← Book details Joy Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 46

Sashe 14

Joy Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Peter bai yi dogon tafiya ba ya iso kofar gidan, tunda dama already ya san gidan don haka bai sha wani wahala ba, daga nisa kad'an ya faka motar shi ya karaso da kafa, babu kowa a wajen hakan yasa ya dan jingina yana jiran ya samu yaro ya aika kiranta, sai dai ya kai kusan minti 30 babu yaron da ya gifta gaba daya duk ya gama gajiya da tsayuwa, cikin wannan halin Al'ameen ya fito daga gida cikin shirin shi na tafiya masallaci, don gabatar da sallan la'asar da ake kira, da sauri Peter ya iso gare shi, ya mishi sallama a gurbace tare da mika mishi hannu, kollo daya Al'ameen ya gane Arne ne, hakan yasa ya ki amsa masa sallman da ya mai kuma ya ki bashi hannu, peter bai damu ba, a haka suka gaisa, Peter ya ce da gurbataccen hausan shi "bros pls a gidan kake." Kollon uku saura kwata al'ameen ya mishi kafin ya amsa da "yes." "Thank God!" Peter ya fada yana Ciro pepen daga aljihu, ya ce " Miss Joy ne ta aikoni na kawowa Fatima wannan takardan pls ko zaka iya yi min magana da ita." Ji Al'ameen yayi ran shi na tafasa, ya tsani duk wani Abu da zai tuni mishi da ko sunan yatinyar ne balle abin da ya shafe ta, kamar ya fatattaki Peter ya kora shi, sai dai wata zuciyar ta hane shi dakewa yayi ya ce " Sorry Fatima bata gida yanzu haka sai dai ko ka kawo a ajiye mata. Ni dan uwanta ne idan tadawo zan bata." Jim Peter yayi ga koshi ga kwanan yunwa, idan ya ba Al'ameen wasikar zai zama babu replay din da zai kai ma Joy, kuma sai da ta ringa jaddada mashi ya tabbatar ya tsaya ya amso mata amsa, dagowa yayi ya kalli Al'ameen dake binshi da ido ya ce "Miss ta ce kar na bawa kowa kuma na tabbatar na amso mata repley. " shiru Al'ameen yayi yana nazari kafin ya ce "I'm coming." Dakin shi ya koma yq samu pepa da biro ya rubuta THANK U ya linke ya fita ya mikawa Peter tare da cewa "ka bata wannan ka ce daga Fatima, kagaya mata cewa ka ba Fatima wasikar hand to hand." Amsa Peter yayi kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa ya ce "ok ngd sai anjima." Al'ameen ya amsa da yawwa sai anjima.

Babu yawa.🙏
[12/29, 2:35 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀

*PAGE 12*

Al'ameen na tsaye har Peter ya shiga motar shi ya tayar ya bar layin, mayar da kallon shi yayi kan pepen da ya bashi , kamar zai bude, jin ana kokarin tayar da sallah yasa ya fasa bud'ewan, sakawa a aljihu ya wuce masallaci. Koda suka idar da sallah bai bi ta kan pepan ba, hasalima ya manta da shi, kai tsaye Sayako ya nufa gidan Alhaji Bala ko zai samu keke, don d'azu da safe ya je babu keke a k'asa. Cikin sa'a kuwa yana komawa ya samu, singning yayi ya dauka ya kama aiki.

*******

A cikin y'an kwanaki kad'an Amira tayi namijin kokari wajen cusa kanta gurin Ummi, har ta kai yanzu da sun zauna hira Ummi bata da wani zance sai nata, a 6angaren Fatima ma babu laifi don tana kyautata mata sosai tare da jan ta a jiki, kun san kuma ita zuciya an halicceta ne da son mai kyautata mata. Sai dai fa har zuwa yanzu uban gayyar bai san da zamanta ba, iyakar ta da shi gaisuwa, shi ma a d'arare don bata sakin jiki idan yana waje ta dinga sunne-sunnen kai kenan, kunyar shi take ji matuka gaya, babu wata sanayya mai karfi a tsakanin su, hasalima duk sanda zasu gaisa da sunan d'aya daga cikin kannenta yake kiranta alamar bai tantance ta daga cikin su ba, bare har ya kai ga batun bata wani matsayi na musammam a zuciyar shi abinda ke matukar ci mata tuwo a kwarya.

Yau a islamiyya bayan an tashi su ka ke6e da k'awarta aminiyarta Zainabu wacce ita ka'dai ce ta san halin da take ci game da soyayyar Al'ameen, haka duk abinda take wa Ummi ita ta bata shawarar yin hakan kasancewar ta fita wayau da sanin duniya. Cike da damuwa ta kalli Zainabu ta ce "Zainabu Ya zan yi Al'ameen ya so ni? ya zan yi ya kalle ni da kallon soyayya koda rabin rabin wanda nake masa ne? na kusa gazawa zuciyata ta kusa tarwatsewa da soyyayar sa, Babban b'akin cikina shine yadda har yanzu ya kasa tantance ni a tsakanin kannaina bare har na samu wani matsayi na musammam a wajensa, bazan yi ci gaba da jurewa ba Allah ya gani nayi Iya yina wajen kare martaba da mutuncina na d'iya wajen ganin ban zubar da kimata na fara furta mashi kalmar so ba, duk wani alama da zan mishi na ma shi ya kasa ganewa, ya zan yi Zainabu ki bani shawara zuciyata zata tarwatse ki taimakamin plsss zeee."ta karashe maganar tare da kama hannun Zainabu ta kamkame cikin nata da karfi. Cike da tausayawa Zainabu ta ce "Na fahimci halin da kike ciki kawata domin nima na taba tsintar kaina a irin wannan halin da kika shiga, dole zamu sake salo tunda munyi mashi ta baya bai fahimta ba, ya zama dole ya san da zamanki don baza mu tsaya kallon ruwa kwad'o ya man kafa ba." Nan suka shiga tsara next plan din su, wanda zasu fara aiwatarwa a ranar ba sai gobe ba.

