Sashe 9
Hamdah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ko da tagama suya kan taburman da na shimfiÉ—a tazo ta zauna cinikin da tayi ta zube su kasa muka soma kirgawa,muka cire kuÉ—in komai da akayi amfani da shi, cikin murnar ganin yau an sami riba har dubu É—aya da É—ari biyar baki na washe nace
"Kai gaskiya yau kam an sami riba har dubu da É—ari biyar".
murmushi tayi tace
"Ai kam yau alhamdulillah bari na fita nayiyo mana cefani".
da sauri nace
"Yauwa Mama yau ni dai bana jin sha'awar hantar nan gara kifi ma kiyi mana irin miyar waken suyar da ranar kika yi manan nan sai asa kifin kawai a ciki".
Nafaɗi hakan ne dan nasan tana fita ribar da aka samun zai kare wajen yin cefanen girkin da take yi min wai na karin jini har sai ta taɓa uwar kuɗin ma.
tace
"To shike nan sai ayi shi tun da kina so".
sallamar da akayi ne yasa mu É—agowa dukan mu,
Wani saurayi ne mai suna Sagir dake layin unguwar, kusan kullum sai ya shigo siyan awara,
da ai kowa yake a siya masa amma yanzu da kansa yake shiga cikin gidan ya siya,
idan ya shigo yarika bina da kallo kenan idan na gana haka sai na shige É—aki.
karaso wa in da muke yayi yana faÉ—in
"Mama ban shigo da wuri ba Allah dai yasa an ajiye min".
murmushi Mama tayi tace
"Ai kuwa yau Sagiru gaba É—aya na mance da ma HAMDAH ce ke tuna min waÉ—an da ake ajiye musu ai kuwa yau ban ajiye wa kowa ba na man ce gaba É—aya dan ita mai tunin bata nan bata jima da shigo wa ba,
Sai dai kuyi hakuri sai na dare kenan".
tsayuwar sa ya gyara tare da dubana yace
"Shine yau baki tunawa Mama ba ai da kafin ki fita kin tuna mata da ta ajiye min kinga dai yanzu laifin kine".
"Laifi na kuma?".
yace "Eh ai kece baki tuna mata ba".
Mama tace
"To an jima kam zata yi min tuni sai na ajiye maka".
yace
"Yauwa to Allah yakai mu".
Sai kuma ya É—an sosai bayar keyan sa ya dube ni kana ya mai da duban sa kan Mama yace
"Mama zaki bani wan nan É—iyar taki mai rashin tunin nan".
da sauri na É—ago jin abun da yafaÉ—a, Mama ko cewa tayi
"Wa wai HAMDAH kake faÉ—a?".
tafaÉ—a tana duban mu duka da shi.
yace
"Eh ita" Mama tayi murmushi tare da faÉ—in
"To ai matar aure ce kai baka ganta da ciki ba haihuwa tazo dan mijin ta soja ne kaga bazai yiwu ta haihu a can ba shiyasa tazo gida".
Ido ya waro tare da buÉ—e baki da mamaki yakai hannu yarufe bakin yana faÉ—in
"Matar soja Innalillahi wlh ban taɓa luraba sai yau duk shigo war da nake,wai Allah ya rufa min asiri da kafata ta ɓalle sabo da sallen kwaɗo inayi ana zuba min bulala,a gafar ceni wlh rashin sani ne ki tai make Ni kada ki faɗawa yallaɓoi,
wlh Ni sai yau naga cikin ni duk gani na da ita ban taɓa lura da cikin ba".
yakarashe maganar yana dubana da haÉ—e hannayen sa guri guda alamun roko.
Murmushi nayi dan kullum idan ya shigo da hijabi a jikina kuma azaune yake sami na,nasan shi yasa bazai ga cikin ba.
yace
"Um bari na tafi wata kila ma tsautsayin wahala ne yashi go da ni,amma da zanyi ido biyu da jarumin sojan nan da na jinjina masa dan ya iya zaɓe kwarai,ko da zai sani sallen kwaɗo sau goma sabo da na tayashi murna".
Mama tace
"Ah to gara dai ka tafi".
"Ai natafi ma". yayi waje yana dariya....★
A can cikin garin birnin Bauchi'n Yakubu kuwa,
A halin ABDULLAHI TURAKI na hango motocin su suna fitowa daga cikin airport,motocine guda uku suke tafiya a jere, cikin mota na biyu wan da yakasan ce shine na tsakiya a ciki na hango su Abbu da Mamie, fuskokin su ɗauke da farin cikin ganin su a kasar su kuma garin su........!★
Mommyn twins ce
Cike parlour'n yake tam da Æ´an uwa da abokan arziki,
kowa sai juya tsara bar da aka basa yake cike da jin daÉ—i.
Mamie bin cikin parlour'n da mutanen cikin tayi da kallo a karo na ba adadi,
yau kwana biyu ke nan da dawowar su amma bataga HAMDAH acikin masu zuwa yi musu sannu da dawowa ba,ko a airport kuwa da a kaje tarar su ba ta cikin waÉ—an da suka je tarar tasu,bata kawo komai a ranta ba dan tasan iyanzu kam cikin yakara girma ko shi zai hanata,sin tiri kan hanya.
