← Book details Hamdah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 34

Sashe 19

Hamdah Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kamar mahaukata duk kayan jikin mu yayi matukar datti bazaka iya shaida wani irin kalar kaya bane a jikin mu,sabo da tsabar datti,
nawa kamma duk ya yayyage daga kasa.
tun wannan mangoron da muka sha bamu kuma samun wani abun ciba a hanya ba sai da muka kuma tafiyar kwana biyu,
daga can da nisa sosai na hangi wani katon dutsai mai girma sosai gefe da dutsai É—in wasu bishiyoyi ne ajere,
daga in da nake tsaye ina jiyo wani irin sauti mai kara da kugi mai karfi sosai duk da kuwa ina juyo sa daga can da nesa,
cikin sauri da fatan Allah yasa bishiyar abun cine nakara sauri duk da azaba da zugin da kafafuna keyi,
nanufi gurin dutsai da bishiyoyin nan suke.
duk da dai zuciya ta ciki da zullumi da tsoron jin ina daɗa matso in da kara da ƙugi wato irin sautin gudun ruwa yake,
amma ban fasa nufar in da bishiyoyi da katuwar dutsai É—in nan suke ba,
kuma nan nake jiyo kugi irin kugi mai amon sauti irin na ruwa mai karfi sosai É—in nan.
a sannu narika tafiya ina yi ina huta wa har na iso kusa da dutsai da bishiyoyin nan,
wani irin juyawa da tsara wa kaina yayi hango wani katon kogi mai girman gaske,
cikin É—an É—ar-É—ar na karaso jikin dutsai É—inan wan da can gaban sa kuma katon ruwa ne yana gudu da sautin kugi mai karfin gaske.
koton kogi ne mai girman gaske ko karshen gaɓar sa bana gani, ruwane mai girman gaske ko a TV ban taɓa ganin irin wannan ruwa mai girman gaske haka ba.
gefe da dutsai É—in kuwa wasu bishiyoyi ne lif-lif-lif masu kyau sai dai da yawan bishiyoyin ban san ko bishyar menene bane gasunan da tarin Æ´aÆ´a a jikin su wasu jajaye wasu koraye,
daga cikin bishiyoyin kuwa akwai na mangoro gwaiba dabino kwara kwakwa da kuma tupa,
gasunan kasa-kasa. gindin bishiyoyin kuwa yashine fari soll amalale agurin kamar an share gurin babu ko datti har zuwa bakin gaɓar ruwan.
daga gurin bishiyoyin zuwa bakin gaɓar ruwan da ɗan tazara kaɗan,
kafin ai nihin babban ruwan akwai wani ruwa a É—an gaban bishiyoyin sai dai shi É—an kaÉ—an ne da alama dai ruwan idan yayi yawa yana haurowa har gurin idan ya koma kuma sai ragowar ya tsaya a É—an wannan ramin.
ruwan fari soll kamar babban ruwan kogin nan da yake gudu....

A hankali natako zuwa gun yashin nan wato karkashin bishiyoyin nan,
na sauke su Naseem na zaunar da su,
da sauri cikin jin matsananciyar kishin ruwa na nufi in da wannan ruwa É—an kaÉ—an É—in yake na sun kuya na saka hannuna narika É—iba ina sha,
sai da nasha na koshi,kana narika É—ibawa da hannuna ina zuwa in da su Nasmah suke na basu suka rika sha,
haka narika kai wa da komowa ina É—iba ruwan a hannuna ina kai musu suna sha,
haka narika yi har sai da na tabbatar da sun koshi,kafin na kyale su.
na koma gurin ruwan nayi al'wala na dawo in da suke nayi sallar azahar da nake tunani yanzu lokacin sa yayi.
ina idarwa na mike lokacin rana yafito sosai na ɗago Naseem na tuɓe masa kayan jikin sa da yayi wani irin datti dattin har ya wuci misali,
na É—auko shi muka taho bakin wannan ruwan da muka sha nakuma yi al'wala da shi, na saka hannu cikin ruwan kasan cewar rana yafito hakan yasa ruwan yaÉ—an yi É—umi sai narika É—iba ina wanke masa jikin sa na wanke shi sosai kana na É—ago shi na goyashi,
na ɗauko Nasmah ma itama na tuɓe mata kayan ta itama da yayi matukar datti kamar bana ɗan adam ba,
na wanke mata jikin ta sosai kana na rungume ta muka koma gindin bishiyoyin,
nan da nan kuwa sukayi bacci ina zaune rungume da su,tabbas datti wani sashi ne mai hana É—an adam sakewa da jin daÉ—i É—an rage musu dattin jikin su nayi sai gashi sunyi bacci cikin kankanin lokaci.
É—ankwalin kai na, na cire na shin fiÉ—a a kasa kana na kwantar da Nasmah dake hannuna,
sannan na kunce Naseem na shinfiÉ—a zanin goyon su na kwantar dashi sannan na É—ago Nasmah a kan É—ankwali na na mai data kan zanin goyon kusa da shi,
hijabina na cire na rufe su da shi kana na É—auki É—an kwali na na É—aura.
gurin ruwan na koma na wanke musu kayan da na tuɓe musu na shanya kan yashin gurin, kana na tuɓe kaya na na wanke jikina duk da ba soso ba sabulu amma naji da ɗin saka ruwan a jikina.
na wanke kayan su da na tuɓe musu na shan ya kan yashi.
sannan
na dawo in da suke na kwanta a gefen su wani nannauyar bacci yaÉ—au keni.
bacci ne mai nauyin gaske yaÉ—auke mu dukan mu ban farka ba sai can dadaÉ—e wa koda na tashi na fahimci cewa yamma tayi sosai dan guri yayi duhu,
al'wala nayi nazo na gabatar da sallar la'asar,
ko da na idar tagumi nayi a gaban su na zuba musu ido,
sun rame sun dishe wagasu kananun kuraje da suka fito musu duk jiki,
ido na rumtse yayin da tausayin su ke daɗa rasa ni har sai da wasu zafafan ƙwalla suka zubo min batare da nasan da fitar suba.
nakai hannu nashare ina cigaba da kallon su a raina nake faÉ—in
"Ya Allah ka tseratar da su ka fidda su a cikin wannan kungurmin daji"...

