← Book details Hamdah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 34

Sashe 28

Hamdah Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

motar mutanen da mukazo da su a gaba namu yana biye da shi a haka muka fita a cikin hotel É—in, duk san da na É—ago kaina sai mun haka ido da Mahmoud,na lura tun fitowar mu idanun sa a kaina, kawar da kaina nayi gefe ganin sai satar kallo na yake tacikin mirror,
munyi tafiya mai nisa kafin muka isa wani katon gida mai matukar girma da kyau da tsaruwa,
a bakin get É—in gidan motar gaban mu ya faka a bakin get É—in Mahmoud ma ya tsaya a bayan sa,
É—aya daga cikin mutanen ya fito ya isa in da sojoji ke zaune a bakin get É—in,
yayi magana da su kana ya koma cikin motar,
nam sojojin suka buÉ—e get É—in,
motar ta fara shiga kafin mu muka bi bayan sa.
sai da na shiga gidan na daÉ—a ganin tsaruwa da girman sa,
muka paka a parking lot.
kana mutanen suka fito daga cikin motar,É—aya daga cikin su yazo yace, muma mu sauko.
daga can wasu sojoji suka taho in da muke,jogororin da muka taho da su suna gaba muna biye da su muka nufi cikin gidan, yayin da sojoji
biyu ke gaban mu.
wani lafiyayyen parlour muka bayyana cikin sa,nan da nan aka cike mu da kayan ciye-ciye da na sha.
munkai kimanin awa É—aya zuwa can mukaji takun sauka daga step's a hankali na É—ago kaina wani mutum ne ya karaso cikin parlour'n cikin girmamawa gaba É—aya Æ´an cikin parlour'n suka mike tsaye,
a sannu ya karatsa ya zauna kan wani kujera lafiyayye,nan kowa ya zube yana mika gaisuwa,
nima dai É—an tutsunawa nayi na gaishe sa,
É—an shiru ne yabiyo bayan gaishe-gaishe sannan mutumin yayi gyaran mursa sannan yace
"Sannun ku da zuwa kune ba'in ko?".
waÉ—an da muka zo da su suka amsa da Eh.
waya ya É—aga ya daddanna sannan ya kara a kunnen sa,
yayi magana zuwa can ya sauke wayar,
kana ya mike yadubi su Bappa yace su biyo shi,suka mike da waÉ—an da mukazo da su É—in da sojojin da suke tsaye har lokacin a cikin parlour'n suka fita,suka bar ni ni da su Nasmah a cikin parlour'n.
tun da suka fita har akayi sallar azahar ina nan zaune har wajen karfe biyu da rabi, babban damuwa ta ma sallar da banyi ba.
can wani soja ya shigo yayi min magana cikin harshen turanci yace na biyo shi,
na mike na ruko hannun su Nasmah muka bi bayan shi.
muna fita wani mota ya nuna min na shiga,
direba na zaune cikin motar shikuma ya zauna mazaunin mai zaman banza, nan direba yaja motar muka fita a gidan.
tafiya muka yitayi har na fara tsorata da tafiyar,naÉ—an ji tsoro ganin dukkamsu ban san suba,
ganin mu nayi bakin wani ramɓasheshen get mai girman gaske,
aka buÉ—e mana get É—in muka shiga shima tafiya mai tsawo mukayi a cikin wannan get É—in kafin muka kuma isowa wata get É—in,
nan mukayi ta wuce get-get kuma ko wanne da sojoji.
wata get muka iso mai kyau da tsaruwa muka tsaya nan kira yashigo wayar sojan, ya É—aga bayan ya sauke wayan ya dube ni yace na sauko.
nafito jiki a sanyaye,
tafiyar kafa mukayi mai tsawo,
kafin nan muka iso wani kofa,
Hmm in da ranka ka sha kallo tsaruwar wannan guri bazai misaltuba,
sojoji ne a tsaye a gun duk kanin su foskokin su sanye da bakin glass,
nan suka shiga saka mana na'ura a jikin mu suna gwada mu,ni da su Naseem,kafin muka haura kan step É—in da zata sada mu da kofar, nan kofar ma,
tafara bada wani sauti tana É—aukar hotunan mu,abun mamaki da al'ajabi,
daga bisa ni kofar ta buÉ—e muka shiga,
sojan na gaba ina biye da shi a hankali,
koda muka kuma isowa wata kofar nan sojan ya tsaya wani sojan da ke tsaye nan bakin kofar shi yayi gaba, yayi min alama da na biyo shi,
