← Book details Hamdah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 34

Sashe 22

Hamdah Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

wani dattijo ne yafito daga cikin wani gidan da ke gefe da garken shanun,
kana yashiga cikin shanun cikin girmama wa da ladabi matasan makiyayan nan suka shiga gai dashi cikin girmamawa,ya amsa cikin sakin fuska
kana yashiga tayasu É—aure shanun.
jijjiga Naseem da yake ta musu-musu a bayana nashiga yi dan nasan yagaji ko kuma jikin sa ya masa tsami dan yabugu sosai,ina matse ido hawaye na zuba,
tuni Nasmah ma ta saki kuka, sai na cigaba da gargiza su ina hawaye,
yan da nake girgiza sun hakan yasa hannuna ke girgiza zafi har cikin raina.
da sauri dattijon nan yafito daga cikin garken shanu yana É—an waige-waige da alama dai kukan yaran yaji yasashi fitowa duba da yan da yake ta É—an waige-waige,
nan idanunsa ya sauka kanmu da mamaki yake kallona kana yace
"Ke wanene me kike yi a na?".
yayi maganar idanunsa a kaina cikin hausar sa da bata tsaya ba,
banyi magana ba sai masar ƙwalla nake,
"Ke wanene nace me yasa mi yaron?".
cikin zubda ƙwalla nace
"MunfaÉ—i ne shine yaji ciwo kuma yunwa suke ji".
"Yunwa?".
yafaÉ—a yana kallo na".
na gyaÉ—a kai na alamar Eh, yaÉ—an yi shiru yana kallona,
kana ya kalli su Naseem da Nasmah da kyau sannan yace
"Garin yaya kuka faÉ—i haÉ—arin mota ne ina zaku je??".
yajero min tambayar
nace
"Acan kan tudu muka faÉ—i kuma Yola zamu".
shiru yakumayi alamar nazari kana yajuya tare da faÉ—in
"Kubiyo ni".
ai ko da sauri na bi bayan sa.
ya shiga gidan tun daga bakin kofa yake faÉ—in
"Sumaye Sumaye Sumaye".
wata yarin yar dake zaune a tsakar gidan ta mike tana faÉ—in
"Inna wuro Bappa na kira".
wata dattijo war mata tafito daga cikin bukko da sauri tana amsa kiran sa,
tare da faÉ—in
"Gani nan Malam".
yace
"Zo ga wani bakuwa nan tazo kuma wai yaron ta ya faÉ—i a kasa kuma yana jin yunwa bashi abinci yaci".
tace
"Subhanallahi kawo shi nan mugani garin yaya?".
namatso in da take tana kokarin karɓar Naseem dake ta zandara ihu, garin cirosa sa a bayana sai ta bige min hannun,
yarfe hannun nayi tare da faÉ—in
"Wayyo Allah hannuna".
tace "Ayya Allah kam sansu ke ma hannunka na siwo ne?".
kai na gyaɗa cikin zubda ƙwalla nace
"Eh da muka faÉ—i ne nima na buga hannuna".
kallon yarinyar dake zaune a gefe tayi tace
"Zo Mero kikarɓa mata yaron hannun ta".
yarin yar ta matso da sauri ta karɓi Nasmah,
tace
"La Inna wuro itama taji ciwo".
Inna wuro tace
"Oh wani irin faÉ—uwa ne haka sai kace haÉ—arin mota".
tafaÉ—a tana roko hannuna tare da cigaba da faÉ—in
"Ko dai haÉ—arin mota kukayi ne".
yarfe É—aya hannun nayi nace
"Wayyo Allah na".
Inna wuro tace
"Malam itama ta buga hannun ta inaga tayi targaÉ—e a hannun".
"Nima dai haka nace kamar wan da suka faÉ—i a mota".
yamatso kusa da ni yana faÉ—in
"Naga hannun".
naÉ—ago haka na mika masa yarike yana É—an jujjuyawa,
rumtsa idanuna nayi da karfi ina faÉ—in
"Wayyo Allah wayyo Allah".
yace "Sannu kinyi targaÉ—e ne".
sai ya saki hannun
"Bari nakawo magani nasha maku".
Bappa yafaÉ—a yana shigewa cikin bukko,
ni dai yarfe hannun narika yi ina matsar ƙwalla.
yana shiga yafito da wasu robobin mai guda biyu, ya dawo in da nake.
Inna wuro tayi sauri ta É—auko taburma ta shin fiÉ—a tace na zauna,
na zauna shiko a kan kujera Æ´ar tsuguno ya zauna kana yaruko hannuna yaja yaja yajijjiga shi da É—an karfi, kara na sake cikin jin azaba har cikin kokon zuciya ta, ina shushshure kafafu kasa kamar zan saki fitsari a jikina.
kana yabuÉ—e É—aya daga cikin roban mai daya fito da su ya lakato maganin ciki yashafa min a hannun da tuni yahaÉ—a zufa,kana ya saki hannun yana yimin sannu.
Inna wuro tace
"Sannu zakiji daÉ—i har kiyi bacci".
kai kawai na gyaɗa mata ina matsar ƙwalla, na matsa baya na jingina da jikin garu ina rike da hannun da ɗaya hannuna...
ya karɓi Naseem yashafa masa maganin dake cikin ɗaya robar a duk kanin ciwukan jikin sa,
yana yi yana É—an mammatsa jikin sa har ya gangaro kasan kafar sa ai ko yana rike guiwar kafar sa yakara sautin kukan sa yana kankame jikin sa,
kafar yarike da kyau yaja sai ga kafar tayi kass,
Maganin da yashafa min a hannu yashafa masa a kafar yana faÉ—in
"Gocewar kashi ne".
kana ya mikawa Inna wuro shi ta karɓe shi tana girgiza shi da yi masa sannu,
nan ya karɓi Nasmah itama ya sha fa mata bayan yagama dudduba jikin ta ko itama da buguwa ko gocewar kashin a jikin ta,sai dai ita ba a samu gocewar kashin ba sai dai buguwar kawai...

