← Book details Hamdah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 34

Sashe 20

Hamdah Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Zaune nake na buga uban tagumi nayi shiru ina lissafa kwanakin da mukayi a cikin daji tabbas yau idan ban mance ba kimanin watan mu biyu kenan acikin dajin,
wasu hawaye ne suka zubo min na share su.
Ikon Allah haka zamuyi ta rayuwa a cikin daji har mu mutu karshe namun daji sucinye mu,
tausayin kaina da na Æ´aÆ´ana ya kamani sai na rungume su na fashe da kuka.
ganin sunyi bacci na shin fiÉ—a musu abun kwanciyar su wato zanin goyon su,
na janyo hijabina na lulluɓe su,
na mike na soma tafiya..
kallon sama nayi hadari ya haÉ—u bakikkirin daga can kasa sai walkiya ake da rugugin tsawa da alama dai anata zabga ruwa daga can da nisa,
ina tsaye ina tsinko abun da zan ci daga can nesa narika jin kugin ruwan nan yana karuwa sosai ba kamar nasauran kwanaki ba ƙugi ne sosai mai matukar amon sauti sosai.
da sauri na juya na fito daga cikin bishiyoyin na nufi in da su Naseem suke kwance cikin hanzari.
Daga can na hango ruwan yana wani irin gudu da kugi daga can da nisa yana wani sama da kasa.
Huff na É—aga Nasmah na goya ta kana É—auki Naseem da gudu na juya ganin ruwan
yana haurowa a hankali inda muke yanata taruwa a hankali har ya wuce idon sawu na,
daga can cikin kogin kuma yana wani irin gudu yana yin sama da kasa sai ruwan ya haÉ—u da junan sa ya fansalu sai yayi sama sannan ya koma kasa.
gudu nake da iya karfi na nayi bayan dutsai cikin sansanin tashin hankali galin ruwan ya iso inda muke zama ya mamaye gurin wan da yake gudu daga can kuma sauran kiris yakaraso,
bayan dutsai da na ɓoyen ma tuni ruwan ya iso har gurin,
cikin kaɗuwa da tashin hankali nasoma hawa kan dutsan da ko a mafarki ban taɓa tunanin zan iya hawan sa ba sai gashi na haura kan sa da goyo da kuma wani ɗan a hannuna can kuma saman sa sosai.
kan kace me ruwan yataho da wannan kugi da ambaliyar da yake,
gurin da muke zama yadawo tamkar cikin ainihin kogin hatta bishiyoyin nan sai da ruwa yahaye kansu,
duk da girma da tsawon da dutsai É—in nan yake dashi sai da ya kusa haurowa sama in da nake tsaye jikina na cirawa,
rumtse idanuna nayi nakuma buÉ—ewa cikin ruwan da yake wani irin gudu da kugi, ina ambaton sunan Allah, yau kam nasan mutuwa ce yazo mana babu makawa ruwa ce zata zamo ajalin mu,zata tafi da mu mu kuma mutu a cikin ta.
kankame Æ´aÆ´ana na kuma yi nagama sadakarwa na mika wuya ga mutuwa gaba É—aya.
wasu irin halittun ruwa narika gani daban-daban wani abun ma idan nagani rufe idanuna nake da karfi har sai ya wuce kafin na buÉ—e,haka sukayi ta wucewa a kan ruwan,
wani abun da yadaÉ—a firgita ni da bani tsoro daga can najiyo guÉ—a mai karfi a can tsakiyar ruwan guÉ—a mai tsawon gaske babu jan numfashi ko sauke wa,
ido na zuba sosai daga can in da guÉ—ar ke tashi sai dai banga komai ba sabo da sakanin mu da nisa kuma da alama daga can kasa abun ke wuce wa.
sai narika jin kamar iska tana jana kuma karfin iskar tacikin ruwan ne,kuka na fashe dashi na durkushe kan dutsai É—in na kankame jikina,ina ambaton sunan Allah.
har lokacin ban fasa jin iska na kokarin jana ba,
a hankali guÉ—an da ake yarika raguwa alamun yana yin nesa da ni,
iskar da ke jana kamar zai faÉ—ar dani cikin ruwan sai yarika sassauta, lokacin da na dai na jin sautin guÉ—ar nan gaba É—aya iskar ta tsaya.
abun tun sassafe sai yamma can kafin ruwan yafara sassauta gudun da yake, yana sassauta yana yin kasa-kasa,
a hankali yarika yin kasa yana wuce wa har ya dawo in da yake,
Numfashi mai cike da zallar tsoro na sauke a sannu narika bin gurin da kallo har zuwa gurin da muke zama,
yashin ya daÉ—a wankuwa yayi fari soll sai dai har lokacin da jikan ruwa sosai a hankali nafara kiciniyar sauka daga kan dutsan nayi matukar mamakin yadda akayi na iya hawa saman dutsan,
daƙyar na iya sauka kasa.
a hankali narika takawa in da kafata har yana lumewa cikin saka sabo da har lokacin da dam shin ruwa,
a hankali na matsa can gefe in da shima akwai damshin sai dai ba kamar in da muke zama ba.
ranar a nan muka kwana cikin ciyawa,
sai dai ban yar da na rumtsa ba dan gani nake kamar ruwan zai dawo....

