Sashe 8
Hamdah Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Ina gama wa na haye kan sallaya dan dama da al'wala ta na gabarar da sallar azahar kana nafito,
Na tadda har ta dama min kunun garin dawa da ruwan tsamiya sai tashi da kamshin kayan yaji yake,
a gefen ta bisa taburma na zauna tamika min kofin kunun,
na amsa nakai kofin bakina a sannu na soma sha,
a sannu cikin ikon Allah narika jin warin maganin da nake jin nan naraguwa,ina gama shan kunun ta miko min gauta a cikin farin laida tace
"Tun da goron bai miki ba ki gwada cin gautar wata kila shi ya miki,
gobe Litinin idan Allah ya kai mu zaki fara zuwa awu nan cikin asibitin unguwar nan,gashi anata faÉ—akar wa a gidajen rediyo yakama ta kifara zuwa dan yana da amfani kwarai."
kallon cikin tayi kana taci gaba da faÉ—in
"An ya kuwa HAMDAH lissafin cikin nan dai-dai kika yi?, cikin wata huÉ—u kamar cikin wata shida ko bakwai,cikin fari da irin wannan girma haka kuma cikin fari bai fiye girma ba".
murmushi nayi nace
"Allah Mama dai-dai nake lissafin kinga lokacin da aka kai ni asibiti watan sa É—aya ne dai-dai, yanzu kuma an kara wata uku kenan bayan wancan wata É—ayan kin ga wata huÉ—un kenan".
baki mama tarike tace
"Iye har kin rike lissafin dalla-dalla ikon Allah zamani da Æ´aÆ´an cikin ta".
dariya nayi cike dajin kunya narufe fuskata da tafin hannuna.
ranar gauta da kunun tsamiya na wuni sha cikin yardar Allah kuwa naji sassaucin abun da nake ji.
Washegari da sassafe ina kwance Mama tashigo ta tadani tace natashi na shirya natafi asibiti yin bukin,
bayan nayi wanka na shirya tare da ita muka tafi asibitin,ita tayi ta zirga-zirga da cuku-cuku ina zaune sai dai abun da yakama dole sai nayi da kai na nake binta muje.
Sai wajen karfe 1 muka gama komai har da awun,
Kasan cewar yau É—in Monday ne hakan kuwa yayi dai-dai da yau ne ranar awun masu cikin fari,dan haka ya zamo ranar zuwa awo na kenan duk bayan wata É—aya.
A gajiye muka shigo gida ga yunwa,
kitchen na shiga na É—auko kofin ragowar kunun tsamiya ta da mama ta dama min da safe kafin mutafi,
na fito tsakar gida gindin É—an bishiyan tsada da muke zama musha iska na zauna kan taburman data shin fiÉ—a,
ita kuma ɗumamen tuwo ta zubo tazo tazau na tana ci muna ɗan taɓa hira,har ta kammala,
lai dar magunguna da aka bamu a gun awu tajanyo ta fiddo da magungunar,
da sauri na kawar da kai na ganin maganin kaÉ—ai yasa naji zuciya ta yaso ma tashi,
"Karbi maza ki haɗiye kin ji abun da suka ce kada ayi wasa da shan kwayar yana taimako sosai,bari ma na tashi naje na nimo miki ƴan abubuwan da suka ce kirika ci wake kam muna da shi,karɓa kisha na tashi".
juyowa nayi jin abun da take faÉ—a ji nayi kamar na zandara ihu, maganin ta mika min tare da miko min ruwa tana cigaba da faÉ—in
"Karɓi mana kada su sha iska".
amsar maganin nayi ban da ruwan nace
"Ni da kunu zan sha bazan iya sha da ruwa ba".
tace "To sha dashi É—in".
da kyar na haÉ—iye da kunun ma jin yana kokarin dawowa da sauri naÉ—au agwaluma da ta siya min a asibitin naso ma tsotsa da sauri.
ta mike tana faÉ—in
"Bari naje gurin mai kayan miyar can na haÉ—o cefani".
kai kawai na gyaÉ—a mata tafita.
