← Book details Hamdah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 34

Sashe 25

Hamdah Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

" *LU'ULU'U?*" nafaɗa ina duban Bappa da mamaki kana nace "Bappa Diamond ƙenan fa?".
yace "Eh shine kwarai shine wannan".
kai na jinjina cike da matukar mamaki,
tabbas naji a na faɗan Lu'ulu'u amma ban taɓa ganin sa ba ko a hoto ne bansan ya kalar sa yake ba,
kuma tun da nake tunanin abun bai taɓa zuwa min ƙwaƙwalwa ta bare har na ƙiyasta kamannin sa acikin zuciya ta ba,
ni dai naji ana faÉ—ar sunan sa Diamond wato Lu'ulu'u,sai dai kaman ninsa kam sam ban sani ba.
baki na washe tare da mika hannu ina faÉ—in
"La ashe dama wannan shine Diamond ɗin da ake faɗar nan ashe akwai a Nigeria ma? in sake ganin su Bappa." nafaɗa ina kokarin karɓa a hannun sa.
da sauri Bappa ya daÉ—a dun kule su a hannunsa yana faÉ—in
"To ai gashi kin gani ai mu arzikin da Allah yayi mana a Nigeria ma wata kasar bata samu kwatankwacin irin sa ba, ke zaki bada shaidar haka tun da gashi kin samo da hannun ki, wannan ba abun wasa bane barsu a hannuna kawai".
baki na washe nace
"Ashe Diamond É—in haka yake".
Gefe da gefen sa Bappa ya kalla tare da like kofar gida kana ya juyo ya dubi Inna wuro yace
"Da muke maganar nan Allah sa dai ba wanda yake kusa ko kin ki motsi alamar mutum a kusa?".
É—an shiru Inna wuro tayi alamun nazari kana tace
"A'a kam banji alamun wani a kusa ba".
Kai Bappa ya jinjina sannan ya dube ni yace
"Kikace zaki gane ruwan idan muka je?". nace
"Eh zan gane".
da sauri ya juya yashige bokkan sa yayi musu kyakkyawar ɓuya kana yafito,
ya dubi Inna wuro da muke tsaye har lokacin yace
Kada ta kuskura tafita kuma kada tabar wani ya shigo gidan.
tace To,kana ta ja hannun Naseem da Nasmah suka zauna kan taburman dake sakar gidan,tana ta jan su da wasa har muka fita basu sani ba...

Muna fita yakira wo waÉ—annan matasan da suke yi masa kiwon suka taho da amalanken shanu Bappa yace nahau.
kana ya dube Ni yace "Ta'ina zamubi?".
nan nashi kwatanta musu hanyar da muka bi ranar da na biyo shanun muka shigo cikin rugar.
ina kan amalanken su suna tafiya a kasa nan muka É—au hanya.
mukayi ta tafiya tafiya mai nisa kafin muka iso in da na sami shanun suke kiwo,
koda muka iso gurin,
sauka nayi nan nashiga waige-waige abun mamaki hanyar ta ɓace min na tsaya shiru ina ta kalle-kallen gurin amma kwata-kwata na kasa gane hanyar, ko wannan babban tudun da muka faɗo a kan tama ban ganshi a gurin ba nayi ta waige-waige amma babu ko a lamar sa.
"Kodai ba nan bane".
nayi maganar a kasan raina.
Bappa da tun É—azu yazuba min ido sai yanzu yayi magana
"Kin tabbata tanan ne hanyar?".
kai na gyaÉ—a alamar Eh.
yadubi matasan da muka taho da su, tare da kiran sunan É—aya daga cikin su yace
"Isa Kunzo kiwo a nan wace rana kuma?".
suka ce masa Eh suka kuma faÉ—a masa ranar,
kuma ranar da nabi su muka shiga cikin rugar su, duk da kuwa basusan ina biye da su É—in ba.
Bappa ya jinjina kai kana ya mai da duban sa gare ni yace
"Ta'ina ne gurin?".
É—an shiru nayi tare da lumshe idanuna a hankali suffar gurin duk da bawai mance sa nayi ba yashiga zuwa min idona, na buÉ—e ido da sauri.
nace "Gurin akwai dutse babba sannan a gefen dutse É—in akwai bishiyoyi karkashin bishiyoyin kuma yashine,
gaban su can kuma babban ruwa ne kafin wannan babban ruwan kuma akwai wani fuwa É—an karami ne sosai".
shiru Bappa yayi kana yace
"Haka ruwan yake".
nace "Eh".
ya tan baye su Isa ko sun san wani gurin ruwa mai irin yanayin da na siffanta?, suka ce
Eh sun san wani ruwa mai dutse da bishiyoyi.
Nan muka juya zuwa wannan ruwan da suka ce sun sanin.
Muna zuwa gurin na tsaya na kalli gurin gashi nan shima dai babban ruwa ne amma sam bai kai wan da muka zauna a gefen sa ba,
Kuma shima akwai dutse da bishiyoyin amma ba irin wancan ba.
nace ba shi bane.
Bappa yace muje wani guri shima ya san wani ruwa irin wan da na siffanta,
muna zuwa can É—in ma na kalli ruwa nace bashi bane.
ranar munyi yawo mun wuni muna yawo muna zuwa gurin ruwa daban-daban duk wani ruwan da muka je ko kaÉ—an bai kai girman wanda muka zauna a gefen sa ba daga wan da bai kai shi girma ba sai wanda shi kwata-kwata ma baya tafiya a guri guda yake.
Abun mamaki nayi-nayi na tuna hanyar da nabi har mukaje wannan gurin ruwan nakasa gashi dai ina ganin ruwan da duk wani abun da ke gurin ruwan a ido na amma sam na kasa tuno hanyar gurin.
duk inda nayi tunanin ta nan ne idan muka je sai naga ba gurin bane,
daga karshe muka je gurin wani katon ruwa mai girman gaske girman sa yakusa kai wancan ruwan yanayin ruwan yana kusan shigen kama da wancan amma shi babu dutse da bishiyoyi da wani alamun gurin da muka zauna agurin babu shi.
Bappa yayi shiru yana duban katon kogin kana yace
"Anya wannan ba shi bane?".
nace "Allah Bappa ba shi bane wancan ruwan yafi wannan girma kuma wannan babu dutse da bishiyoyi".
yace "To ai shima ga dutse tacan".
yanuna gefen mu tacan da É—an tara saka nin mu, nace
"Shi wancan dutse É—in ba a tagurin yake ba".
Shiru Bappa yayi kana daga bisa Ni yace muko ma gida.
Washegari ma muka kuma fita niman wannan ruwan sai dai yau tacan makotan rugan su Bappa mukayi,
a cewar sa ko tacan ne ruwan yake kai na yakife nake ganin kamar ta in da muka je jiyane. shima har yamma muna yawo babu alamar sa,
kwana uku muka jera muna fita, ranar na ukun da yamma muka dawo gida a galabaice muka zube a tsakar gida bisa taburma...