Bayan sallar Isha Ya SALEEM yashigo cikin bedroom É—in Mamie tana zaune tana warewa Æ´an uwan ta na kan gari waÉ—an da bata basu tsaraba,
a hankali yakara so cikin É—akin yazau na kan kujerar da ke cikin É—akin tare da gai da Mamie,
ta amsa tana faÉ—in
"Har yanzu baka tafi gida ba".
cikin yana yin nan nasa kamar an sashi dole yin maganar ko kuma mai jin bacci yace
"Eh yanzu zan tafi na shigo nayi miki sallama ne".
tace "Gara kam ka tafi yanzu haka HAMDAH na can tsoro duk ya ishe ta ga Halima ma naga bata koma ba tace min anan zata kwana".
wani irin bugawa kirjin sa yayi da karfi jin an ambaci sunan ta.
shi har ga Allah ma ya mancewa da wata mai suna HAMDAH in ba yanzu da Mamie ta faÉ—a ba, tun ranar da suka rabu ya goge sunan ta cikin zuciyar sa baya kaunar yaji wani ya ambaci sunan ta,
sai kuwa akayi sa'a a cikin gidan sa uwar gidan tasa wato Na'ima tayi ruwa tayi saki wajen ganin babu wan da yakuma tuno ta bare har arika ambaton sunan ta,dan hakan shine kaÉ—ai zai tai maka wajen ganin ya daÉ—a mancewa da ita na har abada,
kamar yan da bokan ta yasar mata tatafi bazata kuma waigowa ba
sai dai ma takuma yin nisa da su.
yanzu kuma ba wani zuwa family House É—in su yake sosai ba,kuma ko da yaje É—in ma gaisu wa ce kaÉ—ai suke yi yatafi.
da karfi-karfi haka zuciyar sa ke bugawa,har sai da yakai hannu ya dafe dai-dai saitin kirjin sa.
Mamie ta janyo wani É—an madaidaiciya akwati tabuÉ—e, dogayen riguna ne da gyale da sauran su zafafa sai gefen cikin akwatin kayan baby ne wanda mace da na miji zasu iya sawa.
murmushi tayi tare da faÉ—in
"Ga tsara bar ta dana mai gidan dan Ni wa mai gida na tsiya bawa kishiya ba,Abbu ne yayi wahalar siyowa kishiya".
tayi maganar fuska É—auke da murmushi cike da so da kaunar jikan ta da take saran fitowar sa duniya ko mace ko na miji.
ta cigaba da faÉ—in
"Da zan baka kakai mata amma dai bari na bari idan tazo sai ta haÉ—a dana gun Abbu'n ku ta tafi da
shi tun da shi har yanzu bai buÉ—e jakar saba".
Har lokacin hannunsa na dafe kan kirjin sa a hankali ya mike,batare da yace komai ba yafita,
bayan sa Mamie tabi da kallo bata kawo komai a ranta ba dan tasan halin É—an nata sarai miskilanci a jinin sa yake.
yana dai-dai ta zaman sa cikin mota yaja gajeren tsaki jin har lokacin zuciyar sa bata fasa bugawa ba,a haka ya koma gida..
Washegari Mamie tayi ta zuba ido ganin zuwan HAMDAH amma shiru har yamma.
A ɓangaren Abbu ma ranar sai da ya tanbayi Mamie wai shin HAMDAH tazo ta karɓi tsara bar tane bata karɓi na amaryar sa ba.
Nan Mamie ke ce masa ai ko sannu da dawowa bata zo musu ba amma dai tasan jikin ne yasoma nauyi...
Bayan sallar magriba,
da sauri Masa'ud yabi bayan Abbu suka shiga gida tare, a parlour suka zauna in da suka tadda Mamie nan zaune,zama Masa'ud ya gyara dan yau yasha alwashin faÉ—a wa su Abbu abinda ke faruwa duk da Ummi tace kada wani ya sanar musu sai sun daÉ—a hutawa sosai.
a cewar sa wani hutu yarage musu bayan Æ´ar uwar su ba a san halin da take ciki ba.
"Abbu Mamie".
Masa'ud ya kira sunan su yana duban su,a kusan tare suka amsa yayin da suka mai da hankalin su kan shi.
Zaman sa ya daÉ—a gyarawa kana ya nisa yasoma magana,
"Abbu kunsan abun da ke faruwa kuwa?".
A tare suka haÉ—a baki wajen cewa
"Meke faruwa?".
"Assalamualaikum"
gaba É—ayan su suka juyo jin muryar Aunty Rafee'at tana sallama,suka amsa mata,ta karaso ciki ta sami guri ta zauna tare da gaishe su in da Masa'ud ya gai data.
Mamie tace
"Unguwar dare bakya bari gari ya waye ba".
Hmm. kawai tace dan batajin abun da ke tafi da ita zata iya barin sa sai gobe, kwanaki arba'in da suka shuÉ—e tayi sune cikin kunci da tashin hankali,
Dr Farooq ma yayi-yayi da ita kan tabari gari yawaye tace a'a yau kam bazata bari maganar yakuma kwana ba,a son ta ma tun ranar da suka dawo Nigeria taso faÉ—a musu Ummi ce ta hana ta,tun da har yau sun yi kwana uku da dawowa bataga amfanin rashin faÉ—a musun ba gara su ma susanin.
Masa'ud na ganin yanayin ta yasan abun da yazo faÉ—awa su Abbu shi ya kawo ta,
yace
"Aunty Rafee'at yanzu da ma zan faÉ—a wa su Abbu kenan".
da mamaki iyayen nasu ke kallon su Mamie da tun É—azu da Masa'ud yace sunsan abun da ke faruwa taji gaban kirjin ta ya yanke.
tace
"Wai me ke faruwa ne kam?".
tayi tambayar cikin yanayin fara shiga damuwa da fargaba.
A sannu Aunty Rafee'at tashiga basu labarin abun da ya faru tun daga farko har da korar da Abba yayi wa HAMDAH.