← Book details Hamdah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 34

Sashe 18

Hamdah Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Zuwa yanzu kam kuka na fashe da shi ina ambaton sunan Allah duk inda na juya gabar da yamma kudu da arewa daji ne.
Wani kututture da ke gefe da in da nake tsaye ina iya hango shi sabo da hasken farin wata na isa na zauna a kai tare da kuma sakin kuka cikin muryar kuka mai haÉ—e da tsantsar tashin hankali da kaÉ—uwa nake faÉ—in
"Ya Allah kakashe ni na huta Allah ka tsiratar da waÉ—an nan yaran Allah ka gani basu ai kata laifin komai ba,
ya ALLAH ni ka É—auki raina su ka tsiratar da su kasan basu ai kata komai ba".
kukana ne ya tsananta lokacin da na É—aga kai nakuma bin dajin da kallo,
najima sosai a zaune naci kuka har na godewa Allah...........!★

Mommyn Twins ce

Ina zaune a kan icen shiru ina ta girgiza su Nasmah dan bana so su rika kuka dan idan suna yi sai na rika jin motsin abu kamar yana tahowa in da muke,
ina nan zaune babu alamun bacci ko gyangyaÉ—i a idona sai tarin É—inbin tsoro da tashin hankali.......
ganin guri ya É—an yi haske ba kuma hasken farin wata ba,
hakan ya tabbatar min da gari ne ya waye
wato dai mun kwana a zaune kenan.
a hankali na mike tsaye ina bin kungurmin dajin da kallo,
duba na nakai karkashin kututturen da muka kwana a kai jin motsi da huci,
a kiɗime cikin kaɗuwa nayi baya da sauri yayin da hantar ciki na yayi wani irin kaɗawa ganin ƙatuwar maciji tana fitowa daga karkashin iccen,
juyawa nayi da gudu narika gudu cikin matsanancin tashin hankali sai da nayi gudu mai nisan gaske kana na tsaya, ina maida numfashi da gyara rukon Nasmah da tuni suka saki kuka dukan su,
najuya ina wai gen baya na.
kukan nima na sake nakasa rarrashin su sai kukan dukan mu muke.
a galabaice na zube kasa na zaunar da Nasmah a kasa kana na kunce Naseem shima na ajiye shi gefe har lokacin duk kanin mu kuka muke ina binsu da kallon tausayawa,
sai na rungume su duka nakuma fashewa da kuka.
sai da nayi kuka mai isata kana na É—ago su na basu abincin su,
sai dai na san basu koshi ba dan har lokacin basu dai na kananun koke-koke ba tabbbas dole bazasu koshi ba banciba bare su su samu abinci a jikina, ni kai na yunwar nake ji mara misaltuwa.
wasu zafafan hawaye na share kana na mike tsaye,
ina É—an kalle-kallen in da muke zaune, gindin bishiyar mangoro ne ga mangorori sunata rito kasa-kasa,
na É—au wani kara da ke gefe na a kasa na mika hannu nayi tsalle na buga mangorori guda uku suka zubo kasa,
É—aya ja biyun kuma duk basu yi ba haka na É—auka nayi ta shan su kaf sai da na shanye su.
kana nayi taimama,
waige-waige nashiga yi dan bansan inane gabar ba,ina zan fuskanta nagabatar da sallar ba, sai kawai na nafiskanci gabana na gabatar da sallar asuba.
ina idarwa na kuma goya Naseem da tun jiya da ya faÉ—i jikin sa yayi zafi rau har kuma yanzu jikin nasa da zafi sosai,
sannan na É—auki Nasmah muka cigaba da tafiya...

