← Book details Hamdah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 34

Sashe 21

Hamdah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zaune muke muna cin kayan itatuwan dana sinko mana shiru nayi tare da kasa kunne daga can da nisa nake jiyo muryar kukan shanu,
da sauri na mike tsaye ina cigaba da baza kunnena ina son gane in da kukan shanun yake fitowa,
duk da daga ji yana da nisa da mu sosai,
wani irin farin ciki ne da murna ya lulluɓe ni,
dan na tabbata shanu bazai zauna shi kaÉ—ai cikin daji ba sai da mutum.
cikin tsananin farin ciki da murna na sunkuya da sauri naÉ—au ki Nasmah ina faÉ—in
"Kuzo muje naji kukan shanu a tacan wata kila mu sami É—an uwan mu bil adam a gurin".
ina É—ago zanin goyon su duwasun da suke wasa da shi suka zubo kasa,
banko bi ta kan su ba na goya Nasmah da sauri na É—au Naseem da sauri nasoma tafiya.
har nakusa fita daga cikin bishiyoyin sai na juyo ina juyowa kuwa,
na hango duwasun suna wani irin walkiya kasan cewar lokacin rana yafara tasowa,
Naseem dake hannuna kuwa tsalle yarika yi yana nuna duwasun da hannu yanata kokarin zame wa a hannuna,
murmushi nayi nace
"Oh Naseem dutsunan wasan ku ko bari naje na É—ebo muku".
na juya da sauri na ko ma gurin É—ankwalin kaina na ciro naÉ—ibi duwasun duka na zuba cikin É—an kwalin na É—aure na rike a É—ayan hannuna,
na mike da sauri muka kama tafiya.
ta in da nafi zato da tunanin tanan kukan shanun ke fita na É—au hanyar da sauri.
sai dai munyi tafiya mai nisan gaske amma ban ga wani alamun shanukai ba hasali ma kukan su da nake É—an ji yanzu na dai na, har na fara tunanin wata kila ma kunnena ne yajiye min ba dai-dai ba.
a gajiye na ja na tsaya tare da waigawa baya a raina nake faÉ—in
"Zan koma kawai gara rayuwar can ya fiye min na ko ina acikin dajin nan".
ga mamakina sai naga nayi nisa sosai dan ko katon dutsai É—in nan bana hangowa na juya da zummar komawa bakin kogin sai kuma na hakura ganin nayi nisa sosai.
gashi kuma yamma ta fara yi sai na zauna kawai a gurin a nan gurin muka kwana washegari da safe ina zaune ina ɗan gyangyaɗi dan jiya ban samu nayi bacci ba dan acikin sun kuru muka kwana, kukan shanun nan irin na jiya shi ya farkar da ni firgigit na nimike da sauri.........!★

*Na jiya da gobe na baku*👌🏻😆

Mommyn Twins ce

Zunbur na mike tsaye jin da gaske ba wai ko kunne na bane ke yi min karya kamar yan da jiya nayi tunani,
da sauri na É—auki Nasmah na goya ta,
sannan na É—auki Naseem na rike shi,
na É—auki É—an kwali na da na É—aura musu duwatsun wasan su na rike a É—aya hannuna.
cikin sauri mai haÉ—e da gudu narika bin hanyar da nafi sammani da tunanin tanan ne kukan shanun ke fi.
nayi ta tafiya idan naji shanun sun dai na kuka sai na tsaya na huta idan duka cigaba sai na mike da sauri nacigaba da tafiya,
haka nayi ta tafiya ina yi ina hutawa duk san da shanun sukayi shiru idan suka cigaba da kukan sai nima nacigaba da tafiya ta in da nake jiyo kukan su daga can nesa sosai.
nayi tafiya har na godewa Allah.
ina zaune a gindin wata bishi ina hutawa gaba ki É—aya jikina yayi sanyi dan tun É—azu da shanu sukayi kuka basu kuma ba,
har nafara cire rai da sake yin kukan nasu zunbur na muke jiyo sautin su daga can kasa kuma yanzu nafi jin murtar nasu yafi kusa dani akan na É—azu.
da sauri na mike na soma tafi
É—an tafiya kaÉ—an nayi da sauri naja
burki ganin rami a gabana,
in da nake tsaye kuma tudune mai tsawon gaske,
dan saura kiris na zurma kafata kasa.
daga can kasan shima duk daji ne da bishiyoyi,
daga kan tudun in da nake tsaye ina hango shanukai É—in can da nisa suna ta kiwo kasan cewar a kan tudu nake.
kallon kasa nayi mai uban nisa da tsawo
"Taya zan iya sauka a nan gurin".
nafaÉ—a ina daÉ—a kallon kasan.
a hankali nafara bin gefe tacan ɗaya ɓarin gefen dama na,
ganin tacan É—in bai kai in da nake tsawo sosai ba,
a hankali nafara sauka ina takawa a hankali,sam naki yar da na kalli kasa sai naga ya daÉ—a yi min nisa kaina kuma sai yarika juyawa sabo da nisan sa,
nayi rabin saka daga saunin sai kawai kafata ta sule na zame muka rika gungurawa kasa tuni su Naseem suka saki kara mai karfi,
kan kace me Naseem ya suɓuce a hannuna ya ganaga can yafaɗi kasa,
Nasmah da ke baya na kuwa mukarika gungurawa da ita, cak numfashi na ya tsaya dan ganin ina kokarin isan kasa da baya kamar an juyani sai kawai na faÉ—i da gefe a kan hannuna.
kara dukan mu muka sake da karfi cikin azabar jin yadda na faɗi kan hannuna tamkar hannun zai ɓalle yabar jikina.
nayi-nayi na tashi na gagara tashi nafi minti goma kwance ko kyakkyawar motsi na kasa, ina kallon
Naseem yashe a can gefe yana ta zandara ihu,
Nasmah ma sai ihu take tana goye a bayana har lokacin...

