← Book details Hamdah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 34

Sashe 4

Hamdah Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ido na zuba wa hanyar da bansan na wani gari bane,duk tafiyar da motar yake gani nake baya sauri,
munyi tafiyar da yakai na a wa 2,wata matar da take gefe na tabuÉ—e murya tace
"Direba nakusa sauka ni a Narkuta zan sauka".
direban ya amsa mata da to.
tafiya kaÉ—an muka kara muka iso wani gari mai kyau da tsaruwa a dai-dai farkon shiga garin motar ta tsaya direban yace
"Mun iso masu sauka a Narkuta".
kasan cewar Ni ina ta bakin kofa ne yasa dole sai da na sauka kafin matar tafita,
maganar direban naji a sama
"Ƴan mata kema a nan zaki sauka ne".
firgigit na dawo daga tunani da natafi sai kawai na sinci kai na da gyaÉ—a masa kai,
"No wahala"
yafaÉ—a tare da jan motar sa yayi gaba.

ido na baza kan titin kowa na ta harkokin gaban sa,
a sannu na masa gefe kan wani kwalbati da ya kasan ce hanyar shiga wani layi na zau na, tare da aje akwati na a gabana,
yayin da masu a dai-dai ta da mashina suke ta tsayuwa suna tan bayana ina zani,wasu nace musu babu wasu kuma nayi musu shiru.
najima sosai zaune a gurin.
Har guri yafara rufawa yayin da ababen hawa suka yawaita kowa yana kokarin konawa gida,
Ina nan zaune a kan kwalbatin,
shafa cikina da naji yana É—an motsa wa nayi yanzu kam naji ina jin yunwa akasin É—azu da banajin ko É—igon yunwa,duk da wunin yau bansa ko ruwa a baki na ba, dan ko breakfast banyi ba.
a hankali na mike nanufi gurin wata mai sai da abinci da nake hango ta can gefen titin,kuÉ—i na mika mata nace
"Abani abinci".
sai kuma na dubawa kuÉ—in da nake mika mata ido da mamaki ganin naira É—ari biyu ne bayan nasan dubu É—aya da É—ari biyu ne a hannuna,
waige-waigen gefe da gefe na nayi ko dubu É—ayan yafaÉ—i kasa ne amma babu ko alamar sa.
maganar
matar naji tana faÉ—in
"Babu abincin 200".
nace "To abani drink".
ta miko min gora na amsa na juya a hankali hanyar da na bi nabaza ido ko zanga kuÉ—in amma har na'isa in da akwatina yake babu alamar sa,
kurɓa uku zuwa huɗu nayi wa drink ɗin sai naji cikina na murɗa ni sai na rufe gorar,
A sannu na É—ago jin karar mota ta tsaya daf da Ni dai-dai lokacin aka zuge glass É—in motar kasa, wani matashi ne zaune a cikin motar sai busa sigari yake,yayin da wani ke zaune a gefen sa,kai na na kawar da sauri jin hayakin sigarin yana isoni, matashin ya dubi abokin tafiyar nasa yace
"Maye wannan fa ta haÉ—u musala zata rage mana dare sosai".
Kai ya gyaÉ—a cikin cakewa da kayan mayen da yake ta shaka.
matashin ya dubeni yace
"Ya Æ´anmata shigo muje mana mubaki masau ki muhuta kihuta sosai".
yafaɗa yana latso laɓɓan sa,
nan take maganganu Inna da tarika yimin lokacin tana kwance a gadon asibiti suka fara yimin yawo a ƙwaƙwalwa ta.
rumtse idonuna nayi da karfi,sai na
kuma kawar da kai na batare da nako kalle in da suke ba bare na furta wani abun.
É—ayan dake zaune gefen mai zaman banza yaleko tare da É—aga murya yace
"Zazzafa ce fa nawa za'a biya ki?".
nan ma banko juyo ba dan na fahimci Æ´an iska ne inajin É—ayan yana faÉ—in
"Muje gaba akwai irin su, biyu zamu É—iba dan mu huta sosai".
É—ayan kuma yace
"Ta haÉ—u fa duk da tana cikin hijabi".
"Shiyasa take taja mana aji manya masu zaren take so muje kawai".
haka sukayi ta magan ganunsu sukaja motar su sukayi gaba.
numfashi na sauke tare da cigaba da ambaton sunan Allah azuciya ta da nake,
tafiyar su dakamar 5mn wata mota takuma tsayuwa gefe na wannan karon sai da naji gaban kirji na ya faÉ—i,da sauri na juyo jin muryar wan da yake cikin matar
"Shigo na sauke ki a gida mana da alama dai kin rasa abun hawa ne".
saurayi ne shima sai dai baiyi kama da irin waÉ—an can da suka wucen ba yana zaune cikin kamala, murmushi yayi min kana yakuma faÉ—in
"Naga kin jima zaune a nan da alama dai jira kike azo daga gida a É—auke ki in bazaki damu ba muje na sau keki a gidan".
da sauri na girgiza kaina tare da faÉ—in
"A'a Nagode kaje kawai".
kai ya jinjina yadube ni da kyau tare da faÉ—in
"To in ma bazaki shiga motata ba to ina mai baki shawara daki nimi mai abun hawa kihau ki tafi gida".
murmushi yayi cikin maganar da yake kana yaci gaba
"Duk wani wanda yagan ki zaune a nan to zai yi miki kallo irin kallon da waÉ—an can samarin da suka yi miki yanzu suka wuce,gashi dai duk mai tunani idan ya ganki bakiyi kama da irin mata masu tallen kansu ba duk da dai basa da kama,
bai kamata kici gaba da jira a kan wannan hanyar ba dan yana da haÉ—ari sosai,
akwai matasa marasa É—a'a su basa jiran amincewar mace ko kotaso ko kar taso zasu É—auke ta da karfi su kai ta É—aki su kulle idan suka gama kwanakin da zasu yi dake suje su yasar da ke,a irin wannan lokaci suke fitowa, babu kuma wan da ya isa ya dakatar da su domin Æ´aÆ´an manya ne,zai fi miki kyau kitari abin hawa kitafi gida".
ido na waro ina kallon sa har yakai karshen maganar yayin da tsoro ya lulluɓeni sai nashiga gyaɗa masa masa kai,shiko murmushi yakuma kana yace
"Ko za'a bani aron number?".
mikewa tsaye nayi
cike da jin tsoron da ya É—arsa min a zuciya na bashi baya ina ta É—an kalle-kalle.
ina jin sa yakuma maimaita tan bayar sa ganin bani da niyyar amsa shi sai yaja motar sa yayi gaba.

