← Book details Hamdah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 34

Sashe 2

Hamdah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kamar a mafarki haka nake jin maganar nasu sai na rika bin bakin kowannen su da kallo duk wan da yakarɓi maganar sai na zubawa bakin sa ido har sai yakai karshen maganar nasa,
gaba ɗaya ƙwaƙwalwa ta tatsaya cak ta dai na ai ki, bazan iya fasalta yanayin da nake ciki ba sai dai inaji a lokacin in da mutuwa zata ɗauke ni da taga ma yimin gata a rayu.
tabbas na yarda da cewa in kaga kana kuka to shima wata rahama ce da sassauci wa zuciya, idanuna sun kafe sun bushe babu ko É—igon hawaye a cikin su, numfashi na sai yi yake kamar zai bar jikina da zai tafi da yayi min babbar gata a lokacin.
Maganar Ya SALEEM najiyo a sama
"Meyasa duk waɗan nan abubuwan suna faruwa ba wanda ya taɓa faɗa min? har da kai mai gadi in su tunanin su bai kai nan ba ai kai duk kanin mu ka haife mu kana kallon ɓarna na wanzuwa bazaka sanar a magance abun da wuri ba".
kasa baba Mai gadi yadaÉ—a yi da kai kana yace
"Allah ya huci zuciyar ka gudun faruwan wata matsalar ce yasa ban sanar ba".
da hannu yayi musu alama da kofa kana yace
"Ku tashi kuje".
da sauri suka mike sukayi waje Na'ima ma ta mike tanufi side É—in ta.
sai a lokacin na sami damar janyo numfashi na.
idanunsa ya rumtse da karfi kana ya mike zumbur ya damko hannuna cikin tsananin bakar ɓacin rai da kunar zuciya.
kai nashi girgizawa jin yan da harshe na yayi min wani irin mugun nauyi nakasa koda iya matsa shi bare na iya furta wani abu da kyar nakuma iya jan numfashi tare da faÉ—in
"Wlh Ya SALEEM ban san komai ba ban san komai game da wannan maganar ba wlh na rantse da Allah duk abun da suka faÉ—a ba gaskiya bane Ya SALEEM cikin nan naka ne kai ma kasan naka ne".
hannuna yakuma damkewa da karfi kana
ya yarfamin wani marin da saida naji jina ya tsaya na É—an wani lokaci,cikin kakkausar murya yace
"Kada ki sake dan ganta ni da wannan kazamtaccen cikin Ni ba uban sa bane
kada ki yaudari kanki da abun da ke cikin cikin ki kan cewa Ni uban sane". sai kuma ya sassauta murya ya É—aura idanunsa kan fuskata kana yace
"Akan me yasa zaki hori zuciyata da wannan mummunar horon me na gaza miki da har bayan bana nan zaki kawo wani cikin gidana harkan shin fiÉ—in mu har ki isar dashi muhallin da ni kaÉ—ai na dace dashi??
Jeki na haramta kaina gare ki,jeki nace!!".
yafaÉ—a cikin karaji tare da hangizani, nayi tangal-tangal kamar zan faÉ—i kasa, wani irin motsawa cikina yayi har sai da nakai hannu na dafe cikin,a fusace ya maso ni tare da kuma ruko hannuna yafisgo ni yanufi kofa yabuÉ—e ya hangizani waje cikin nuna Ni da yatsa yace
"Tafi na daina ganin ki na dai na ganin wannan kazamtaccen cikin na haramta kai na gare ki!".
yakuma nanata karmar haramta kansa a gare ni a karo na biyu,
yana kaiwa nan yaja kofar ya rufe da karfi.
"Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un".
nafurta da karfe sai kawai naji wani kuka yazo min da sauri mai haÉ—e da gudu na juya tare da fashewa da kuka mai tsanani nanufi side É—ina, koda nashiga bedroom rasa me zanyi sai narika zaga cikin É—akin ina cigaba da kuka nakai tsawon minti 10 ina zaga cikin É—akin da kuka narasa meke min daÉ—i me zanyi guda É—aya,
sai a lokacin na juya na isa gaban wardrobe na tuɓe kayan jikina na ciro riga da zani na atamfa nasa na zura hijabi na janyo akwatin da lokacin rasuwar Inna yakai min kaya a ciki tun da na dawo na aje akwatin ban kuma bi ta kansa ba kayane kala biyar a cikin na janyo
nayi waje.

