rikitarwa." Ta fad'a damuwa bayyana k'arara a fuskarta ta, hakan ya k'ara daga hankalin Ummi, "Ki shigo daga ciki gata nan." Maman Amira ta fad'a tana juyawa cikin d'akin da sauri tare da d'auke dan guntun hawayen da ya zubo mata ba tare da ta bari Ummi ta gani ba.
Salati da sallallami Ummi ta saka a lokacin da ta yi arba da Amira kwance a kan gadon Mama tana barci, wanda sai gabanin asubahin nan ya dauketa cewar Mama "Na shiga uku ni Balkisu! Mai zan gani haka." Sai kuma ta fashe da kuka tana maimaita kalmar "Innalillahi wa'inna ilaihi rajiun, allahumma ajirni fi musabati wa aklifni khairan minha!" Ganin tana neman fad'uwa yasa Mama saurin rikota tare da zaunar da ita a bakin gadon.