← Book details Hamdah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 34

Sashe 24

Hamdah Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Zaune muke a bakin gado bayan Inna wuro tayi musu wanka ina shafawa Naseem mai Mero na gefe tana yiwa Nasmah kwalliya da kayan kwalliyar ta sai dariya nake musu ganin yan da take ta zana mata fuska da kwalli irin kwalliyar su na Fulani.
ina gama shafa masa na mike na É—auko kayan su guda É—ayan nan wanda dashi mukayi ta rayuwa a daji,
kullum idan na sa musu idan yayi datti sai na cire musu na wanke,yagama koÉ—ewa har ba a iya gane kalar kayan saboda yayi fari wani gun ma duk ya yayyage.
shekaran jiya Bappa ya siya musu yadi irin na Fulanuka yaba da a É—in ka musu,
yace idan aka É—in ka musu wancan É—in na dai na sa musu waÉ—an nan kayan sun mutu.
na mikawa Mero kayan Nasmah nace
"Gashi idan kika gama mata kwalliyar sai ki sa mata".
tace
"To adda HAMDAH ba Bappa yace a daina sa musu waÉ—an nan kayan ya tsufa ba".
nace
"Eh to ai ba a amso na gun É—inkin bane shi yasa zan sa musu wannan É—in".
tace "To bari na gama mata kwalliyar sai na goye ta muje gun telan mu karɓo".
Nace to.
sallama Bappa yayi daga can waje, Naseem najin muryar sa yakama salle yana mika hannu,
dan yanzu sun saba sosai dan ko masallaci zai je yarika kuka kenan sai yaje da shi,
in ko zaije duba shanukan sa sun dawo daga kiwo sai ya É—auke shi sutafi tare.
in ko Bappa na waje ya É—an jima bai shigo gida ba sai yaÉ—au hanyar kofar gida dan yanzu tafiyar sa ta ya fara kwari.
ganin yana ta tsalle yana nuna kofa da yin kwalaɓe yana faɗin
"Pappa Pappa".
sai nayi murmushi ganin karfi da yaji yana son yayi magana,
Inna wuro dake bakin kofa tayi dariya da faÉ—in
"Yana kiran mutumin shi É—aga murya da karfi bai jika ba".
nace "Ai kam gashi nan sai tsalle yake kamar zai tashi sama".
Mero tace "Yi sauri Adda ki gama sa mishi kayan sai na kai shi".
nace to, hannuna na kika ta baya na janyo wandon sa sai na haÉ—o da É—ankwalina dana É—aura musu duwatsun nan aciki,
ina É—ago É—ankwalin sai guda É—aya yafita ya faÉ—i, na É—auka na sa masa a hannunsa ina faÉ—in
"Ungo abun wasan ka kaje gurin Bappa sai kun dawo Mero kai shi".
nafaÉ—a ina mika mata shi bayan na sa masa wandon,
ta karɓe shi tafita ta kaiwa Bappa shi,
ya karɓe shi yana faɗin
"Mutumin zamuje gurin shanu ko".
yayi dariya tare da yin gwalaɓen shi yana tsalle a hannun Bappa.
har sunkai bakin kofa zasu fita dutse É—in da ke rike a hannun Naseem yafaÉ—i kasa, ai ko yashiga zillewa yana kokarin zamowa kasa,
Bappa yagyara rukon sa tare da kallon kasa jin abun yaÉ—an bigi kafar sa yana faÉ—in
"Tsaya na É—auko maka abun naka kar.."
cak ya haÉ—iye maganar nasa cikin matukar É—inbin mamaki yake kallon abun kamar a mafarki,
hannunsa na rawa ya mika yaÉ—auko dutse É—in,
shiko Naseem hannu ya mika yana kokarin karɓar abun wasan sa yana washe baki.
cikin tsananin mamaki da kaÉ—uwa Bappa ke kallon dutse É—in, kana murya na rawa hatta hannunsa rawa yake yace
"Waya baka wannan abun a ina ka samu!".
yafaÉ—a yana kallon yaron da mamaki yake juya dutse'n a hannunsa wan da hakan yake tabbatar masa da ba mafarki yake ba.
kwaÉ—awa Inna wuro kira yashiga yi yana faÉ—in
"Sumaye Sumaye Sumaye".
da sauri Inna wuro ta fito tana faÉ—in
"Na'am Malam".
dutse É—in ya É—ago yana faÉ—in
"Wannan abun a'ina yafito daga ina yafito a hannun wannan yaron nagani!".
naganar yake cikin kaÉ—uwa.
Inna wuro ta matso gurun Bappa tana faÉ—in
"Wani abun kuma?". tafaÉ—a tana leko hannunsa yace "Wannan abun daga ina yafito".
tace "Bansan ta in da yafito ba a'ina ka ganshi?".
tayi maganar ita ma cikin girgiza da ganin dutse'n da yake nuna mata.
Bappa yace "A hannun wannan yaron nagani".
Inna wuro ta saki kabbara da karfi tana faÉ—in
"Malam ta ya akayi abun nan yashigo cikin gidan nan".
Bappa har jikin sa na cirawa yafara kwaÉ—a min kira yana faÉ—in