Baya na na jikina da jikin bishyar da nake zaune a gindinta,a hankali naci gaba da shan agwalumar,
Ina zaune agun har ta dawo da cefane niki-niki a talakance,
nayi mamakin ganin har da hanta a cikin cefanen,
batare da ɓata lokaci ba ta haɗa min gwaten wake da hanta da ganyen ogu. kamar yan da ma'aikatan asibiti suka faɗa...
duk bayan kwana biyu Mama zata siyo kifi ko hanta ko kwai ta sarrafa min shi,
lurar da nafara yi jarin awara da kosai yafara yin kasa nasan ba komai bane ya kawo hakan sai waÉ—an nan kayan cime-cimen da take girka min,
wani ranar da zata je yin cefanen har takai bakin kofa nabiyo ta da sauri nace
"Mama ki bar kashe kuÉ—in nan haka kwanakin baya awara mudu huÉ—u ake yi kosai mudu biyu, amma yanzu mudu biyu ake yi wani sa'in ma mudu É—aya da rabi,kosai kuwa yanzu mudu É—aya ne,kuma fa duk wannan siyan kayan abin cin da aka faÉ—a a asibitin ne yake cinye kuÉ—in,Ni dai Allah Mama ki bar siya haka ai naci da yawa ma fiye da yan da suka faÉ—a tun da sunce kwai É—aya ma naci ya wadatar,kifi kuwa ko na É—ari ne ba sai lallai an siyi hantan ba".
tace
"Tafi can me kika sani so kike kizo haihuwa kirasa jini sai an yi faman niman jini ko,ai waÉ—an nan abubuwan da kike cin sune zasu tai maka wajen kara miki jini, ko kin zubda jini gun haihuwa ma baza a sami wata matsala ba dan akwai jinin a jikin ki sosai".
kai na jinjina.
waje tayi tana cigaba da faÉ—in
"Yo menene amfanin niman kuÉ—in da baza'a magance damuwa ba lafiya ai yafi kuÉ—i".
juyawa nayi na koma ciki ina saka yadda zanyi na hanata kashe kuÉ—in nan da yawa dan yanzu jarin da muka dogara dashi É—in ma yafara yin kasa idan ya karye gaba É—aya wace madafar zamu dafa...
Acan kasar India lokacin da Ya Masa'ud yasa mi labarin abun da ya faru,bakara min girgiza da tashin hankali ya shiga ba,cikin matukar tashin hankali yabaro kasar yatoho Nigeria,yayi kuka da hawayen sa da yazo ya iske Abba yakori HAMDAH ba'a masan in da take ba kuma yahana a nimo ta.
lokacin yayi yunkurin nimota Abba yace kada ya soma,bai dai bi na Abba'n ba, ya baza cigiya cikin garin Bauchi sai dai ba'a sami wani alamar da ya nuna tana cikin garin ba.
su Aunty Rafee'at
sunyi yunkurin kiran su Abbu da suke can kasa mai tsarki su sanar musu,
Ummi tace kada su sanar musu su barsu suyi iba dan su cikin nutsuwa da kwanciyar hankali da lumana.
kullum Ummi na kan sallaya tana yiwa É—iyar tata addu'a da fatan samin kariyar Allah agare ta aduk in da take a faÉ—in duniyar nan....
....★
After 1 month
Yau da wuri na dawo daga awu dan da sassafe Mama ta tashe ni na shirya ta rakani har cikin asibitin kafin ta dawo, lokacin da muka isa asibitin mutum uku na samu a gabana.
na shigo gida na tadda Mama tana ta suyan awara masu siya sun zagaye ta,
ɗaki na wuce na tuɓe hijabi na na aje laidar agwaluma da na siya da ɗarin da Mama ta bani tace ko zan ga wani abun da nake so na siya,
kana nafito.
in da take na isa nayi mata sannu da ai ki tace
"Har kin dawo da wuri haka an yi miki awun kuwa?".
nace "Eh ai yau mutum uku ne a gaba na".
tace "Ai yafi kaje da wuri ka dawo da wuri wani watan ma da wuri zamu tafi".
kofin kunun tsamiya mai É—umi ta miko min da alama bata jima da dama shiba,
ta tsamo kosai cikin mai tazuba cikin kwano shima ta miko min na amsa, zan zauna kan kujera tace
"A'a É—auko taburma ki shin fiÉ—a kimike kafafun ki".
nace to.