← Book details Hamdah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 34

Sashe 26

Hamdah Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

washegari da rana Mahmud ya iso rugar, yayi mamaki da jinjina lamarin ta yadda nayi nasamo Diamond masu yawa irin haka,
yayi murna da godiya wa Allah da samun wannan É—inbin dukiyar,yakuma ji daÉ—in da abun ya shigo acikin gidan su, dan kuwa ba shakka hakan abun alfahari ne.
bayan ya huta yaci abinci,zaune muke a tsakar gida Bappa da Mahmoud suna zaune kan taburma guda yayin da ni da Inna wuro Mero Nasmah muke zaune kan taburma guda,
Naseem kam na can kan kafar Bappa ya like masa sai tsalle yake a jikin sa.
ina zaune shiru duk maganar da Mahmud da Bappa su ke da tsare-tsaren da Mahmud yake na yan da lamarin zai tafi cikin sauki,
ban iya cewa komai jikina yayi sanyi natuno wani sashi a rayuwa ta, tun isowar Mahmud da yayi sallama cikin gidan inadaga ɗaki sai da naji gaban kirjina ya yabuga, jikina sai ya kama ɓari muryar sa tamkar muryar Abba har na fara tunanin ko Abba ne sai da naji Mero tana faɗin
Oyoyo Yaya Mahmoud.
ko yanzu da muke zaune ganin fuskar sa shima ya sani shiga wata yanayin, kamannin sa irin na Abba yana matukar kama da Abba.
sai dai shi baikai Abba girma ba shekarun sa bazai wuce 38 zuwa 40 ba,
kira ce tashigo wayar sa da sauri ya É—aga kiran kana yakara wayar a kunnen sa "Ok godiya nake".
abun da yafaÉ—a kenan tare da sauke wayar.
maganar sa naji a sama yana faÉ—in
"Tun jiya na nimi ganawa da gwamnatin jihar nan, gashi da ikon Allah cikin sauki an bani tabbacin ganawa da shi cikin sauki in sha Allah, wa gwamnati za'a siyar domin samun cigaban kasa".
ya mike tsaye yana cigaba da faÉ—in
"Bappa mu hanzar ta."
tun kan ya rufa baki Bappa yamike yana faÉ—in
"masha Allah hakan yayi".
bukkar sa yashiga zuwa can yafito yana gyara babbar rigar da yasa ka kan kayan jikin sa,tuni Mahmud yayi waje Bappa na fita ya shige mota suka É—au hanya...
kwance nake a kan gado Nasmah da Naseem suna gefe na sai wasa suke,Mero ta shigo nace ta É—auke su sufita dan kaina ciwo yake min sai kuma dami na da surutun su suke, suna fita na gyara kwanciya ta,gaba É—aya yau tunanin gida da ya dame ni tun ganin da nayiwa Mahmoud tunanin family na ya addabe ni,ina kwance shiru a haka har bacci ya É—auke ni...

Bappa sun isa cikin Adamawa batare da ɓata lokaci ba suka sami ganawa da Gwamnan jihar su, saboda muhimmin abun da ke tafe da su.
bayan sun gabatar da abin da ke tafe dasu, shi kansa Gwamnan yayi mamakin yawan Diamond É—in, yace gaskiya wannan Daimond É—in kam sai dai a jingina da shugaban kasa. sabo da babu kuÉ—in da zai iya canza wannan Diamond É—in a fadar jahar.
batare da ɓata lokaci ba yayi magana da fadar shugaban kasar Nigeria, kana ya haɗa su da wasu jagororin da zasu tafi tare, sannan yace dole sai sun tafi da wanda yasamo Diamond ɗin sabo da za'a iya bukatar hakan acan fadar shugaban kasar.
da yamma lis suka baro cikin Adamawa suka koma rugarsu da jagororin da aka haÉ—a su da su, da sojoji mota guda waÉ—an da zasuyi musu rakiya, dan acewar gwamnar komawar su cikin daji da wannan abu yana da haÉ—ari sosai dole sai an haÉ—asu da jami'an tsaro.
mota uku ne motar Mahmoud sai na jagororin da aka haÉ—a su dasu motar su guda sai motar sojojin.
motar su Mahmoud ne a gaba na jogororin a tsakiya na sojojin na biye da su...
bayan sallar Isha
muna zaune a tsakar gida muka jiyo jiniyar sojoji,
Ido Inna wuro ta waro tare da faÉ—in,
"Sojoji kuma shanun wa aka kuma kaÉ—awa yau?".
batakai ga rufe bakin taba muka ji jiniyar ya tsaya daf kofar ida,

