← Book details Hamdah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 34

Sashe 30

Hamdah Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Washegari bayan mun dawo daga masallaci muka tadda an cike mana parlour da breakfast kalolin abinci iri-iri irin na gida Nigeria da kuma irin na nan kasar Saudi,
bayan munci munsha mukayi su wanka, aka kuma É—iban mu da sojoji jama'a sai gamu a fadar Saudi,
Ya ilahi ya lillahi na ga karrama wa naga karamci daga gurin larabawa, gaskiya larabawa akwaisu da karrama wa,
nan da nan ina za'a saka akarika yi da mu tamkar mu wasu ne, anawani kafa-kafa da mu.
Nan da nan aka cike mu da kayan cime-cime irin na larabawa....★
Bayan maganganun da ya gudana sakanin fadar Saudi da jagororin kasar mu da shugaban kasar mu yahaÉ—o mu da su,
nan fadar ta bukaci ganin Diamond É—in,
nan Bappa ya ciro sa cikin lajuhu wan da suke É—aure cikin laida ya mikawa É—aya daga cikin jagororin mu,
kana shikuma ya mikawa wani na kusa da shi sannan shi kuma yamika wa da dukkan alamu hukuma ne, ya karɓa kana ya taka zuwa sakiyar katafaren parlour'n saman table ɗin dake gaban wani farin dattijon balarabe yana zaune cikin kamala da dattako fuskarsa ɗauke da annuri,
ya aje laidar, tare da yin magana cikin harshen larabci.
shugaban shima yayi magana cikin harshen larabci da sauri wani da ke zaune a kasa kusa da kafar sa ya mike ya shinfiÉ—a wani farin gyalle kan table É—in kana yashiga kunce laidar,
ya juye Lu'ulu'u'n kan farin gyallen.
wani dake tsaye taÉ—an can gefe rike da wani É—an karamin a kwati ya maso da sauri tare da buÉ—e É—an karamin a kwatin,
yaciro wani na'ura kana yamaso kusa da table É—in,
ya É—aura na'urar kan Lu'ulu'u'n nan na'urar ta kawo haske tare da bada É—an sauti, idanun mutumin tar a kan na'urar, yaÉ—au mintuna da É—an dama kana yaÉ—ago,
cikin garshen larabci yayiwa wan da nafi tunanin shene shugaban magana,
kai ya jinjina tare da duban mu da murmushi É—auke a kan fuskar sa,kasan cewar bama jin bama jin larabci shima bayajin yaren mu, sai ya juya cikin harshen turanci yake magana,
"To a binciken da akayi yanuna wannan asalin *LU'ULU'U* ne muna tayaku murna".
yafaÉ—a fuskarsa É—auke da yelwataccen murmushi,
ai ko gaba É—aya gurin yakace me da hayaniya kowa yana faÉ—ar albarkacin bakin sa, sai faÉ—i ake wai wanene yasamo Diamond kuma wai a Nigeria.
mutanen saudi suke maganar, nan jagororin mu suka nuna ni, nan aka rika nuna Ni a na faÉ—in nice nasamo diamond É—in, sai kawai nadawo abun kallo, sai nuna ni ake wasu kam ma sai sun zo har kusa dani suna tayani murna,
wasu cikin harshen larabci suke magana sai dai bana fahimtar su gara waÉ—an da suke magana cikin harshen turanci suma É—in dakyar sabo da harshen su yanuna da Larabci turancin nasu da kyar nake iya ganewa.
nawo abun kallo har hotuna sukarin ka É—aukawa dani, wani zaizo kawai yatsaya yaÉ—auki hoto da ni,
mutane suka rika shigowa suka rika kallo na ni da yarana suka rika É—aukar su Naseem da Nasmah,suka rika magana cikin harshen larabci idan suka juya da turanci ne nake É—an fahimtar su,
sukayi ta yabawa yaran da kokari da gararabba da sukayi a bakin ruwa kafin mu samo Diamond É—in,
hatta shugaban sai da ya jinjina min.
nan da nan ya umurta aje banki a kawo kuÉ—i, muna nan zaune har waÉ—an da sukaje kawo kuÉ—in suka dawo aka rika shiga da gana masgo-masgo cike tam-tam da kuÉ—i, aka tarasu a tsakiyar parlour'n.
ido na ware cike da tsananin mamakin ganin yan da ake buÉ—e gana masgo É—in ana ciro kuÉ—i a ciki, kuÉ—i irin na kasar su.
"Sai kace kasa ko kuÉ—in ganye, to me zamuyi da wannan kuÉ—in?".
nafaÉ—a a fili har sai da Mahmoud dake kusa da ni yajuyo ya kalleni,
wasu larabawa ne suka shigo da sallama,in da shi shugaban yayi maga da harshen da muke ganewa wato turanci yake cewa sune masa na farashin Lu'ulu'u, nan suka ƙiyasta kuɗin Lu'ulu'u'n batare da ɓata lokaci ba.
nan da nan aka fara zuba kuÉ—in cikin na'urorin kirga kuÉ—i da suka kai guda goma, wan da duk da su akazo daga banki da kuma ma ai katan bankin. bayan an shafi tsawon awanni ana kirga kuÉ—in
masana farashin Lu'ulu'u' sukayi magana da shugaban,
kuma umurtar su yayi a koma a karo kuÉ—in dan basukai kuÉ—in Lu'ulu'u'n ba,
wannan karon har da zinari aka haÉ—o.
aka rika kirga kuÉ—in duk gana masgon da aka kirga kuÉ—in cikin sa sai a maida kuÉ—in ciki a rufe a kuma zubuta a dadin kuÉ—in cikin sa,haka akayi tayi anayi ana rubutawa.
ni dai ido na zubawa sarautar Allah ni ban ma iya kirga tulin gana masgo É—in da suketa tura kuÉ—i ciki kamar takardu ba,har naji na gaji tamkar nice na'urar dake kirga kuÉ—in, da mutanen da suketa sakawa cikin gana masgo É—in.
bayan da aka gama kirga kuÉ—in a ka jibgesu a sakiyar parlour'n haÉ—e da
gwala-gwalai da sauransu....

