← Book details Joy Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 46

Sashe 31

Joy Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ba su sha wahalar fita ba, don kafin ma su iso Mom ta sanar wa security din ta. Suna dan yin nisa da gidan David ya kalle ta ya ce " To Miss yanzu sai ina." Ta ce "Gidan su Fatima Hussain." "Fatima Hussain!" Ya maimaita sunan cike da dimbin mamaki, juyowa ta yi ta kalle shi cikin ido ta ce "Yes ko kana da magana." Yadda ta tsare shi da manyan idanunta masu kwarjini yasa ya yi saurin d'age kafad'a tare da cewa "Nop! Zan je wani waje na dawo mu had'u a nan." Ta ce "OK ya yi." Gaba ya yi ya barta a tsaye har sai da taga k'ulewarsa.

Ajiyar zuciya ta sauke, a hankali kamar wacce kwai ya fashewa a ciki ta kama tafiya.

Cike da karsashi da shauk'in so dake d'ibarta ta dauki hanyar gidan, zuciyar ta na k'ara karfafa mata gwiwa.

Sai dai ko da ta iso k'ofar gidan sai ta kasa shiga, tsayawa ta yi tana rarraba ido, sai lokacin wani tsoro da fargaba ya shigeta, ji take kamar ta juya ta runtuma da gudu, amma wani bangare na zuciyar ta na ingizata, kar fa ta shiga ya yi mata wani abin, cewar wani side na zuciyar ta, don warning din shi na ran nan har yau yana nan rad'am a kwakwalwarta.

Ta fi karfin mintuna ashirin a haka tana karantar wasikar jaki, ita bata shiga ba ita bata wuce ba, kamar daga sama ta ga an bud'e k'ofar gidan, a daburce ta d'ago manyan idanunta da suke cike da tsoro ta kalli k'ofar don ganin mai fitowa.

Al'ameen ne, ya lalla6a ya fito don ya sha iska , yana bude k'ofa ya ci karo da ita, rasa wani yanayi zuciyarsa ta shiga a lokacin da idanunsa suna sauka akan kyakkyawar fuskanta ya yi, farin ciki ne ko kuwa kewa ne oho, sai dai ko da wasa bai bari fuskarsa ta nuna ba, sai ma k'ara tamke ta da ya yi babu fara'a ko kadan, sannan ya zuba mata kaifaffun idanun shi.

Numfashinta ne ya dauke na wucin gadi, lokacin da idanuwanta ya sark'e cikin na shi, baki ta ke son ta bud'e ta yi magana amma kamar wacce aka sakawa padlock.

Sosai ya hango tsoratar da ta yi a cikin kwayar idanunta, yadda take rarraba idanu tana muymuy!! Da d'an bakinta ba bakaramin kyau ta yi mashi ba, tana d'aya daga cikin mutanen da ko wani irin yanayi suka shiga kyau ya ke musu.

Jin ta yi shiru bata ce komai ba yasa ya ce "You again? Ba nace miki kar na sake ganin k'afar ki a gidan nan ba, babu ke babu Fatima, ok baki jin magana ko?." Da sauri ta girgiza kai a raunace ya ce "Ba wajen Fatima nazo ba, wajen ka nazo." Had'e hannayenta ta yi take har ruwan hayawe sun cika mata idanu, ta ce "Na zo ne na sake baka hakuri akan abin da ya faru ran nan, ka yafe min for God sake, it all my fault." Ta k'arashe maganar tana kallon d'aurarren k'afar shi.

Wani irin rauni gami da tsantar tausayinta ne suka shiga ratsa zuciyarsa, shiru ya yi yana kallonta, yana jin wani irin yanayi a zuciyarsa game da ita, kwatankwacin yadda yake ji a zuciyarsa game da tilon kanwarsa.

Ganin bai amsata ba bai kuma daina binta da wani irin kallo mai kama da harara ba, yasa ruwan hawayen da take ta kokarin rike wa wanke mata fuska, ta san dama bazai kalleta da idon rahama ba, cikin muryar kuka ta ce "Nasan ni mai tarin laifuka ne a gare ka Yaya Alamein, zai yi wuya ka iya yafe min at once." Ta karsahe maganar cikin kuka da shessheka.

Rintse idanu ya yi da karfi. Da tasan yadda kukanta ke tsisstinka jijiyoyin zuciyarsa da ko da wasa bata yi ba.

Ita kam bata san abin da ke faruwa ba ganin yadda ya rintse idanu, yasa ta k'ara sautin kukanta wanda kukan da biyu ne, harda na yadda soyayya ke nukurkusarta.

"Stop!!!" Ya fad'a a tsawace jin tana shirin tarwatsa masa kwakwalwa.
Ta sauri ta had'iye kukanta, tana zare idanu, still hawaye bai bar zubo mata ba, kasa ya yi da murya ya ce "Is ok, na hakura ki dai na kuka, kinji." Yadda ya yi maganar a sanyaye cikin shigar rarrashi yasa ta yin shiru ta na kallon shi.

Hannu ya saka aaljihunsa ya dauko farin handkerchief ya mik'a mata ya ce "Oya wipe ur tears."

Wannan karon kasa ignoring ta yi duk da wannan time babu sassanyar murmushi nan a fuskarshi kamar wancen karon, sai ma sa6anin hakan.

