← Book details Hamdah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 34

Sashe 17

Hamdah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Direban dake tuka motar yazoge glass É—in motar yaleko ni kana yace
"Tafiya ne?".
Kai na gyaÉ—a masa kana nace
"Eh". yace "Wani gari".
nace "Yola".
"Ok shigo ai wannan motar Yola can na nufa yanzu".
da sauri na gyara rikon Naseem nasun kuya na janyo akwati na,
da saurin sa yafito daga cikin motar ya karɓi akwatin yabuɗe but yasaka kana yabuɗe min gidan baya nashiga kana ya mai da murfin yarufe yakoma mazaunin sa kana yaja motar muka soma tafiya.
mamaki ne yakama Ni lokacin da naga Ni É—aya ce cikin motar babu kowa babu ko fasinja acikin motar.
abun da tadaÉ—a bani mamaki ma shine motar batayi kama da na fasinja ba,ban kuma lura da hakan ba sai da nashiga motar.
lafiyayyiyar mota ce irin na shiga kawai. shiru nayi ina bin motar da kallo motace mai kyau tabbas batayi kama da motar É—iban fasinja ba.
wani irin tsalle zuciya ta tayi dai-dai lokacin Naseem da Nasmah suka zabura lokaci guda suka kankame ni Naseem dake rike a hannuna yajuya kansa tare da kife fuskar sa a kirjina sai ya shiga sauke numfashi,
leka fuskar sa nayi sai naga yana bacci,
Saukar numfashin Nasmah nakeji a bayana itama a hankali.
Idanuna na lumshe tare da kuma buÉ—e su,
"Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un"
nafurta kan laɓɓana batare da nasan da fitowar sa ba.
yayin da yanayin da nake jinsa a tun motar farko da na rika ji ya karu matuka,
sai dai har lokacin nakasa gane kalar yanayin.
haka mukayi ta tafiya yayin da tsalle da bugawar da zuciya ta take ke karuwa a kowani dakika,jin zuciyata nacigaba da azalzala ta sai nashiga nanata kalmar Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un.
tafiya muke tafiya mai nisar gaske nayi mamakin ganin garin Yola da irin wannan nisar wajen karfe 6 muna kan hanya can muka iso wata kungurmin daji danake hangosa daga nan kan hanya.
a sannu direban yaÉ—an sakai ta godun da yake yafaka motar a gefen titi sakamakon kiran da ya shigo wayar sa,
yajuyo ya kalleni yace
"Bari na amsa waya ina zuwa".
jiki a sanyaye nace masa "To".
ya sauka da sauri ya mai da murfin ya rufe, yaÉ—a masa can gefe yana wayar,
gabaki ɗaya hankali yakuma mummunar tashi tsoro mai firgitarwa ya lulluɓe ni, bugu da kari ganin yanayin da Naseem da Nasmah suke ciki duk da bacci suke amma sai zabura suke suna kankame ni.
daÉ—a kankame Æ´aÆ´ana nayi ina ambaton sunan Allah,
magana yake yana kallon motar a hankali nakai hannuna nayi kasa da glass É—in gefen da nake a hankali batare da na saukar dashi duba.
naÉ—an maso jikin kofar na kasa kunnena..

A hankali nake jiyo sautin maganar sa duk da bana fahimtar abun da yake faÉ—a
sai dai yanayin iska dake kaÉ—a wa yana É—an É—ibo maganar zuwa inda nake.
"Yes oga yaukam nayi babban kamu wata yarin yace da Æ´aÆ´a biyu a ajiye min kuÉ—i na ayi musu kyakkyawar ajjiya ina zuwa a damka min su,
ina faɗa maka rai uku da babba da yara kananu guda ku a dana min kuɗi na kawai munkusa isowa,ina faɗa maka yarin ya ce gatanan inaga budurwa ce da yara guda biyu ai yau kam fitar sa'a nayi, haba oga ai kai ma kuɗin da zaka karɓa akan su bana wasa bane jinin su ma kaɗai makudan kuɗi ne bare sauran sassan jiki".
wani irin masifaffen tsalle zuciyata tayi tamkar zata faso kirji na ta fito,
da karfi na dafe kirji na yayin da kai na yayi wani irin mummunar sarawa,
jikina yaɗauki ɓari kamar mazari kallon mutumin nake cikin matukar firgita da masifaffen tsoro.
Naseem na kuma rungume wa da karfi a kirjina,
cikin matsanancin tsoro hawaye yafara sauka a idona,
a hankali na masa ɗaya ɓarin hannun na rawa naɗaura jikin murfin motar na buɗe a hankali, nazuro kafafuna waje namike,
na mai da marfin a hankali har lokacin yana tsaye yabaiwa motar baya yana ta kan wayar,
cikin sanÉ—a narika tafiya ahankali-ahankali narika tafiya na gangara gefen titi nashiga cikin dajin dake gefen titin a hankali cikin sanÉ—ar narika shiga cikin dajin.
ina shiga cikin dajin narika gudu ina kankame da Naseem gudu nake babu ko kakkautawa da iya kafina ban kuma sanin inda nake jifa kafata cikin tsananin tashin hankali mara misaltuwa,
gudun nake da iya karfina na sai da na isa gindin wata ƙatuwar bishiya kafin natsaya a gun na rakuɓe jikin bishiyar,
ina mai da numfashi,
muryar mutumin najiyo daga can yana faÉ—in
"Ke ina kike ina kika shiga?".
cikin wani irin kaɗuwa da firgici nadaɗa rungume Naseem na rakuɓe sosai ajikin bishiyar, jikina na cirawa...