Wannan dattijon balaraben da ke bada umurnin duk abun da za'a yi, yayi gyaran murya tare da nuna kuÉ—in kana yasoma magana cikin harshen turanci,
"Wannan shine kuÉ—in Lu'ulu'u'n".
nan kuma ya bukaci a kira masa shugaban kasar Nigeria,
cikin hanzari na kusa da shi yaÉ—aga waya ya danna kiran lambar shugaban kasar Nigeria,kana ya haÉ—a shi da shi,
nan yake sanar masa an ƙiyasta kuɗin Lu'ulu'u'n sannan kuma gashi an kirge shi, nan shugaban kasar mu yabukaci a haɗa shi da Bappa,yace yaya za'ayi da kuɗin,
Bappa yace kawai a sashi a sanunun banki dan bamusan yanda zamuyi da wannan kuÉ—in ba.
shugaban kasar mu ya turo da number account É—in da za'a saka kuÉ—in ciki.
nan shugaban yabada umurnin a tafi da kuÉ—in banki,
nan da nan aka fara fita da kuÉ—in,
a ka kwashe su zuwa banki,
a ka zuba su cikin account ɗin da shugaban kasar mu yabada na bankuna daban-daban.....★
masauki a ka kuma mana acikin masarautar, kwanan mu uku a gurin naga halacci iya halacci, nadawo abun kallo har daga waje ana zuwa kallo na duk wan da yazo kuwa sai yayi hoto da ni.
har nayi kawaye Æ´an matan larabawa Æ´an cikin masarauta.
idan naji suna larabci sai nace su koya min, nace an ya ma kuwa zan iya?, sai suce zan iya babu wuya.....★

Acan cikin garin Bauchi kuwa, zaune Ya SALEEM da Na'ima suke a parlour'n sa........!★

mommyn Twins ce
Chapter 30 · 0% Book details