Nayi ta yunkurin tashi na kasa da kyar na kai É—aya hannuna na kunce zanin goyon ta kwanta gefe tana cigaba da tsala ihu duk jikin ta ya kwakkwar jane,
hannuna da na faÉ—i a kansa na É—agosa da kyar kana da kyar na iya mike wa zaune.
yayin da hannun da na faÉ—i a kansan ke min wani irin zugi da raÉ—aÉ—i,
da kyar na yunkura na mike ina É—ingishi nazo gun da Naseem yake kife a kasa yana ihu,
na zauna na É—ago shi da É—aya hannuna mai lafiyar,
nashiga kakkaɓe masa jikin sa ina jijji gashi,
shima duk ya kukkuje a.
Nasmah ta rarrafo tana kuka ta zo in da muke na janyo ta na cigaba da rarrashin su,
duk abun da nake cikin dauriya kawai nake dan nima duk jikina a kukkuje yake,zafin raunukan jikina bai kai na hannun da na faÉ—i a kan sa ba.
duk raunukan jikin yaran sai jini yake fidda wa.
rungume su na yi tare da fashewa da kukan azabar da hannuna yake min, ko matsi nayi da hannun sai naji zafin har cikin raina.

Mun jima zaune agurin jin tamkar karamin zafin ake a hankali na lallaɓa da kyar na mike,
na kamo Naseem da hannun na mai lafiyar na É—agoshi da kyar na iya goya shi, dan shi yafi Nasmah jin ciwo.
ina matse idanuna hawaye na zuba cikin jin azaba,
sannan na É—auki Nasmah na rike ta
a ɓarin hannuna mai lafiyar,
gefe na na waiga in da É—ankwali na dana É—aura musu duwatsun wasan su yafaÉ—i can gefe shima na isa na É—au ka da hannuna mai ciwon,
Jin wani irin zugi da hannun yayi min sai na sake É—ankwalin kasa,
na juya ina faÉ—in
"Naseem Nasmah bazan iya É—auka muku abun wasan kuba hannuna yana min ciwo idan na samu wasu zan É—iba muku a hanya".
a sannu na soma tafiya ina É—aga kafata ahankali-ahankali,
sai kuma na tsaya a raina nake faÉ—in
"To yanzu idan na tafi na bar É—ankwali na anan a ina zan samu abun da zan É—aura a kaina idan na cire hijabi na na rufe su Nasmah da shi?".
nayiwa kai na tan bayar,
idanuna na rumtsa nasan idan na É—auka hannuna zai min zafi.
a raina nake ayyana na kunce Duwatsun na zubdasu sai na É—auki É—an kwalina nasan shi bazai min nauyi ba.
na koma in da yake na É—auki É—an kwalin ina kokarin kuncewa nayi nayi na kunce na kasa saboda da hannu mai ciwon ne jin hakan yana daÉ—a kara ramin zugin hannuna ne sai na bari.
na zaunar da Nasmah a kasa Sannan naÉ—an kunce zanin goyo na cusa É—an kwalin sakanin bayana da jikin Naseem,sai na mayar na É—aura,
kana na É—auki Nasmah muka fara tafiya a hankali.
dan yanzu bana iya tafiya da sauri dan duk jikina ciwo yake min ga su Naseem har yanzu suna ta kuka.

Idan muka É—an tafi kaÉ—an sai na sauke su na huta kana muku ma ci gaba,
Abun mamaki munyi tafiya mai nisa amma har lokacin bamu iso in da shanun nan suke ba, daga can saman tudun da muka gangaro da nake hango su banyi zaton zanyi irin wannan tafiya mai ni haka ba kafin na iso su.
a haka dai nayi ta tafiya har na iso kusa da su,
wasu matasa Fulani ne guda biyu suke kiwon shanun,suna tsaye can gefe sai dai na lura basu san da zuwa na gurin ba duk da dai sakanin mu da É—an tazara,
a sannu na isa gindin wata bishiya na zauna kana na sauke su Naseem,
nayita rarrashin su Nasmah har sukayi bacci.
muna nan zaune a gurin har yamma sai sannan makiyayan nan suka fara kaÉ—a shanukan,sunayin gaba,
Ganin haka na mike da sauri na É—auki su Nasmah narika bin bayan su duk inda sukayi ina biye da su,idan suka tsaya na tsaya idan suka cigaba da tafiya nima na bisu.
haka dai mukayi ta tafiya har naji badaÉ—i gashi babu halin nace zan tsaya na huta sutafi su barni,
tafiyar nake ina matsar ƙwalla sabo da tsaɓar gajiya gajikina da ya daɗa kara yin tsami,
muna nan muna tafiya har guri yafara rufawa.
can naga shanun sun tsaya kana a sannu naga sunayin kwana can na hangi bukkoki gefen bukkar cikin wani gurin da a ka zagaye shanun suka shiga, nan makiyayan suka fara É—aure su,
a sannu na karaso gurin sai na tsaya gefe da garken shanun ina ta raba ido,
Fulani mazaunan gurin sunata harkokin su wasu daga kusurwa daban-daban suna ta É—aure shanukan su da alama suma yanzu suka dawo daga kiwo,
numfashi na sauke tare da yin murmushi cikin zubda ƙwalla gani na acikin mutane wan da nagama fidda sammanin yiwuwar hakan,
a hankali na tako na tsaya kusa da garken shanun....
Chapter 21 · 0% Book details