Ina fita naga Salele tsaye a can gefe yayi jigum ya zubawa kofar side É—in ido,muna haÉ—a ido da shi sai ya girgiza min kai tare da share wasu kwallar da suka zubo mishi,juyawa nayi nasoma tafiya in da tafiyar kawai nake amma bana sanin in da nake jefa kafata,
har nafita daga gidan na tari mai a dai-daita ko da muka isa na sau ka nace masa bari naje na amso masa kuÉ—i ganin yan da nake kuka yasa mai napep É—in cewa nabar shi Allah ya jikan rai. dan shi a zaton shi mutuwa akayi.
A farfajiyar gida na yar da akwatin ina jin mai gadi yana tanbaya ta lafiya ban ko juyo ba nayi ciki da sauri,
A parlour na tadda Ummi zaune ganin yan da nashiga yasata mikewa da sauri tana faÉ—in
"Ke HAMDAH menene?".
rungume ta nayi tare da kuma kara sautin kuka na,
a kiÉ—ime Ummi taci gaba da faÉ—in
"Menene me yafaru??".
ban iya cewa komai ba sai rusar kukan da nake.
Jijjiga ni tayi tace
"Ke HAMDAH ki nutsu ki faÉ—a min menene menene kuma???".
cikin muryar kuka sosai nashiga faÉ—in
"Ummi wlh cikin sane narantse da Allah cikin sani".
cikin rashin fahimta da soma shiga damuwa da ganin yan da nake maganar kamar numfashi na zai kwace tace
"Cikin wa? menene ya sami cikin?? kinutsu ki faÉ—a min".
hannunta na rike da karfi cikin fizgar numfashi nace
"Ya SALEEM Ummi Ya SALEEM Ni ban san komai ba ban san me suke faÉ—a ba na rantse Ummi ban san komai ba"..
da sauri goggo Hauwa da Aunty Halima suka fito suna faÉ—in
"Menene me ya same ta?".
Ummi tace
"To ni ma dai ban sani ba ganin ta kawai nayi kamar an jefo ta".
goggo Hauwa ta ruko ni tace
"Ke HAMDAH wani abun ne yafaru a gidan naku?".
kai nashiga gyaÉ—a mata tace
"To menene".
Nace "Goggo Ya SALEEM ne Ya SALEEM ne".
sai kuka yaci karfina,gaba É—ayan su jikinsu yagama mutuwa cikin hanzari Ummi ta nufi É—akin Abba kasan cewar yau Saturday ne yana gida,a tare suka fito da shi har lokacin ina rike a hannun goggo Hauwa,tsawa Abba yabuga min yace
"Ke wai meye haka kin bi kin tadawa mutane hankali da safen nan".
kokarin danne kukan nashiga yi dan nasan halin Abba shi ba irin Abbu bane mai jurar rarrashi,karaso wa cikin parlour'n yayi yana kuma faÉ—in
"In bazaki faÉ—i abun da ya same ki ba yi waje kije kiyi kukan naki,ina SALEEM É—in yake?".
toshe bakina nayi da tafin hannuna cikin jan shashsheka nace.
"Yace na tafi ya haramta kaishi gare ni wai cikin ba nashi bane".
na karasa cikin kuka sosai.
wani irin zabura su goggo Hauwa sukayi Ummi kam sai da tayi baya ta zauna kan kujera tare da ambaton sunan Allah,
goggo Hauwa da Aunty Halima suka shiga rafka salati goggo Hauwa ta buga kirji tace
"Ya haramta kansa da ke ya sake ki fa kenan kuma ciki ba nashi ba SALEEM É—in shaye-shaye yakoma"...