Ina zaune nayi jugum zuwa lokacin kam alhamdllh zafi da zugin da hannuna yake min sai raguwa yake,
ido na zubawa su Naseem da ke jikin Inna wuro sunyi shiru sunata rarraba ido,
Bappa kuwa tun da yagama shafa mana maginin yamike yafiya sai yanzu yashigo rike da kwarya a hannunsa,
ya karaso in da muke ya mikawa Inna wuro kwaryar yana faÉ—in
"Basu susha dan su daÉ—a jin karfin jikin su".
Inna wuro ta amsa
tare da faÉ—in
"Dama yanzu nake shirin aiken Mero taje ta tatso musu madarar".
ta aje kwaryar ta mike da sauri ta shiga bokkar dake gefe da mu tafito da kwarya da ludayi guda biyu,
ta raba madarar biyu ta mika min rabi kana ta zauna tana É—ibawa da ludayi tana baiwa su Naseem,
ai ko suka karɓa suna ta sha,
A hankali na É—ibo nadarar cikin lodayi nakai bakina,
lumshe idanuna nayi jin É—umi da garÉ—in madarar ya ratsa ni,ai ko na gyara zamata sai gashi na shanye madarar tass har ina tanÉ—e baki...
Bappa ya fito da shirin tafiya masallaci ya dube ni yana faÉ—in
"To ni zan tafi masallaci yanzu ina zakuje tun da naga kun gama shan madarar?".
kaina a kasa nace
"Yola zanje".
suka haÉ—a baki da Inna wuro wajen faÉ—ar. "Yola??".
Bappa yace
"To ke da zakije Yola me ya kawo ki rugan nan Yola da yake tacan gefe Yola da yake tacan mezai sa kibiyo ta nan?".
ko mai ban ce ba sai kasa da kai na da nayi.
da sauri ya juya yanufi kofa yana faÉ—in
"Bari na tafi kar na rasa sallah".
a hankali na mike nace
"Ni ma zan yi sallar".
Mero ta mike da sauri ta zubo min ruwa a buta ta mika min tare da nuna min banÉ—aki.
na je nayi sarki kana nafito nayi al'wala,
koda na fito na samu Inna wuro ta shinfiÉ—a min sallaya Mero kuma na rike da Nasmah sai wasa da gashin kanta daya cukuikuye take,
bayan na idar da sallar ina zaune kan taburma tuni su Naseem sun yi bacci,sai na gyara musu kwanciya kan taburman na rufe su da abun goyon su.
Mero da Inna wuro ma duk lokacin sun shiga yin sallah..
ina zaune jigum...

Bappa ya shigo da sallama,
na amsa kallon in da su Naseem suke kwance yayi kana yace
"A'a ya zaki kwantar da yara a wannan gurin sanyin ke bakyajin sanyi?".
murya ya É—agaga yashiga kiran Mero,
da sauri Mero ta fito yace
"Kira Sumaye tazo ta É—aga yaran nan anan ya za'a barsu cikin sanyi".
da sauri Inna wuro tafito tana faÉ—in
"Ai kwanciya sukayi ne".
ta dube ni tana cigaba da faÉ—in
"Ke ma in kin gama ki taso a sanyin nan".
ta É—auke su ta kaisu É—aki.
numfashi na sauke wai yau mu ake ce wa mutashi a cikin sanyi kar sanyi ya kamamu Allah sarki rayuwa bayan acikin ta mukayi rayuwar wata biyu da É—ori..
A sannu na mike nabi bayan su muka shiga cikin bukka.
abakin gado gado irin na Fulanuka in da aka kwantar da su Nasmah na zauna.
tace idan ina jin bacci na gyara na kwanta a gefen su,a hankali kuwa na gyara dan kuwa baccin nake ji...
Chapter 22 · 0% Book details