Bappa yayi tagu mi lokaci zuwa lokaci sai yace
"Allahu Akbar Allah mai girma".
Inna wuro tace
"Kwarai kuwa buwayi gagara misali".
yace "Kwarai kuwa Sumaye Allah buwayi ne gagara misali, tabbas maganar tun zamanin iyaye da kakanni ya tabbata,
tabbas maganar su na cewa a kwai arziki a yankin nan kuma sai mai rabo yake iya ganin sa har ya same sa ya tabbata ya tabbata sai mai rabon,ita kaÉ—ai take da rabon gani da kuma samu".
Bappa yakuma faÉ—in
"Allah mai girma taya kika gani ne cikin babban ruwan kika shiga kika samu?".
nace "A'a Bappa a dai cikin wannan karamin ruwa da ke kusa da babban da na faÉ—a maka muke wanka da sha da Sallah da shi É—in, aciki na samu bayan da ruwan ya cika kogin har gurin da muke zaman nan".
nan nakuma basu labari kamar yadda nabasu da fari da lokacin da naso tafiya na barshi a gurin da kuma faÉ—uwar da mukayi naso kuncesu na zubar da su na É—auki É—an kwali na.
"Ikon Allah wannan abu naki ne shi yasa bai baki ikon zubar da su ba,
yayi ta sa miki da ke da Æ´aÆ´an ki son abun a ranku duk da baki san menene shi ba,
in da baki da rabo da ko ganin suma bazakiyi ba,idan yaga dama kuma sai ya nuna miki yakuma nufeki da barin su agirin É—in"...

Adaren ranar Bappa yakira babban É—an sa Mahmud,
Mahmoud costom ne yana da zama a Abuja, matar sa É—aya da Æ´aÆ´ansu uku.
nan Bappa ya shige bukkar sa dan acewar maganan sirri ne.
bayan sun gama magana da Mahmoud yafito nan yake faÉ—a mana "Gobe idan Allah yakai mu Mahmoud zai zo zai yi hanyar da za'ayi a canza Lu'ulu'u zuwa kuÉ—i,kuma yace dole sai an haÉ—a da manyan shuwagabannin Nigeria, tun da har yawan su yakai guda goma,
sannan kuma barin Lu'ulu'u a cikin gida tare da mu yana da mugun haÉ—ari,
domin kuwa har idan labarin yafita zamu iya fuskantar matsala, dan kuwa ba shakka za'a iya kawo mana hari,
gobe da sassafe yace zai taso dan ma yanzu dare yayi ne".
Chapter 25 · 0% Book details