koda muka kuma zuwa wani kofar ma, tsayuwa wannan sojan yayi kana sojan da ke tsaye a wannan bakin kofar yayi gaba da ni.
muna zuwa wata kofar mai shigen, kama dana farko yakuma É—aukar mu a hota,ina tsaye ina kallon ikon Allah abun dai ya fara bani tsoro,
shima still anan sojan ya tsaya sojan dake wannan bakin kofar yayi ciki.
"Innalillahi ya ilahi ya lillahi".
abun da na furta kenan,
wani mashahuriyar katon parlour ne kamar ba a duniya yake ba,
wannan parlour'n muka shiga yanuna min gurin zama na zauna.
sai na janyo Æ´aÆ´ana na rungume su dan nasan sun gama gajiya da wannan tafiyar,
munyi zaman da yakai na 30min,
kafin daga can wata kofa ta buÉ—e wani mutum yafito yayi min alama da nazo na mike nabi bayan sa,
nan muka kuma shiga wani gurin na daban wan da yafi ko ina girma da tsaruwa.
muna shiga gurin can da nisa na hango su Bappa zaune kan wasu tsararrun kujeru,
numfashi na sauke,
cikin tsananin mamaki da kaÉ—uwa nake kallon wan da yake zaune kan kuje ran dake gaban su Bappa,
da mamaki nake lallon mutumin,
shugaban kasar mu na Nigeria ke zaune gaban su Bappa na karaso in da suke na zauna a kasa har lokacin mamakin ganin sa fal zuciya ta, mutumin da nake ganin sa a TV da mujallu,sai kuma cikin ɓarin baki nashiga gai da shi.
cikin sakin fuska fuska É—auke da annuri ya amsa gaisuwar,
kai Bappa ya É—an dukar cikin ladabi da girmama wan da yariga da yafi ka cikin girmama shugaba yace
"Ranka shi daÉ—e wannan itace yarin yar".
yafaÉ—a yana nuna ni.
annurin fuskar sa ya faÉ—aÉ—a idanun sa a kai na, ya jinjina kansa.
hannu ya miko yayi wa su Naseem alama da suzo, ai ko Naseem sarkin sabo ya mike ganin ya mike sai Nasmah itama ta bi bayan sa,
hannun su ya ruko yana faÉ—in
"Masha Allah sannun ku jarumai".
yafaÉ—a yana shafa kawunan su.
baki suka washe kamar sun san abun da yafaÉ—a shima yabisu da murmushi haÉ—e da yi musu wasa...
bayan wasu maganganun da yayi da na kusa da shi,
wan da duk kanin mu babu wanda yaji abun da suke faÉ—a, kana ya mike yabita wata kofa.
É—aya daga cikin mutanen da suke zaune a gefen sa yadube mu yace wa wasu da ke gefen mu a tsaye sukai mu masauki.
nan muka mike muka bi bayan su wani masauki na musamman a ka kai mu, nan ma kowa da É—akin sa.
anan muka kwana É—aya washegari
da safe aka buga min kofa koda na buÉ—e breakfast a ka shigo da shi wan da ya kawon cikin harahen turanci yace min na hanzarta mushirya a kwai kaya acikin É—akin muyi amfani da su, nace to.
na É—aga su Nasmah na basu abinci nima na ci, sannan mukayi wanka ,muka kimsa cikin kayan da naganau cikin wardrobe É—in É—akin lafiyayyun kaya na manya da yara.
muna gama shirin akayi knocking na kofar koda na buÉ—e wasu mutane ne maza guda biyu sukace min muje,
To. nace sannan na koma cikin É—akin na kamo hannun su Nasmah mukabi bayan mutanen.
acan waje muka haÉ—u da su Bappa nan muka shige mota mukayi gaba.
ido nazubawa hanya a raina nake faÉ—in
"Yau kuma ina za'a yi da mu?"....★

tundaga bakin get É—in da yanzu muka iso na fahimci airport muka zo a bakin get É—in muka haÉ—u da Mahmoud,
muna isa tuni sojoji sukayi ciki da mu.
direct in da jirgi yake suka nufa da mu,
lumshe idanuna nayi tare da kuma buÉ—e wa lokacin da na É—aura kafata kan step É—in jirgin, sai nake ganin komai tamkar a mafarki.
"To ina kuma yanzu za'ayi da mu a cikin jirgi?".
nayiwa kai na tambayar......!★

Ayi hakuri da typing error busy over👌🏻

*Wlh na fiku matsuwan ganin na kammala littafin nan hausawa sukace in aski yazo gaban goshi yafi zafi insha Allahu mun kusan isa.*🤦🏻‍♀️

*Ina barar addu'ar ku wacce tagoye ni tamkar mahaifiya aguna Allah yayi mata rasu*😭😭😭😭

Mommyn Twins ce
Chapter 28 · 0% Book details