← Book details Hamdah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 34

Sashe 29

Hamdah Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

A sannu narika taka matattakalar jirgin, har muka shige ciki,
Kujerar da ke kusa da window wani mutum ya nuna min yace na zauna anan.
kana ya É—ago su Nasmah da Naseem ya É—aurasu kan kujerar da ke gefe na,
ya janyo sit belt ya sarkafe su da shi.
tun shigar mu cikin jirgin hankalin jamar cikin da ma'aikatan jirgin duk yadawo kaina,
sai nuna ni suke suna magana wan da ni bajin me suke faÉ—a nake ba,
sai dai yanzu na fara tsarguwa da yawan kallo da nuna ni da mutanen suke.
ina zaune shiru sai raba ido nake a cikin jirgin, Allah mai iko wai yau nice gani a cikin jirgi wan da da sai dai na hangosa daga nesa in muka yiwa su Abbu rakiya in zasu tafi Saudi.
sai gashi yau gani a cikin sa ko ina za'a kuma kai mu yau oho, ina kuma za'ayi da mu acikin jirgi?.
Kamar Bappa yasan abun da nake ta sakawa cikin zuciya ta,ya mike daga kan kujerar da yake yatoho in da nake, da ƙagan sa kasan yana cikin matsanancin farin ciki, bashi kaɗai ba hatta Mahmoud tun ɗazu bakin su yakasa rufuwa, yakaraso in da nake cikin matukar farin cikin da yagama mamaye ilahirin zuciyar sa
Yace "HAMDAH Allah yayi miki albarka Allah yadaÉ—a karawa rayuwar ki albarka, hakika rayuwar ki mai cike da É—inbin albarka ne,
yau gashi ta sana diyyar ki zamu tafi kasa mai sarki".
Amin nace cikin rashin fahimtar in da maganar Bappa yadosa,
"Kasa mai sarki?".
nayi maganar da fuskar tambaya da kuma rashin fahimta.
da sauri Bappa ya gyaÉ—a kansa kana yace
"Eh kasa mai sarki zamuje Saudi zamu tafi yau da yardar Allah, domin kuwa shugaban kasa yace can zamuje a canza yagama duk wani abun da yakama ta duk wani abun da ya dace adalin shugaba nagari ya gudanar da shi,
zamuje can a can zamuje a canza, do min yace a can za'a fi canza shi da farashi da daraja mai kima a can sunfi mu sanin daraja da kimar Lu'ulu'u, bugu da kari kuma yace a nan babu isasshen kuÉ—in da zai canza waÉ—an nan Lu'ulu'u'n duka, dan a yanzu tsaron kasa ya sa a gaba,
Shi yasa yayi magana da masarautar Saudiyya can za a kai musu su zasu canza insha'allahu, Allah dai yayi miki albarka yakarawa rayuwar ki albarka da ke da Æ´aÆ´an ki baki É—aya".
Bappa yarika zabgamin addu'a da samin albarka.

Mahmoud daga can yana zaune sai washe baki yake,
Ido na waro tare da furta
"Bappa Saudi fa Saudiyya zamuje yanzu?".
nayi maganar cikin muryar dariya mai bayyana matukar farin ciki,
Bappa kam kai yashiga gyaÉ—a wa yana faÉ—in
"In sha Allahu".
Wani irin matsanancin farin ciki ne ya lulluɓe ni wai nice zanje Saudi nice a jirgi da zai kaini Saudi.
har lokacin Bappa na tsaye yanata zabgamin addu'a da sanya albarka har sai da ma'aikatan jirgin suka ce yazo ya zauna lokacin tashi yayi.
nan ne ya koma mazaunin sa.
Nan na'ura tafara bada sanarwar jirgi zai tashi kowa ya kimsa.
duban Naseem da Nasmah nayi tare da gyara musu zaman su murmushi nayi ina faÉ—in
"Nasmah Naseem kunsan in da zamuje kuwa yara makka zamu".
nafaÉ—a ina dariya suma baki suka washe.
Batare da ɓata lokaci ba jirgi ya ɗaga da mu,
cikin yardar Allah da buwayar sa.
Idanuna na lumshe tare da kuma buÉ—e wa ina yiwa Ubangiji buwayi gagara misali godiya, lokacin da na ganmu muna keta hazo, tabbas Allah mabuwayi ne kuma mai izza,
sai baza idanuna nake cikin gajimare ina kallon wasu da ke cikin jirgin har sun sami da mar yin bacci,
ni kam zunzurutun farin ciki da murna ko ɗigon bacci bana jin sa a cikin idona.....★

