← Book details Hamdah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 34

Sashe 5

Hamdah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yau kwana na uku a kan layi nake kwana idan nayi ta yawo har dare ya riskeni sai na sami kofar wani gida na rakuɓe gefe a haka zan kwana a zaune,batun yunwa kuwa tarigada ta shiga jikina har ya zamana bana jinta sai dai cikina sai yayi ta murɗeni abun cikina yayi ta motsawa,idan naji kishin kuwa sai na bazama yawon niman kofar gida mai panpo na tara da hannuna nashi,
ina sha kuwa sai nayi hawaye sabo da murÉ—an da cikina zai yi ta min...
Zaune nake akofar wani gidan da nake tunanin a nan yau zan kwana dan yamma tayi sosai ana daf da kiran magriba,
kishin ruwa ne ya dameni tun É—azu sai dai nayi yawo a layin da nashigo yau ban sami wani gida mai panpo a kofar gidan ba,sai dai na fuskanci wannan unguwar na marasa karfi ne dan gine-ginen su ma kaÉ—ai kagani zakasan unguwar talakawa ne.
a hankali na mike na janyo akwakina nacigaba da tafiya ko zan sami ruwa dan ina jin kishin sosai,
ina sharar wata kwana can na hango rijiya mutane na tsaye a kansa anata jan ruwa a cikin sa,
da sauri na nufi gurin dan ruwan da nafi muradi kenan,ina isa gurin na tsaya gefe da wata Æ´ar dattijuwar mata nace
"Dan Allah a sammin ruwa".
matar ta juyo kana tace
"Sha zakiyi ne?".
kai na gyaÉ—a mata tace "Ai ho". wani É—an kara min roba ta janyo ruwan ta zuba ciki tace
"ÆŠauka kisha".
To nace da sauri na É—auka nasoma sha nasha sosai sai da naji cikina ya cika sannan na aje robar tare da yi mata godiya,ta É—au ruwan ta tatafi a hankali naji cikina na É—an murÉ—a min sai dai ba kamar na duk lokacin da na sha ruwan panpo ba,a hankali nasoma tafiya naÉ—an yi nisa da rijiyar kaÉ—an sai na zauna kan wani bulo dake gefen ciyawa jin cikin bai dai na yimin murÉ—a ba.
kai na na cusa sakankanin cinyoyi na inajin yan da cikin ke ci gaba da murÉ—a ni,
da sauri na É—ago kai na jin abu na tafi a kafata,wani irin waro ido nayi cikin firgici da razana ganin maciji a saman kafata,cikin zafin nama na mike tsaye tare da kwalla kara na yarfe kafar da karfi macijin ya faÉ—i can gefe yashige cikin ciyayin dake gurin,
da iya karfina nake ihun ina yarfe kafar....

"Wane ne waye a nan?".
naji murya daga can ana tan baya,cigaba da tan bayar a kayi ana motsawa in da nake,niko sai ihun nake ina tsalle da yarfe ƙafan,
jin an dafa kafaÉ—a na ana faÉ—in
"Subhanallahi Æ´ar nan menene?".
da sauri narike hannun matar da naji tana tan baya na da karfi cikin sananin tsoro nace
"Maciji maciji maciji".
nafaÉ—a da karfi ina cigaba da yarfe kafar,
a kiÉ—ime matar tace
"Ya cije ki ko au da ma kece? me yazaunar dake a nan tun da kinsha ruwan basai kiyi azamar tafiya gida ba, kyazo gidan macizai kizau na ba'azo in da suke Bama ana tare-tare dasu acikin gida bare kinzo nan cikin su,maza zo muje a samiki magani tun kan dafin ya haura miki,wani irin zuwa unguwa ne har guri ya rufa baza'a koma gida ba".
tafaÉ—a tana janyo hannuna,sai lokacin na gane matar itace wacce na roketa ruwa ta bani nasha É—azun nan.
ta janyo hannuna ina É—angala kafar, tana cigaba da faÉ—in
"Dage kiyi sauri muje tun kafin dafin ya haura miki,waÉ—an nan abu ai sai a hankali har gida suke shiga mana dan ma yanzu da sauki muna saka musu magani shine suke É—an yin nesa da gidajen mu".
dai-dai lokacin muka isa kofar wani gida muka shige ciki, murya ta buÉ—e tashiga kwaÉ—a sallama tare da faÉ—in
"Zainabu zainabu matar gidan nan tana nan kuwa".
wata mata tafito daga cikin É—aki tana amsa sallamar tace
"Ina nan, a'a Mama mai awara kece tafe".
Matar da muke tare da ita tace
"Eh,malam Musa na nan kuwa ko har yatafi masallaci?".
Zainabu tace
"Yana nan yanzu yake shirin fita yazaga ne, yauwa gashi ma yafito".
tafaÉ—a tana kallon hanyar bayi,
mutumin da a ka kira da malam Musa ya dube mu yana faÉ—in
"Sannu Mama mai awara ku ne da yammacin nan".
tace
"Eh wlh malam Musa maciji ne ya cije ta dan Allah a sa mata magani kafin ya haura mata".
ya dube ni da har lokacin ina masar kwalla
yace
"To subhanallah garin yaya?".
Mama mai awara tace "Can gefen fadama tabi kasan kuwa kamar gidan su ne".
"Kwarai kuwa Allah yasa ba mugayen bane".
yafaÉ—a yana shige wa cikin É—aki mama mai awara tace
"Amin dai". ni dai ina nan itana masar kwalla ban iya cewa komai ba, matar malam Musa wato Zainabu tashiga tafito da taburma ta shin fiɗa tace muzauna,ba jimawa kuwa malam Musa yafi ɗauke da wata ƴar karamar jaka ya zauna gefen taburman kana yadube Ni yace na miko kafar da yaga ina ta girgiza shi,na mika masa yazuge zip ɗin jakar yaciro kayakin magungunar sa ya zaro wani farin gyale ya gyara zaman sa da kyau ya ɗaura ƙyallen saman kafata kana yaɗauko wani magani acikin kwalba yaɗan ɗiga kan ƙyallen dake kan kafar tawa.
yazubawa ƙyallen ido
sai kuma ya É—ago ya dube ni yace
"An ya nan ne kuwa".
kai na gyaÉ—a da sauri cikin matsar kwalla nace
"Allah nan É—in yahau".
nafaÉ—a ina daÉ—a girgiza kafar dan ji nake kamar har lokacin yana kan kafata,
Maganin yadaÉ—a É—igawa kan gyallen kana ya dubi mama mai awara
yace
"Babu wani alamun dafin maciji a tare da ita gashi nan dai kina gani".
sai ya mai da dubansa gare ni yace
"Amma yaya kikaji da ya sare kin?".
nace "Ganin sa nayi a kan kafata kawai ban san yan da akayi yahau ba".
kai malam Musa ya jinjina kana yayi murmushi da faÉ—in
"Allah ya tai make ki wata kila wucewa zaiyi ke kuma kika tsaya masa takan hanya yabi takafar ki yawuce batare da yasan kina ma gurin ba da taimakon Allah".
mama mai awara ta sauke numfashi da karfi tace
"To Allah ya taimaka ina gama macijiya ce dan su matan basu fiye yin saraba sai sunji matsi".
Zainabu dake gefe tace "Haka ne kam Allah dai ya daÉ—a karewa".
suka amsa da amin nidai ido naketa cirewa cike da tsoro.
mama mai awara ta mike tana yiwa malam Musa godiya tayi wa zainabu sallama tayi waje nabi bayan ta.