A hankali na mike tsaye jin cikina na murÉ—an yunwa na sinko Æ´aÆ´an itatuwa da yawa wanda na sani har da wan da bansan su ba duk wan da na sinko na gusura najisa da zaki sai na kama ci,
nan su Nasmah suka farka da kuka na É—ago su na basu abincin su suka sha wanda sai dai susha ne kawai bawai kodun ya koshar da su ba.
suna rungume a jikina a haka guri yarufa sosai lokacin tuni sun koma bacci sai nayi musu addu'a na kwantar da su naje nayi al'wala bayan na idar da sallar magriba da isha sai na kwanta gefen su.
Washegari naji daÉ—in bacci a gurin sosai bakamar na sauran kwanakin da mukayi a cikin dajin ba,tabbas nan gurin da muke zaune wata rahama ce dan kuwa anan muna samun ruwan sha da Æ´aÆ´an itatuwan da zance,da ruwan da zanyiwa Æ´aÆ´ana wanka da kuma ni kaina duk da bada soso da sabulu muke yin wankan ba.
da waÉ—an nan abubuwan mukayi ta rayuwa a gefen ruwa har na tsawon wata guda.
gurin ya zame mana tamkar gida kuma É—aki,
a gurin na kan iya ajiye su na ɗan zaga ta bayan bishiyoyin nan na sinko mana wasu kalar kayan itatuwan nakawo mana dan yanzu har su Naseem ma ci suke mu samman abu mai ɗan laushi....★

Zaune muke bayan na musu wanka suna kan kafata ina ta yi musu wasa sai ɓarkewa da dariya suke,
cikin dabara na sauke su namike naje nayi wanka kayan su dana wanke musu É—azu da nayi musu wanka nashan ya kan yashi yabushe na É—auko nazo na sa musu.
ina zaune a gefen su Naseem ya lankwasa kafar sa ya rarrafo yazo in da nake,
cikin tsananin farin cikin ganin yau yaron ya fara rarrafe nashafa kansa ina dariya da faÉ—in
"Iye lallai Naseem wato kayi wa Nasmah wayo ko kai ka fara iya zama shine kuma zaka riga ta iya rarrafe ko,
amma dai zaka barta ta iya da wuri itama ko?".
baki yawashe kamar yasan abun da nake faÉ—a,
na kama kuma tun Nasmah ina faÉ—in
"Kema ki dake kinji kada yarika yi miki wayo da yawa".
nayi maganar cikin shauki,
itama dariya ta saka min duk na rungume su ina dariya,
a take kuma naji wani kuka yazo min sai kuma na fashe da kukan.....
cikin Æ´ar dar Allah bayan sati É—aya kuwa Nasmah itama ta fara rarrafe.
tun da naga rarrafen su yafara yin kwari, sai bana yin nesa da su dan gudun kada su rarrafa suje su shiga cikin ruwan nan idan zan je tsinko mana abun da zamuci sai na É—auke su mu tafi tare,
ko bacci nake ji har idan idon su biyu bana yar da natafi na barsu su idan su biyu,
dan duk lokacin da naje na musu wanka Naseem yarika zillewa yana son shiga ruwan yarika bori da shure kafafu wai sai dai na barshi yashiga ruwan,
shi yasa nake jin tsoro kada wata rana nayi bacci yace zai je yashiga ruwan bugu da kari ma zai iya tunkarar babban kogin nan,
to haka zan yi ta zaman gadin su har sai sunyi bacci kafin nima nayi.....
Chapter 19 · 0% Book details