← Book details Joy Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 46

Sashe 1

Joy Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

[12/29, 2:19 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀

*BY*

*AYSHA NALADO*

*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATIO*

*LITTAFI NA ƊAYA*

*PAGE 1*

Bismillahir-Rahmanir-Rahim

NIGER STATE

*Abayi close* fitacce ne kuma sananiyar unguwa a cikin garin na *Minna*, unguwace dake dauke da nau'ikan mutane kala kala
ƙabilu dabam dabam
musulmai,cristain, talakawa, masu matskaicin ƙarfi,da ma manya masu hannu da shuni, hakan yasa unguwar ke cakuɗe da gidaje maya da ƙanana.

Misalin karfe biyu na sulisin dare, ruwa ake tsugawa kamar da bakin kwarya, ko ina ya dau sanyi bakajin
ƙarar komai sai na yadda ruwa ke sauka a saman kwanukan gidajen mutane da mugun karfi haɗi da walkiya tare da razananiyar tsawa mai firgita mai sauraro tare da wani iska mai ƙarfi dake kadawa jefi jefi, hakan yasa gaba ɗaya garin ya ɗauki wani irin sanyi mai ratsa jiki.

A ɗaya daga cikin gidajen talakawan dake unguwar, kwance *AL AMEEN* yake cikin ɗan madaidaicin ɗakin shi dake zauren gidansu a kan yar madaidaiciyar katifar shi, kuɗundune yake cikin bargo idanun shi a lumshe, a kallo ɗaya zaka dauka barci yake, sai dai ko kaɗan ba haka bane, yadda yake sauke numfashi a wahale da yadda zufa ke karyo masa duk da matsanancin sanyi da iskar dake kaɗawa a garin ne zai tabbatar maka ba lafiya yake ba.

Cike da tsananin azabar ciwo ya buɗe rinannun idanun shi ya sauke akan wani jaka dake rataye jikin hangar dake manne a bangon ɗakin, so yake ya miƙe ya isa ga jakar domin ya dauki magungunan shi da ya musu kyakyawar buya a cikin jakar , sai dai inaa! Bazai iya ba domin Ko kwakwaran motsi baya Iya yi balle har akai ga batun miƙewa tsaye, idan kuwa yace zaiyi wani motsi mai karfi a halin da yake ciki, komai zai Iya faruwa da shi ciki harda rasa numfashin shi. Ci gaba yayi da kallon jakar, ji yake da yana da dama da ya kira jakar daga kwancen da yake, sai dai shi kanshi yasan hakan ba abune mai yuwuwa ba,

A hankali ya mayar da idanun shi ya lumshe, cike da tsananin azabar ciwon maran da ke neman hallaka shi, ya riga ya sani a duk sanda za'a wayi gari cikin irin wannan weather ko makamancin sa, to kuwa shi a ranar bashi da sauran lafiya, yau kimanin shekara hudu kenan yana fama da wannan lalurar, tun daga lokacin da yakai munzilin balaga, lokacin yana da shekaru sha takwas a duniya ya fara fuskantar wannan matsalar, tafi tafi abu ya fara ƙamari wanda har sai da ya danganta kanshi da likitaba tare da sanin kowa ba, shi ƙadai yake gwagwarmaya da faɗi tashin shi ba tare da kowa ya sani ba, ciki harda mahaifiyar shi wacce duk duniya bashi da kamar ta.

Cikin karfi hali irin nashi na jarumin namiji ya shiga, ambaton Allah a zuciyar shi domin ya kawo mishi
ɗaukin gaggawa, yayin da ya kai duka hannayenshi biyu ya dafe marar shi dake mishi wani irin matsanancin ciwo tare da daurewa kamar jijiyoyin gurin zasu tsinke.

Kimanin awa ɗaya da rabi ya dauka ba tare da bakin shi ya gaza da ambaton ALLAH ba, a hankali cikin hukucin ubangiji ya ji komai na lafa mishi.

A hankali ya miƙe hannunshi ɗaya dafe da marar shi, yana tangaɗi ya isa gaban jakan da maganin shi ke ciki, hannu ya saka can kasar jakar tare da dauko sacet din magani, guda data ya ɓalla ya maida sacet din, komawa yayi bakin katifar shi ya zauna tare da jawo jug din dake gefe cike da ruwa babu bata lokaci ya afa maganin ya kora da ruwa, ajiyar zuciya ya sauke tare da komawa ya kwanta rigingine yana sauke numfashi.

*Washe gari*

**********

6 Am dai dai Alarm ɗin agogon dake ajiye akan bed side drowan dake kusa da gadonta ya fara ƙara yana girgiza, a hankali ta buɗe kyawawan idanunta tare da miƙa hannu ta kashe alarm ɗin, kusan minti biyar ta kwashe a kwance kafin ta yaye bargon da ke lullube a jikinta ta miƙe zaune tana tattare dogon gashin kanta daya barbaje ta ɗaure shi a baya, yunkurawa tayi ta miƙe akan kafafunta, mika tayi tare da dogon hamma baki bude tana furta "in Jesus name" cikin zazzakar muryarta, kayan bacci ne riga da wando masu kauri a jikinta saboda yanayin da ake ciki yau na sanyi a garin, cike da kasala ta fara takawa a hankali Kamar wacce bata da laka a jiki ta nufi wani ɗan ƙofa ta buɗe ta shige.