"HAMDAH HAMDAH HAMDAH".
da sauri na karasa fitowa daga É—aki dan dama fitar zanyi da naji Inna wuro ta saki kabbara da karfi a tare muka fito da Mero har muna rige-rige.
dutse É—in yaÉ—ago yana nuna min yace
"Ta ina yaron nan yasa mo wannan abun a hannun sa nagani".
kasan cewar rana yafito dutse É—in yafafa walkiya har yana kashe ido.
murmushi nayi ina faÉ—in
"La wannan ai abun wasan su ne".
Ido Bappa ya waro cikin É—in bin tarin mamaki da shiga shok yace
"Abun wasan su!!??" yafaÉ—a cikin kakkausar murya.
kai na gyaÉ—a ina faÉ—in
"Eh abun wasan su ne na bashi yayi wasa da shi".
baya Bappa yayi cikin tarin mamaki yace
"Abun wasa? wannan abun shine abun wasa kinsan meye wannan kuwa!?".
kafaÉ—a na É—aga nace
"Oho ni ban san shi ba kawai dai na É—iba musu ne acan in da muka zauna na É—iba musu sunayin wasa da shi, to da zamu tafi shine na É—ibo musu naga suna son wasa da shi."
baki da hanci Bappa da Inna wuro suka buÉ—e suna kallona,cike da É—inbin mamaki kana Bappa yace
"Wannan suke wasa da shi? da ahi sukeyin wasa!".
yayi maganar yana juya dutse É—in a a hannunsa.
"Bappa to ai akwai wasu ma da yawa na É—ibo musu bari ma kagani".
nafada tare da juyawa da sauri nasgige É—aki,
na kunce É—ankwalin na É—ibo guda 9 a hannuna na kulle É—an kwalin da sauran biyu a ciki na fito da sauri.
ina faÉ—in
"Kagan su Bappa". baya Bappa yaja da sauri tare da jinginuwa da jikin garu yana bina da wani irin kallo mai cike da al'ajab tsorone a'a mamaki ne.
ni kai na sai da naÉ—an razana tare da kallon duwatsun hannuna ko ganin yaga wani abun ne ni dai ban ga komai ba sune dai duwatsun a hannuna.
Inna wuro ma kirji ta dafe tare da waro ido tace
"A ina kika sami wannan abun!?".
Bappa kam kasa magana yayi yana cigaba da bina da kallon mamaki.
nace
"Wlh acan in da muka zauna kusa da ruwan nan na samu acikin wani ruwan da muke yin wan ka shine na É—iba musu shine suke yin wasa da shi".
sai yanzu Bappa ya buÉ—e baki da kabbara
"Allahu Akbar Allahu Akbar Allahu Akbar!". yayi ta nanata kalmar har sau uku kana ya mika hannu yakarɓi sauran na hannuna yana juyasu a cikin hannun shi.
ya dubeni da kyau kana yace
"kinsan meye wannan?".
kai na girgiza nace "A'a".
"Allah mai girma da É—aukaka".
Bappa ya faÉ—a tare da kuma cigaba da faÉ—in
"A wani ruwa kika same su tayaya a kayi kika same su idan mukaje zaki gane ruwan??".
yajero min tambayar.
na gyaÉ—a kai na nace
"Eh zan gane ai a bakin ruwan mukafi daÉ—e wa ma".
nan nabasu labarin lokacin da ruwan yacika kogin ya mamaye ko ina bayan wucewar sa muka dawo gurin zaman mu da yan da akayi har nasa mi duwatsun.
cikin matukar mamaki suka haÉ—a baki wajen faÉ—ar
"Ikon Allah Allah buwayi gagara misali".
Bappa yace
"Wannan dutse da kike gani kuma kike masa kallon abun wasa dukiya ne arziki ne, kwalli É—ayan sa ma kaÉ—ai ya ishe ki rayuwar duniya ingantacciya mai tsafta,
hakika Allah yayi miki ni'imar da bakowa yake masa ba sai wan da yaso".
kallonsu kawai nake taya za'ayi ace dutse shine kuÉ—i nace
"Bappa baka gansu da kyau bane fararen duwatsu ne fa".
dun kule su yayi a hannunsa gamgam yace
"Da ma tun zamanin iyaye da kakanni sunsha faÉ—an cewa acikin yankin nan akwai arziki muna da arziki sai dai arzikin sai mai rabo yake iya ganin sa har ya same sa,tabbas kun tabbata ke da Æ´aÆ´an ki ku masu rabo ne,
wannan duwatsun da kike gane sune *LU'ULU'U*.......!!!!!!!!!★

Mommyn Twins ce

🌺HAMDAH🌺

t NA
*RASHEEDA S DIRECTOR*

_BOOK TWO_

*Sakon ta'aziyya gareki Aysha Aliyu Garkuwa*
*Tabbas babu abun da yakai rashin hamaifiya zafi da kunci😭 Allah yajikan Mahaifiyar ki yayi mata rahama ya gafarta mata yasa Aljanna ce makomar ta da sauran namu iyayen baki ɗaya😭 ku da tabari ya baku hakurin rashi ya sanya albarka a rayuwar ku da zakuyi shi bayan rashin UWA!!*.
*Sannu Aunty Aysha rashin mahaifiya akwai zafi Allah yabaku ikon cin jarabawar da yayi muku*😭👏🏻
Chapter 24 · 0% Book details