********

Lokacin da Peter ya koma gida, Mom na main parlour, hakan yasa bai nemi Miss Joy ba bare ya samu ya bata sakon ta, har dare basu samu haduwa ba, Mom ta kasa ta tsare kamar ta fahimci tana aikata wani abu. Wajejen karfe taran dare ta kasa jurewa, dabara ne ya fado mata , da sauri ta dauki telephone din dakinta takira kitchen ta bada umarnin a kawo mata juice daki, babu jimawa daya daga cikin ma'aikatan gidan ta yi knocking, umarnin shigowa ta bata, bayan ta ajiye mata juice din zata wuce Joy ta kira ta, juyowa yayi cike da ladabi ta tsaya, ta ce mata, tana son ta bin ta kofar baya na kitchen ta je wajen Peter ta karbar mata sako,idan ta karbo ta boye sosai yadda Mom ba za ta gani ba ta hado da bottle water ta kawo mata.

Haka ko aka yi, babu bata lokaci, maid din ta kawo mata, amsa ta yi ta mata godiya, sai da ta maida kofar ta saka lock saboda tsaro, sannan ta koma ta zauna ta shi ga warware pepen cikin wani irin yanayin mai wuyar fassaruwa, idanunta da hankali ta kacokam na kan shi pepan Har ta gama warwarewa. Wani irin yankewa gabanta yayi ya fadi lokacin da idanunta ya saka akan wani unique handwriting mai shegen kyau da kayatarwa, a fili ta furta abinda ke rubuce a jikin pepan THANK YOU. Sake kure rubutun tayi da idanu har zuwa lokacin gabanta bai daina faduwa ba, zuciyarta ta ne ya bata ba rubutun Fatima bane, to amma kuma rubutun yayi kama dana Fatima, sai dai yafi na Fatima kyau da kayatuwa, to idan ba rubutun Fatima bane na wanenen? AL'AMEEN, zuciyar ta ya bata amsa, take wani irin tsoro had'i da firgici ya ziyarce ta, zaro kyawawan idanunta tayi tare da sakin pepen ya fadi kasa.

A dai dai wannan lokacin Al'ameen ya fito daga masallacin unguwarsu, dawowar shi kenan bayan ya mayar da keke ya tsaya yin sallah, yana isowa kofar gida ya tuna da letter Joy, dakatawa yayi a kofar gida kasancewar a kwai wutar NEPA ko Ina na wadace da haske, yasa ya lalubi dakalin dake Jikin gidan su Amira ya zauna tare da zaro latter a aljihu. A hankali ya warware linkin da aka yiwa pepen, shina kamar yadda ya faru da joy haka ya faru da shi ras ras! Gaban shi ya fadi,lokacin da idanun shi su ka sauka akan wani dan rubutu da kwata kwata bai wuce layi goma ba, babu abin da yafi daukar hankalin shi irin drowning din hearts din dake Kasan rubutun, samun kanshi yayi da kasa dauke idanun shi akan hearts din. Bai san Iya adadin lokacin daya dauka a haka ba, sai jin sallama yayi a gefen shi, firgigit yayi tare da saurin kallon side din da ya jiyo sallamar, Amira ce sanye da dogon hijabinta daya sha guga har kasa, tana tashin kamshi kamar wacce tayi wanka da turare, idanun su na sarke wa tayi kasa da kanta teke duk wani jarumta da karsashin ta ya tafi, jikinta ya d'an fara rawa.

Kallon ta ya yi, ganin tayi shiru ya ce "Aysha ya akayi." (Kanwarta dake binta) wani bakin ciki ne ya ziyarceta take ta dake , cikin dan rawar murya ta ce "Amira ce ba Aysha ba ce." Ya ce "Ooh sorry Amiran Ummi ko?" Dan murmushi tayi cike da farin ciki, ya sake cewa " ya akayi ne?." Dan Jim ta yi kafin cikin dan. jin nauyin tsareta da yayi da idanu, ta kara yin k'asa da kanta ta ce" Yaya Ameen dan Allah dama nace idan babu damuwa zan kawo pass questions na waec and neco ka koya min saboda muna daf da fara exam kuma kuma ni ban samu yin karatu sosai ba." Ta kareshe maganar a d.arere.

Shiru yayi yana jin wani irin kasala na saukar masa saboda karfin turaren da ke ta shi daga jikinta.

Ganin yana shirin Shiga wani yanayin yasa ya ce da sauri " shikenan kike idan na saka lokaci zan neme ki." Daga haka ya mike ya shigo zauren gidan su da sauri ba tare da ya jira ita ta fara tashi ba.......

Yau na je suna ban wuni gida ba amma dai ga alkawarin da na muku jiya na cika duk da babu yawa🙏
[12/29, 2:35 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀

*PAGE 13*
Chapter 14 · 0% Book details