Ina jin Muryar sa yana ta matsowa in da nake daga in da nake ɓoye ina kallonsa ya gangaro har yazo kusa da ni yana ta waige-waige yana cigaba da faɗin,
ke Ina kike. numfashi nane yasoma yin sama-sama tamkar zai fice a jiki, ganin sa daf da Ni.
dubana nakai kan Naseem da ya buÉ—e ido yana kokarin yin kuka kai nashiga girgiza masa tare da É—aura hannuna kan bakin sa narufe da karfi.
mutumin
ya É—au lokaci agun yana dube-dube kana yayi tsaki tare da faÉ—in
"Kash ga samu ga rashi taya ma akayi har tafita ban ganta ba".
yakuma jan dogon tsaki yajuya yakoma gon motar sa.
ina ganin haka nakuma sa gudu narika kusawa cikin dajin, gudu ne irin na ceton rai ko ina ce rayuka,
bana ko ganin gabana.
ga lokacin tuni guri yasoma yin duhu sai dai hasken farin wata daya haske ko ina...

Tuntuɓe nayi da wata katuwar kututture da bansan tana gaba na ba,nayi luuu zan faɗi sai nayi baya tangal-tangal kaɗan yarage na faɗi da baya,
Naseem ya suɓuce a hannuna yafaɗi kasa timm,bayan da nayi kuwa hakan yayi sana diyyar kan Nasmah ya garu da jikin wata bishiyar dake baya na,
a tare suka saki kuka Naseem kam tun da yasaki wani irin kara mai karfi tun da yasaki karan nan bai kuma yin motsi ba.
cikin tsananin firgici da tashin hankali nayi kasa naÉ—a go
Naseem da ko matsi bayayi na rungume shi a jikina da karfi nashiga girgiza shi da kiran sunan sa,
"Naseem Naseem Naseem katashi dan Allah katashi katashi Naseem".
narika faÉ—a ina girgiza shi da kiran sunan shi amma ko motsi baiyi ba,
cikin rasa abin yi na zube kasa ina cigaba da girgiza shi,
babu ko alamar nunfashi tare da shi, hankali na yakuma mummunar tashi ga Nasmah sai zandara ihu take.
wani kuka nasake da karfi ina girgiza shi da karfi,
É—ankwalin kai na na ciro nashiga fifita shi ina kiran sunan shi,
nan ma shiru rungume sa nayi da karfi ina faÉ—in
"Naseem ka tashi dan Allah kada ka mutu, ka kabuÉ—e idon ka dan Allah Naseem kada ka mutu Naseem Naseemmmmmmm".
NafaÉ—a da karfi cikin muryar kuka...

Duk yan da nayi ta jijjiga shi da kiran sunan sa da kuma yi masa fifita yana nan a inda yake babu numfashi a jikin sa,nayi ta kuka kamar raina zai fita ina kankame dashi,kamar an zabure Ni na É—agosa da sauri na shin fiÉ—a shi a kasa na mike da sauri nashiga duba gefe da gefe na ko zan ga ruwa na yayya fa masa ko Allah zai sa ya tashi,
bazan mance ba ɗan goggo Hauwa yataɓa yin irin yan da Naseem yayi sai dai shi ba faɗuwa yayi ba rashin lafiya yake sai numfashin sa yaɗauke lokacin sun zo gidan Inna sai naga Inna ta ɗibo ruwa tayi ta yayyafa masa sai ya farfaɗo numfashin sa ya dawo.
da gudu nayi gaba narika É—an zaga gurin babu alamar ruwa agurin,
da gudu na dawo in da yake na É—ago shi
nashiga hura masa iskar bakina a fuskar sa, narika hurawa ina kiran sunan shi.
mun kai minti 30 agurin ina abu É—aya babu kuma sauyi,
da sauri nasaka bakina kan bakin sa narika hura masa iska da karfi,
wani nannauyar numfashi ya sauke tare da sakin kuka mai karfi ya kankame Ni,
nima kukan na kuma fashewa da shi na rungume shi ina faÉ—in
"Alhamdulillh Allah na gode maka".
da sauri na kunce Nasmah da take ta kuka tun É—azu na haÉ—e su duk na rungume.
nayita rarrashin su sai da naga sun yi shiru,
nakuma basu abincin su nan ma sai da naga sun koshi,
kana na É—ago Naseem wannan karo shi na goya shi narike Nasmah a hannu.

A sannu narika waige-waigen gefe na nashiga kallon kungurmin dajin da muke ciki ciki kaɗuwa da tsoron ganin guri yagama rufe wa yayi duhu ga daji bakajin motsin komai sai na tsuntsaye da wani irin muryoyi da numfarfashin abubuwan da ban taɓa jin irin suba,
da sauri na juya hanyar da nafi tunanin tanan nabiyo nashigo cikin dajin nabi da sauri narika tafiya sai dai abun mamaki nayi tafiya mai tswon gaske ban ga alamar titi ba,
firgici da tashin hankali yaku baibaye ni ganin kamar daÉ—a kusuwa cikin dajin nake ga wasu abubuwa masu firgitarwa da razanar wa da nake ta gamuwa da su a hanya.
da sauri na ja na tsaya ganin wani abu saman sa haske kasan sa duhu mai tsoratar wa,
cikin firgici da kiÉ—i ma najuya da sauri mai haÉ—e da gudu na koma da baya jikina na cirawa,
sai da natafi da nisa sannan na tsaya,
gefe da gefe na na kalla ina tunanin ta wace hanya ce nabiyo nashigo cikin nan,
a kiÉ—ime na kama wata hanyar ta daban wan da nake ganin ko ita zata fidda ni bakin titi,
nayita tafiya har na godewa Allah amma ita ma babu alamar titi a gaban ta.
nakuma canza wata hanyar haka nayi yawo har guri yagama rufawa gaba É—aya..
Chapter 17 · 0% Book details