ido na kurawa cikin layin da nake tsaye a mashigar sa, matasa da magidan ta kowa yana ta haramar tafiya masallaci sallar magriba. Da sauri na sunkuya na janyo akwati na nasoma takawa cikin layin da sauri sosai dan ba karamin tsorata nayi da jin abun da mutumin nan yafaÉ—a min ba,sai dai ina soma tafiyar naji cikina yayi min wani irin murÉ—a yayin da kai na yake mugun sara min.
Na yi tafiya mai É—an nisa sai na zauna kan dakalin kofar wani gida,tare da tafe kai na dake matsa nancin tsaramin, da hannuna É—aya É—aya hannun kuma na dafe cikina, tausayin kai na ya kamani sai kawai na fashe da kuka mara sauti.
cikin muryar kuka nake faÉ—in
"Wayyo Allah cikina kai na wayyo Allah na, innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un²".
wani sabon kuka ne yakuma zuwa min Allah sarki Inna banki a yanzu Allah ya É—auki raina kamar yan da yaÉ—auki nata ba yafiye min wan nan rayuwar.

nayima ina kuka mai matukar kona zuciya kukun da naɗau lokaci mai tsawo batare da nasan lokacin yakure har haka ba,guri yayi shiru bakajin motsin komai sai haushin karnuka da kukan wasu tsuntsaye, na rakuɓe jikin garo na cusa fuskata sakankanin cinyoyi na,an ce bacci ɓarawo ne to ni dai na tabbata duk iya satan sa bazai iya sace ni a wannan irin lokacin ba,ta ya zai sami narasar saceni bayan ina tangare a dandamalin guri wan da a iya ƴan shekaru na ban taɓa mafarkin kasan tuwa a irin hakaba,ban taɓa rayuwa cikin bakin duhu irin haka ba,ina zaune a haka gari yawaye..
nayi al'wala a panpon da ke jikin gidan da nakwana a kofar gidan nayi sallah.
Koda gari yayi haske jama'a suka fara zirga-zirga a kan hanyar duk wan da yazo wucewa sai ya kalleni ganin na zame wa mutane abun kallo dai na mike naja akwati na,
a sannu narika kusawa cikin unguwar haka na rika zaga cikin unguwar idan na gaji sai na sami guri na zauna in na huta sai na mike nacigaba da tafiyar da ban san in da zani ba.
ranar wuni zubur nayi ina haka yunwa kishin ruwa zafin rana sune abokan rayuwata...
Chapter 4 · 0% Book details