Washegari da safe gurin ya daÉ—a sha ya tsantsame sai dai har lokacin da É—an damshin sai dai ba kamar na jiya ba,
sai da rana yafito sosai kana
a hankali na É—auko su Nasmah muka dawo gurin zaman mu,
ido na kurawa kogin nan ganin yadawo yan da yake da, kamar bashi bane jiya yayi ta hauka Allah mai iko.
É—an kwalin kai na na kunce na shin fiÉ—a a kasa kana na zaunar da Naseem a kai ina faÉ—in
"Zauna kada ka sauka kasa kaji gurin da sanyi".
da sauri na kunco Nasmah da take ta musu-musu tana kuka a abaya,
na zauna na basu abincin su,
sai dai har lokacin bata fasa kananan kuka ba,
jijjiga ta nashiga yi ina faÉ—in
"Yi hakuri Nasmah nasan wan ka kike so kuma nasan ruwan nan akwai sanyi kibari rana yadaÉ—a yin zafi idan ruwan yayi É—umi sai na muku".
nayita jijjiga ta.
zuwa can an jima
jin rana yadaɗan yi zafi sosai sai na tuɓe su na dubi Naseem da ke zaune yana ta wasa da yashin gurin nace
"Zauna na fara yi mata wanka sai na ma ka ko".
na mike da ita a jikina na isa gurin ruwan da muke wanka, ruwan yada É—a yin fari soll,
kasan cewar rana ya taso ruwan har yana kashe ido sabo da tsabar hasken da ya kara,
a hankali na fara yi mata wankan ina yi ina kawar da kai na daga kallon ruwan saboda kashe min ido da yake, tamkar hasken ranar a cikin ruwan yake.
koda na gama yi musu wankan.
babu jimawa sukayi bacci,
mikewa nayi na koma gurin ruwan domin yin al'wala, na sun kuya ina ta kare fuska ta da hasken rana ke haska cikin ruwan yana kashe min ido, na saka hannu cikin ruwan a hankali na ɗibo na fara yin al'walar, na kuma mai da hannuna a karo na biyu, da sauri na ciro hannun jin na taɓa wani abu,
sai kuma na mai da hannun a hankali jin kamar dutsai ne na taɓan, a raina nake ai yana cewa ai dutsan yashi ne,
na cusa hannuna nakuma É—ibo ruwan sai na haÉ—o da yashi da wani farin dutsai, ina É—ago hannuna hasken rana ya haska dutsan tamkar wutan lantar ki mai hasken gaske. da sauri na rumtsa idanuna jin hasken har cikin jijiyoyin idanuna, cikin hanzari na watsar da yashin gefe ina mammatse idanuna,
nayi al'walan da sauri na bar gurin...
koda yamma tayi da nazo yin al'walan la'asar lokacin rana tayi sanyi hasken ruwan yaÉ—an ragu,
ina saka hannuna cikin ruwan nakuma É—auko dutsai É—in,
A hankali na É—ago shi narika juyashi a hannunna dutsan fari soll mai kyau da shi sai kyalkyali yake duk da kuwa babu hasken rana,
narika kallonsa gwanin ban sha'awa.
A hankali na mika hannu na É—auko É—ayan da É—azu nayi wurgi da shi na haÉ—a su ina ta juya su cikin sha awa,
nakuma saka hannuna cikin ruwan nayi ta laluɓo duwasun ina ciro su sai da naciro guda takwas na haɗa da biyun hannuna suka zamo guda goma,
bayan na gama al'walar na koma gun su Nasmah a kan abun goyon su na zuba duwasun,
ina zubawa kuwa da sauri har suna rige-rigen É—auka sukayi ta wasa da shi,
nima ina idar da sallar na zauna nayi ta tayasu wasan da duwasun gwanin ban sha'awa da kyau da É—aukar ido.
dariya nayi ganin yanda suke wasa da duwasun su É—auki wannan su wurga sai subi sukuma É—auko wa,
nace
"Kuma yayi muku kyau ko ai dutsan mai kyau ne nima wlh yayi min kyau kuyi wasan ku da shi".
nafaÉ—a da murmushi ina daÉ—a tura musu duwatsun gaban su...

Washegari ko da rana yafito dukan su na kwasa naje musu wanka Nasmah na goye sai na fara yi wa Naseem ko da na gama mishi, sai na saka hannuna nayita laluma cikin ruwan can na ciro dutsai É—in guda É—aya na dunkule shi cikin hannuna na cusa masa cikin hannunsa ina faÉ—in
"Gashi na karo muku abun wasa dun kule shi a hannunka kar ya kashe mana ido".
na kunce Nasmah na goya shi itama nayi mata wanka kana na laluɓo mata guda ɗaya na saka mata cikin hannun ta nace
"Kema ga naki".....★
Chapter 20 · 0% Book details