Abba ma sai da ya girgiza da jin abun da nafaÉ—a da sauri ya juya yakoma É—aki.
Number Ya SALEEM yakira yace yazo yanzu-yanzu yana niman sa.
a parlour kuwa zaunar dani goggo Hauwa tayi suma suka zazzauna kowa jikin sa yagama sanyi,a hankali naci gaba da kuka na.
batare da ɓata lokaci ba motar sa yashigo gidan
duk muna zaune a parlour har da Abba yayi sallama yashigo,
gefe da Abba yasamu guri yazauna a kasa kana yashiga gai da Abba da su Ummi, Abba ya nisa tare da gyaran murya yace
"SALEEM wai me ke faruwa ne tashigo ta É—agawa mutane hankali da koke-koke da wasu magan ganun da babu daÉ—in ji wai kace ka haramta kanka gare ta da kuma ciki wai ba naka bane ko mene?".
sautin kuka na kuma karawa jin yadda zuciya ta ke tafasa, sawa Abba ya buga min yace
"Zaki rufawa mutane bakine ko sai nazo gun kiyi Mai dalili!".
kai na na jingina da kafar goggo Hauwa ina kukan a hankali.
muskutawa yayi kana yaÉ—an yi kasa da kansa yace.
"Eh Abba gaskiya ne abun da tafaÉ—a".
basu Ummi kaÉ—ai ba hatta Abba sai da ya girgiza, goggo Hauwa ta waro ido tare da buga kirji tace
"Kai SALEEM kan ka É—aya kuwa kasan abun da kake faÉ—a kuwa?".
Abba ya gyara zama kana yace
"To me yafaru da wannan yanke hukunci haka? An san aure abune mai rai wata kila karshen rayuwar sa kenan, shikuma cikin taya akayi yazamo ba naka ba tana da wani mijin bayan kaine??".
Abba yafaÉ—a yana duban sa dason jin ba'asi dan shi kan sa yashiga É—imuwa matuka...

Kafafun sa ya tanƙwashe kana yayi kasa da kansa yace
"Kayi hakuri Abba da abun da zan faÉ—a".
da sauri na É—ago kai na yayin da naji kukan ya tsaya cak na zuba masa ido babu ko kiftawa.
sai ya kuma yin kasa da kansa kana yacigaba da faÉ—in
"Lokacin da nayi tafi
naje nayi wata 1 ranar da na bar garin nan tana cikin yanayin rashin sarki,ranar da na dawo kuma na tadda ta bata da lafiya bayan da na kai ta asibiti kuma likita ya tabbatar da tana É—auke da cikin wata É—aya gatanan kuma ita shai da ce".
YafaÉ—a yana nuna Ni da hannu.
Salati goggo Hauwa ta farka tace
"Amma lallai SALEEM a gaishe ka sabo da haka zakace ka haramta kan ka da ita sannan kuma ciki ba naka ba? zancen banza kenan mata nawa suke da ciki kuma suna jinin al'ada ai ba akan ta aka soma ba in ba ka sani ba kasani".
Maganar sa ce yasa goggo Hauwa yin shiru da nata maganar cikin É—inbin mamaki kowa ke kallon sa
yayin da shiko ya karkata hankalin sa gurin Abba da son bashi amsar tambayar da yakuma yi mishi yanzu kan cewa da yayi mishi "Dalilin ka kenan?".
kan sa ya girgiza kana yace
"Bayan tafiya ta akwai wani wan da yake zuwa gurin ta É—azu ma ai katan gida na suka tabbatar min da haka".
wani irin zabura su Ummi suka yi suka haÉ—a baki wajen cewa
"Wani yake zuwa gurin ta??".
Abba kam hular kansa ya cire yashiga yin fifita da shi,niko ido na daÉ—a kura masa kamar tv...
Chapter 2 · 0% Book details