A hankali ta miƙa hannunta dake d'an karkarwa ta kar6a, sai kuma ta kasa goge hawayen ta rik'e hankin a hannun tana kallon shi, gyada mata kai ya yi ya ce "uhumm!. a hankali cike da shauki ta kai handkerchief d'in fuskarta, wani irin sassanyar kamshine ya ziyarci hancinta, a ta ke ta lumshe idanu tare da k'amk'ame handkerchief d'in gam ta na shakar shi.
Duk abinda ta ke yi idanunsa na nan k'em akanta.

Minti biyu ta kwashe a haka, kafin ta bud'e idanunta tare da sauke handkerchief d'in a fuskarta ta mik'a ma shi, had'i da cewa"Thank u." Bai san sanda sassanyar murmushi ya ku6uce masa ba, mi'ka hannu ya yi kar6a hankin ya mayar aljihu tare da "gud gal! Don't cry again kin ji" A sanyaye ta gyada kai tare da cewa
"Ni zan wuce ina rok'on ka ka mika min gaisuwa wajen Fatima ka gaya mata ina kaunarta kuma ina tsananin kewarta." Tana fad'in haka ta juya ta kama tafiya.

Gaba d'aya lakkan jikinsa sun mutu, so yake ya bud'e baki ya dakatar da ita ta hanyar kiran sunanta amma kamar last time ya kasa kiran sunan, sai a zuciya yake ta maimaita Kalmar JOY.

FARHAT ya fad'a akan la66ansa, tabbas d meaning of d word Joy in Arabic is FARHAT.

Sai ya tsinci bakinsa da furta FARHAT da 'karfi, cak ta tsaya duk ta san ba ita yake 'kira ba, amma haka kawai ta ji k'iran ya ratsa har cikin kwakwalwarta.

Ganin ta tsaya yasa ga sake furta FARHAT, a karo na biyu, dis time juyowa ta yi, don jikinta ya gama bata da ita yake, daga Inda take tsaye ta nuna kirjinta da hannu ta mashi alamar ita yake kira, kai ya gyada mata tare da cewa "Yes u FARHAT."

FARHAT ta maimaita sunan a zuciyar ta, tana tsaye a in da take bata motsaba, ganin kamar bata da niyyar zuwa yasa shi fara d'ingisa a hankali yana nufarta, ganin haka yasa ta saurin takowa itama ta nufo shi, a gaban shi ta tsaya ta zuba mishi ido tana jiran ji daga gare shi.

Ya kalleta ya sakar mata murmushin da ke shagaltar da ita, ya ce "Kin nemi yafiyata na yafe miki amma ni har yanzu baki ce kin yake min ba akan abin da na miki ran nan." Shiru ta yi tana son gano akan me yake magana, ganin kamar ta manta yasa a hankali ya kai hannun shi goshinta daidai inda ta k'uje ran nan ya ce "For dis." Sai lokacin ta gane me yake nufi, Karo na farko ta saki murmushi har fararen jerarrun hakwaranta suka bayyana.

"Masha Allah, tsarki ya tabbata ga Ubangijin halitta." Ya fada a zuciyarsa, muryarta ne ya katse mai tunani cikin sanyi ta ce "Baka yi min komai ba Yaya Alamein, idan ma kayi min ni ban 'rike ka rai ba, I know it fault, duk wanda aka yi wa kanwar shi abinda Mom ta yi wa Fatima in dai yana da hankali zai iya daukar matakin da yafi wanda ka dauka, ka ce wa Fatima ta yi hakuri, kaima kayi hakuri." kallon ta kawai take yi cike da birgewa har ta dasa aya. Ta matukar birge shi kalamanta da hikimarta sak irin na Fatimarsa sai yake ganin kamar ma ita ce tabbas maganar Ummi gaskiya ne a cikin tarayyarasu akwai wani sirri wanda Allab daya haɗasu ya barwa kansa sani. A tausashe ya ce "Kina son ganin Fatima?" Bata iya bashi amsa ba sai gyada kai da ta yi da sauri, ya ce "Oya muje na kai ki wajenta." "Da gaske!" ta furta cikin wani irin farin ciki tare da zaro ido............

Harda na gobe🙈🙈🙈

09116099486
[12/29, 2:43 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀

~FARHAT~

*PAGE 29*

Murmushi ya yi tare da gyad'a mata mata kai alamar da gaske ya ke yi. "Oh my god!!! I'm so happy." Ta fad'a cike da mad'aukakin farin ciki, fuskarta dauke da yalwataccen murmushi.

Kallon juna suke yi kowanne zuciyarsa fari 'kal, shima murmushin yake ganin yadda ya wanzar mata da farin ciki, cikin sigar zaulaya ya ce "Miss smiller! Wannan murnar duk na ganin Fatima ne?" Da sauri ta gyada kai, ya girgiza kai tare da ce wa"To Oya let's go to her." A hankali ya juya ya fara tafiya yana d'ingisa k'afarsa.
Tsayawa ta yi tana karewa bayan shi kallo, ta na zayyana irin kyawun surar shi a ranta, sai da ta ga yana daf da shigewa zaure sannan ta bi bayan shi da sauri.
Chapter 31 · 0% Book details