Mero tace "Inna wuro anan suka tsaya".
tafaÉ—a tana nuna kofar gida, ganin yan da sukabi suka tsorata nima sai na fara shiga yanayin da suke ciki,
har kuma lokacin jiniyar na tashi, nace
"Eh..Eh akofar gida suke".
duk mukayi jigum idanun mu a kofar gida tsoro fal zuciyoyin mu.
bayan haka dakamar minti 15 muka jiyo sallamar su Bappa duk muka mike tsaye tare da amsa sallamar.
suka karaso ciki,tun kan su zauna Inna wuro tace
"Malam lafiya da sojoji a kofar gida?".
ganin duk hankulan mu a tashe yasa Bappa faÉ—in
"Babu komai fa rakomu sukayi domin su bamu tsaro sabo da abun da muke tare da shi".
tsaguwar sa ya gyara kana yace
"Duk ku zauna". nan muka É—an sami kwarin guiwa muka koma mazau nin mu,
Mahmoud yacewa Mero ta tashi tazuba ruwa acikin bototi, tana zubawa ta mika masa yakarɓa yafita,yakai wa ba'in da suke tare da su a waje.
Bappa ya zauna kan taburman sa da Inna wuro ke shinfiÉ—a masa duk dare a bakin kofar sa kana a nutse yashiga faÉ—a mana yan da sukayi da gwamna kana ya É—aura da faÉ—in
"Sai ki shirya tun yau dan gobe idan Allah ya kai mu da sassafe zamu tafi".
kai na gyaÉ—a cike da mamakin jin abun da Bappa ya faÉ—a.
Inna wuro tace
"Ikon Allah to Allah ya kai mu sai ki tashi ki kimsa".
to kawai nace dan ni ban san me zan kimsan ba, ba kaya nake da shi ba bare na ce shi zan kimsan, su Naseem ma ba kayan suke dashi ba sai kala bibbiyun da Bappa ya É—in kamusu.
washegari da sassafe Inna wuro ta tasheni,tace naje nayi wanka taÉ—aga su Nasmah taje tayi musu wanka,
ta shirya su, ina fita ta bani wani kayan ta mai É—an haske na saka duk da kayan yaÉ—an min girma,
Mahmud yashigo yace nayi sauri ni ake jira, da sauri na karasa saka hijabi wan da shima ita ta bani,
Inna wuro da Mero suka rako ni har waje,tuni kowa ya shige mota sojojin nan suna saman motar su sun tasa bindigogin su gaba, da hannu Mahmud yayi min alama da inzo, na karaso gun motar sa na buÉ—e gidan baya muka shiga ni da Nasmah, Naseem kam tun da yaga Bappa yarika mika hannu yana tsalle Bappa yace a kawo shi..
motar sojojin a gaba yayin da motar mu ke biye da shi sai na jagororin
a baya..
nan muka ɗauki hanyar birnin tarayya Abuja....★

muna isa garin Abuja wani kayataccen masauki aka wuce da mu, nan Mahmoud ke faÉ—a wa Bappa,
an tabadar da masaukin domin mu ne, É—akina ni da su Nasmah da ban, É—akin Bappa da ban sai na Mahmoud É—in,sai kuma na jagororin da muka taho da su,
sojojin kam suna cin abinci suka juya suka É—au hanyar Adamawa,dan da ma suma rakiyar sukayi mana yanzu kuma kulawar mu yafita a hannunsu yadawo hannun wasu hukumar da muka tarar da su a nan.
a gayiye na zauna bakin gado Naseem da Nasmah suna zaune tsakiyar gadon sunata wasan su.
bin lafiyayy É—akin nayi da kallo, numfashi na sauke ashe dai zan sake gani na cikin É—aki irin wannan, dan ni na fidda sammanin hakan arayuwa ta mai cike da tarin kaddara da jarabta.
kasan cewar mun isa ana kirana sallar magriba, dan da muka iso sai da muka tsaya a wani guri naga jagororin da aka haɗo mu da su, suka tsaya yin magana da wasu, mun ɓata lokaci a gurin kafin muka taho nan.
Chapter 26 · 0% Book details