Munyi tafiya mai nisa jin na gaji nakuma tsayuwa na huta, kana na kuma ci gaba da tafiyar,
wunin ranar haka na wuni ina tafiya idan nagaji da tafiyar duk inda na samu sai na zauna sai dai ban kuma yar da na zauna kan itace ko sunkuru sosai ba guri mai É—an fili nake samu sai na zauna,
a duk inda nayada zango na kwatanta lokaci kawai nake sai na gabatar da sallah.
ko yanzu ma a wani guri mai É—an fili na zauna bayan na idar da sallar isha ganin guri yayi duhu sosai sai hasken farin wata,
ina rungume da Naseem da Nasmah,
cikin tsananin tsoro da kaÉ—uwa na daÉ—a rungume su jin matsi da kukan wasu abubuwa cikin wasu irin muryoyi daban-daban.
idanuna na rumtse ina ambaton sunan Allah,
zuwa can da daÉ—ewa sai na rage jin sautin muryoyin,
a haka dai har gyangyaÉ—i yarika É—an fizgata nayi ta É—an gyangyaÉ—in har gari yawaye...
Washegari ma haka na tashi nayita tafiya in na gaji na huta,
yunwa kishin ruwa zafin rana, zuwa yanzu kam jan kafata kawai nake Nasmah da Naseem sai kuka suke nakuma san suma yunwar ce ke É—awai niya da su.
yunwa da ta addabe ni tafiyar ma da kyar nake iya yin ta
zuwa yanzu kam duk wani
bishiyar da na haÉ—u dashi idan naga yayi min kama da na ci sai na sinka naci.
nayi tafiya har na gaji kafata duk sunyi bororo kaya sun kwakkwar janeni bani kaÉ—ai ba hatta su Naseem da kwarjanin kaya a jikin su dan idan muna tafiyar naga wani abun tsoro zan sa gudu ta sana niyyar hakan zasu faÉ—i ko kuma mu faÉ—i tare haka zan tashi naÉ—a ga su na rarrashe su sai in sunyi shiru muka cigaba da tafiyar...

Tafiyar da bansan ina muka dosa ba tafiyar da har yanzu bata ɓulle dani titi da nake sammanin tana gabana ba,
tafiyar kunci da wahala..
Yau kwanan mu biyar a cikin dajin nan,
nagama galabai ta na susucewa nafita hayyaci na,
yunwa kishin ruwa zafin rana,
baci ba sha ba wanka haka mukayi ta rayuwa acikin dajin nan har na kimanin kwanaki biyar.
a hankali nake jan kafata da ta kumbura ganin dare yayi ina ta É—an sauri dan mufita a cikin sun kurun da muke mu isa É—an sararin da nake hangowa a can a gabana,
da kyar na karaso gun na sauke su Nasmah muka yada zangon mu agun,
rukon su na kyara kan kafata cikin sansanin tausayin su, na zuba musu ido,
sun rame sun dishe sun dawo abun tausayi.
ina nan zaune yunwa ya hanani sakat,
suma sai kananun kuka suke wan da nasan kuma na yunwa ce,
daƙyar na rarrashe su sukayi bacci,
niko kasa yin É—an gyangyaÉ—in da nake yi É—in ma nayi saboda tsabar yunwa,
haka na raba dare ina zaune..
koda gari ya waye kuwa nacigaba da aiki na wato tafiya....

Nayi taganin abubuwa masu razanar wa da firgitarwa idan naga wani abun ma kasa ihu ko niman gudu nake sai dai na rufe idanuna da karfi ina ambaton sunan Allah, nakuma sadakar da cewa rayuwa ta dana Æ´aÆ´ana yazo karshe...
Allah sarki rayuwa dani da Æ´aÆ´ana mun sauya kamanni mun rame mun fita hayyacin mu mun dawo wasu irin abu da kama,
mun dawo tamkar mahaukata,
Zuwa yanzu karfina yagama kare wa É—aukan su yana so yafi karfi na,
idan na É—auke su mukaÉ—an yi tafiya kaÉ—an sai naji numfashi na nayin sama-sama idan na É—an tafi kaÉ—an sai na ajiye su na huta sosai kana mukuma yin gaba.
Yau kimanin sati biyu kenan muke rayuwa acikin dajin da nake mana fatan mutuwa dan na tabbata ita zatafi zame mana hutu da wannan rayuwar.
cikin jan kafa da É—an sauri na nufi bishiyar mangoro danake hangosa can sakanin mu daÉ—an rata dashi,
da sauri narika jan kafata dan rabon da na haÉ—u da bishiyar mangoro ko wani abu mai zaki na kai kwana biyar, sai dai naci Æ´aÆ´an itace mai É—aci ko tsami ko burti.
daƙyar na isa gin din bishiyar ina sauke numfashi da sauri na sauke yaran kasa naɗau san da narika kaɓe mangoron sai da na zubo da su da yawa kana na zauna na tattaro su gaba na,nasunku ya sha ba ko kakkautawa har jikina na ɓari,
ina kallon su Naseem suka É—auka waÉ—an da ke kusa da su, suna ta gwaguya ban ko hanasu ba dan suma nasan kalar yunwar da nake ji shi suke ji.
ina gama sha naji cikina yawani irin murÉ—a wa na kwanta a kasa, na da fe cikin nayita murkususu har da hawaye.
najima zube a kasa ina juyi can naji yaÉ—an sassauta min na mike na É—au kesu muka cigaba da tafiya.....
Chapter 18 · 0% Book details