Muna fita ta dube ni tace
"Allah ya kare mugayen basu cije kiba,ai wannan mai maganin har wasu garuruwa suna kawo masa jin yan sarar maciji dan shi gada yayi tun iyaye da kakani,idan maciji ya cije ka to da wannan kyallen yake gane kalar macijin da ya sare ka,sai ya baka magani,idan yasaka kyallen dai-dai in da maciji yazuba dafin sa to kyallen zai canza kala yakoma kalar jikin macijin,kinga ai yan da yaÉ—au ra kyallen a fari a farin sa ya É—aga,babu rabon wahala Allah ya kare,
Maza kiyi gida yanzun nan muje na nuna miki hanya mai sauki da zaki fita bakin hanya,jirani a nan na É—auko miki jakar ki".
kai kawai na gyaÉ—a mata yayin da naji wasu zafafan hawaye sun zubo min,yanayin yan da matar take magana yasa ni tuno da Inna ta,
"Allah sarki Inna na tabbata in da kina numfashi bazan taɓa hofanta ba".
Kwalla na kuma share wa lokacin da matar tadawo gaba na tana mika min a kwatina,
tace
"Maza ki tafi gida dare yayi ke bakya tsoron kije gida iyayen ki su miki faÉ—a, Allah ma ya takai ta ai da sai dai a kai ki gida da raunin maciji,
yi sauri muje na nuna miki kinga har na makara markaÉ—en awara nafito É—auka wa shine na jiyo kururuwar ki da yanzu na dafashi har na tsane".

Duk abun da take faÉ—a sama-sama nake jinta wani irin kuna da raÉ—aÉ—i zuciya ta ke min sai sharar kwalla nake.
muna fita gaban rijiyar nan da hannu ta nuna min hanya tace
"Ki mike nan hanyar ta ɓulle har titi Allah bamu alheri".
kai na gyaÉ—a kana a hankali nasoma tafiya,ita kuma tabi ta wani hanyar.
A hankali nake tafiyar idanuna a kasa sai gani nake kamar zan ɗaura kafar kan wani macijin,duk da kuwa guri yafara yin duhu lokacin........!★

Mommyn twins ce

*Masha Allah yau Allah yayi ikon sa na dawo Nagode da addu'o'in ku sosai*🥰

Ina ganin shige war matar cikin wani gida sai na rakuɓe kofar gidan da na iso yanzu,
hawayen tsoro ne suka shiga zuba min a ido shike nan Ni nasan rayuwa ta ta kare yau maciji shi zai yi saniyyar barina duni,tun da kuwa garin su nazo,
wani sassanyar kuka na sake mara sauti nasadakar ma kawai macijin yacije ni na mutu ko zan huta da wannan rayuwar kunci da bakin cikin.
Ji nayi an gasko min toci da sauri na É—ago kai na tare da kare fuskata da hannuna sabo da hasken tocin dake haska min ido.
da sauri takaraso in da nake rike da roba mai É—auke da kullun waken awara a ciki,salati ta doka tana faÉ—in
"Yau naga ikon Allah ƴar nan ashe baki tafi gida ba,kuma zama anan kikayi,hanyar koma wa gida ne ta ɓace miki kokuwa wani laifin kikayi kike tsoron komawa,in ba haka ba mai zaisa kiki komawa gida,ki zauna kina ta rabuɓe-rakuɓe a nan,
yaran zamani ga iya laifi ga tsoron hukunci,tun da kana tsoron hukunci ai sai ka riƙa gujewa ai kata lai fi,to baki tsoron ki karawa kanki wani laifin ni sam banason yaro irin haka to menene am fanin fitowa a gidan da har zaki ki koma wa gidan ki rakuɓe a nan kinata koke-koke, to in bugun naki za ayi bagara ki koma a bige ki ya wuce miki ba, ka zauna ka karawa kanka laifi,ɗauki jakar maza kizo nan".
tafaÉ—a tana dubana.
Chapter 5 · 0% Book details