Kusan minti 30 ta kwashe, sannan ta fito daure da dan ficilin tawel iyakarsa cinyoyinta, jikinta da gashin kanta na ɗigan ruwa, gaban mirron dake shake da kayan shafa na mata da turaruka ta tsaya, hand dryer ta kunna ta fara busar da gashin kanta bayan ta gaba ta shafe shi da mayukan gyaran gashin kusan kala uku masu kyau da tsada take ya dau kwalli da sheki, taje shi tayi kafin ta tattare shi tayi parking din shi a gefen kai.

Body lotion dinta mai kamshi da tsada ta shafa, tare da turarukan ta na jiki, fuskarta ta gyara batayi wani dogon kwalliya ba hoda kawai ta shafa da lip gloss sai maskara data karama Zara zaran lashes dinta.

Gaban makeken wadrob mai kofa shida dake dakin ta tsaya Wanda set ne da gadon da mirron dake dakin, kofan farko ta bude, inner wears ne shake a wurin kalakala kamar za'a bude kantin sayar da su, pant da vest da sock ta dauka ta maida kofar ta rufe, kofar dake kusa da na farko ta bude, school uniform dinta ne a goge a ninke kusan kala goma, ɗaya ta Zara tare da madai kofar ta rufe cikin Sauri ta shirya cikin farin riga mai dogon hannu tare da skirt sky blue damamme iyakarsa cinyanta, tayi stokin,farin sock ta Sanya dogo ta dauki wani farin both a cikin jerin takalmanta dake cikin abin jera takalma sunfi a kirga ta saka a kafarta, agogon ta dauka a cikin wani dirowa ta daura a hannuta, daga haka bata kara komai ba ta sunkuci gabjejen school bag dinta ta fice daga dakin.

Sauri sauri take saukowa daga kan stairs ta iso wawakeken falon dake kasa, a share yake tsab sai tashin kamshi yake babu abin da ke tashi sai sautin TV dake kunne a tsahar eagle TV wani babban pastor na wa'azi cikin karadi da tsoratarwa, da alama ma,aikatan gidan masu alhakin kula da tsabtar falon har sunyi aikin su, bata bi takan TV ba ta ajiye jakanta akan daya daga cikin kujerun dake kewaye da falo ta fice.

Hanyar dining Wanda ke kusa da makeken kitchen din gidan Wanda shine general kitchen na gidan a nan ake duk wani girki ta nufa, abin mamaki a shirye tsab ta tarad da dining din shake da warmers kala kala ga flask da kayan tea da sauran su.

Bata bata lokaci ba gurin Jan daya daga cikin kujerun dining din ta zauna tana mai duba agogon dake daure a tsintsiyar hannunta, motsin da taji daga stairs ne yasa tayi saurin daga kanta ta kalli hanyar gurin, kamar yadda tayi tsammani iyayen nata ne biyu mom and papa ke saukowa cikin shirin su ta tafiya aiki hannayen su sarke cikin na juna , mom sanye cikin dogon rigar less kanta babu dankwali, gashin dokin data kara a kanta a bayyane, papa kuma sanye cikin suit ash da kagansu kaga tsofafi masoya ya boko.

A tare suka sakar mata murmushi, itama babu bata lokaci kyakyawar fuskarta ta yalwatu da farin cikkin ganin iyayen nata.

Mikewa tayi tun kafin su ƙaraso tanufe su , jikin papa ta fara faɗawa ta bashi kyakkywan runguma tana cewa "gud morning my papa" shima zagayeta yayi da hannayen shi yana ɗan bubuga bayanta yake cewa "morning dear how ar U how was ur n9t." Ta amsa mai da "fyn papa." Sannan ta sake shi ta dawo jikin mom dake kallon su tana ta sakin murmushi, itama gaisawar sukayi kamar yadda sukayi da papa, kafin duk suka dunguma suka karasa kan dining.

Suna zama kuku ya futo daga kitchen da alamar dama tsaye yake yana jiran fitowar su, cike da girmamawa ya gaishesu, kafin ya shiga serving dinsu, abinci ne lafiyayyu akayi shi kusan kala bakwai kai da gani kasan a kwai almubazzaranci a lamarin.

Kusan duk a tare suka miƙe ba tare da sun ci abin kirki ba, Jakarta ta dauko a falo bayan ta shiga kitchen ta cikashi da chocolate da sauran kayan kwalama nau,i nau,i suka dunguma zuwa compound din gidan, ma,aikatan gidan ne suka Shiga kwasar gaisuwa, da sauri drivan dake kaita school ya fito da mota, duk da school din nasu ba wani nisa gare shi ba cikin anguwa ne amma kullum a mota ake kaita a dawo da ita tsabar gata.

Mom ce ta kalli driven cikin harshen nasara ta ce "Peter ka barshi kawai yau ni zan yi dropping dinta tunda ina da aikin safe, kai kuma in sun tashi sai kaje ka dauko ta." A ladabce ya amsa da "yes maa." Sallama suka kara yi da papa ya sunbace ta a kumatu bayan ya sake hugging dinta a hankali yake gaya mata ta kula mishi da kanta cikin shagwaba take amsawa a sangarce.

Daga cikin gidan zuwa school din kwata kwata tafiyar 15 minute sukayi har cikin school mom taso shigar da ita amma ta nuna bata so saboda gudun bacin ranta yasa mom ajiyeta a get, suna daga ma juna hannu har motar mom ya bace ma ganinta.
Chapter 1 · 0% Book details