Da misalin ƙarfe 3:15 jirgin mu yasauka a kasar Saudi wayyo Allah, zo kuga farin ciki da murna bakina kasa rufuwa yayi daga Ni har su Bappa bakin ko wannen mu a buɗe yake.
bayan saukar jirgin da kamar minti 15 nan aka umurci fasinjoji da su sauka, bayan murfin jirgin ta buÉ—e da kanta.
A hankali na mike ina kokarin cire belt É—in jikin su Nasmah,
da sauri wani ya iso in da muke cikin hanzari yayi abun da nake shirin yi tare da É—aukar Naseem, daga can wani shima ya karaso da sauri ya É—auki Nasmah kana sukayi gaba nikuma na bisu a baya.
su Bappa suna gaban mu, tunkan mukarasa sauka daga saman matattakalar jirgin sojojin kasar Saudi suka buÉ—e murfin motacin su da ke pake a cikin airport É—in.
Lumsh idanuna nayi lokacin da na sauke fafafuna kan kasar Saudi tare da yiwa Ubangiji tasbihi,
a ɓangaren su Bappa ma haka abin yake Bappa kam har sai da ya ɗaga hannunsa sama yanayiwa Ubangiji da ya halicci wannan sarkakakkiyar kasar godiya da ya nufesa da zuwa cikin sa.
daga can sojojin kasar saudi sanye da uniform É—in su, suna tsaye jikin motocin su,
tun kan mukarasa sauka sukayi hanzarin nufo in da muke,
Nan suka samu a gaba mu da jagororin da shugaban kasar mu yahaÉ—o mu dasu,
sauran sojojin da ke tsaye jikin motar sukayi hanzarin buÉ—e mana mota, muna karaso wa muka shige ciki, yayin da Ni Bappa Mahmoud Naseem Naseem, muke mota guda sauran motocin kuma jagororin mu suka shige ciki.
batare da ɓata lokaci ba sukaja motar mukayi gaba,
Ido nayi ta bazawa kan shahararren titin da muke tafiya kansa da kayatattun guraren da muketa wucewa,
Kai jama'a na rantse babu kasar da takai Saudi kyau duk tafiye-tafiyen ka duk wani yawon buÉ—e idon ka zuwa wasu kasashe daban-daban har in bakaje Saudi ba,
to Tabbas bakayi kallo ba, baka kuma baiwa idanunka abinci mai kyau ba.....

Wani kayataccen masauki aka sauke mu,
bayan munci munsha munyi su wanka, Bappa yace muje masallaci muyi sallah,
wasu sojoji uku sukayi mana rakiya zuwa Masallaci sai bayan sallar isha muka dawo masaukin mu a gajiye dan munyi sallole kam ba iyaka, tun a cikin masallaci su Naseem sukayi bacci,
a cikin parlour sojojin suka dire su saman kujera,
É—aukar Nasmah nayi na nufi É—akin da a ka sauke ni É—azu,
shin fiÉ—a Nasmah da ke hannuna nayi kan lafiyayyen gadon, da É—an sauri na juyo jin an turo kofa,
Mahmoud ne rike da Naseem, gefe na ja tare da soma cirewa Nasmah takalmin kafarta, ya karaso bakin gadon ya shin fiÉ—a shi,
Ina É—agowa muka haÉ—a ido da shi, saurin kawar da kaina nayi,na lura tun a mota yake ta satar kallo na sai ya rika niman yimin magana musamman idan muna hira da Bappa sai ya rika saba ki ciki, yana fara sa baki cikin maganar ni kuma zanyi shiru haka kawai nake jin mogun nauyin sa,
gefen sa na bi ina kokarin wuce sa yace
"Shima kicire masa takalmin zai masa nauyi ai".
yafaÉ—a tare da nufar kofa yafita, a sannu na isa na cire masa takalmin, zubewa nayi a gefen su dan bacci ne tam ido na..
Chapter 29 · 0% Book details