← Book details Hamdah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 34

Sashe 27

Hamdah Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

kayan jikina na tuɓe na ɗaura zanin a kirji nashige bathroom naje nayi wanka,sannan na fito na tuɓe su Naseem suma naje na musu, ina fita na shinfiɗa sallaya da nagani cikin ɗakin kasan cewar nayi al'wala nagabatar da sallar magrima.
tuni su Nasmah sunyi bacci sabo da gajiyar mota,
sai na gyara musu kwanciyar su a kan lafiyayyen gadon,
bayan na idar da sallar Isha ina zaune a kan sallaya akayi knocking É—in kofar,
a sannu na mike na isa bakin kofar na buÉ—e, wani mutum nagani sanye da uniform irin na masu ai kin hotel, da tray É—in abinci a hannunsa,
yayi min sannu na amsa,baya mayi na É—an ja murfin kofar ya shigo ya dire tray'n kan table É—in da ke tsakiyar É—akin mai lodin kayan abin ci da drinks kala-kala kana yafita, na mai da kofar na rufe, na koma bakin gado na zauna.
da ma yunwa na ke ji nan na janyo tray'n na soma cin abincin,
inaci ina kallon su Naseem dan na san suma yunwar suke ji sai dai gajiya ya sasu bacci,
ina gama ci naje na wanko bakina na dawo, na kwanta bakin gadon tare da yi musu addu'a nima nayi nagyara kwanciya ta.
washegari bayan nayi wanka nayiwa su Nasmah na shirya su muna zaune,a ka shigo mana da breakfast bayan mun karya.
Bappa yashigo da sallama kan kujerar É—akin ya zauna,
nan nashiga gaida shi ya amsa kana yake tanbaya ta ya gajiyar hanya?,
nace
"gajiya yabi jiki". Naseem kuwa tuni ya wuce jikin sa yana ta tsalle Nasmah ma tabi bayan sa sunata yi masa gwalaɓe,suna ta shekewa da dariya Bappa shima sai biye musu yake yana ta taya su sai zuba masa surutu suke wan da ma maganar tasu bagane ta ake ba.
zama Bappa yagyara tare da duba na kana yace
"ÆŠazun Mahmoud ya zo ya same ni da jagororin da aka haÉ—a mu da su sun bani tabbacin bazamu sami ganin shugaban kasa a yauba,
zamu É—an É—au lokaci sai dai kawai muÉ—an jira,
idan kuma zamu koma to,amma gaskiya
ni ina tunanin komawar mu domin iyanzu maganar Lu'ulu'u'n nan ya karaÉ—e cikin rugar mu har da wajen sa, ina tunanin mukoma yanzu mutane basa da gaskiya É—ai-É—ai ku ne masu gaskiya a zamanin yanzu, yan da yashiga kunnen mutanen gari kuwa na tabbata zai fita har wajen gari,
har miyagon mutane suje suji sukawo mana farmaki,
gaskiya bazamu koma ba zamu jira har lokacin da zamu sami ganawa da shi shugaban kasar".
kai na jinjina alamun gamsuwa tabbas,
kuÉ—i a gida akwai haÉ—ari musamman irin wannan da na ga gwamna yahaÉ—o mu da jami'an tsaro, nace
"To Bappa duk abun da ka yanke dai-dai ne".
yace
"Gaskiya zamu zauna ko nan da kwana uku ko huÉ—u ne in dai har zamu gana da shi É—in yafi mana komawar mu da dukiya kan hanya domin ko a hanyar komawar mu ma kaÉ—ai hatsari ne bane kuma ace mun koma cikin ruga in da babu jami'an tsaro".
nace
"Hakane Bappa muzaunan kawai".
kai ya jinjina kana ya mike yana rike da hannun Naseem, Nasmah da take ta kokarin binsu yace ta zauna ta tayani hira,
zai tafi da Naseem shima ya tayashi hira....

kwaman mu uku a Abuja acikin wannan hotel É—in, alhamdllh a kwana na ukun bukatar mu ta isa ga shugaban kasa sai dai har lokacin ba'a bamu da mar ganin sa ba, a kwana na biyar,da safe ina zaune akayi knocking naje na buÉ—e kofar Mahmoud ne yashigo da sallama,
rike da babban laida a hannunsa,
na gaishesa cikin girmamawa ya amsa tare da mika min laidar dake hannunsa tare da faÉ—in
"Gashi ku shirya kuyi sauri, yau kam in sha Allah zamu sami ganawa da shi koba shi É—in bama zamu zauna da wasu manya na kusa da shi kuyi sauri ku shiriya ya zama na dai da kuna cikin shiri".
nace "Tom".
na karɓi laidar tare da yi masa godiya yafita.
na zawo bakin gado na zauna tare da buÉ—e laidar na fara ciro kayan cikin, kayane na sawa,kaya masu kyau narika É—aga na Naseem da Nasmah masu kyau Æ´arkanti, dukan su da takalmar su masu kyau,
da ma tuni na riga da na musu wanka, na cire musu kayan jikin su nasa musu wannan kayan,
yara suka fito shar da su tamkar Æ´aÆ´an turawa, sunyi kyau sosai na tasasu gaba inata kallon su cikin ban sha'awa,
sannan nima na mike na camza nawa dogon riga ne da gyalen sa Ash mai ratsin gold
É—in duwatsu haÉ—e da takalmi Black and gold, takalmin mai É—an tudu ne kaÉ—an.
nasaka kayan a hankali na isa yaban mirror abun da na daÉ—e banyi shi ba yau nayi,
nashafa
pawda da nagani kan mirror'n haÉ—e da man lips kana,
nayi rolling É—in gyalen a kaina,tsayuwa ta na gyara gaban mirror'n
masha Allah duk da na rame na dishe amma bai hanani fitowa a HAMDAH ta ta daba kaÉ—an ba,
murmushi nayi ganin yan da nayi kyau a cikin kayan yaɗan ɓoye min rama ta.
da misalin karfe 12 Mahmoud yashigo daga bakin kofa yatsaya yace nayi sauri na zo. sai ya juya yafita ,
cikin hanzari na sakawa su Nasmah takallamar su sannan na kama hannunsu muka fito,
muna fita farfajiyar hotel É—in,
nan na tadda su, Bappa yana zaune cikin mota gefen mai zaman bamza yayin da Mahmoud ke zaune a mazaunin direba. muka karaso Bappa yana ta kallon mu yana murmushi,
nima murmushin nayi muka karaso na buÉ—e gidan baya na shiga Naseem kam fir yaki shiga sai da na mika sa wa Bappa.
Chapter 27 · 0% Book details