← Book details Hamdah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 34

Sashe 1

Hamdah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani irin kallo yake bin Na'ima da shi yayin da yakejin kwakwalwar sa nawani irin juyawa zuciyar sa kuwa bugu yake kamar zai faso kirjin sa yafito,
System É—in gaban sa yature gefe kana cikin jan numfashi haÉ—e da huci yace
"Me kike son faÉ—a ne kam me kike nufi?!".
baki ta karkata tace
"Ina nufin akan gado na samesu sarkafe da juna suna ai kata baÉ—ala".
É—an sakai ta maganar nata tayi kana tashiga jan hanci tana matse ido da karfi wasu gun tayen hawayen da suka fito takai yatsa ta sharce kana cikin murya mai kamada mai sonyi kuka tacigaba da faÉ—in.
"Wlh abun nan ya jima yana dami na, Ni nasan akuyata tayi kuka nasan bani da hakuri amma bazan iya cin amanar aure ba,bazan iya cigaba da zuba ido ana ha'intar kaba bazan iya gani ka karɓi ɗan shege a rashin sani ba,kayi tunani da kyau taya za'ayi cikin wata guda ya zamo naka bayan a cikin watan baka garin kuma ka barta bata da sarki".
da karfi ya furta
"Ya isa!".
ya mike tsaye cikin jin yanda kansa ke juya masa yanufi cikin bedroom É—in sa.
bayan sa tabi da kallo har yashige yarufo kofar da karfi,
sai ta saki wani murmushi tamike ta koma side É—in ta tanajin zuciyar ta wasai...

Wani irin bugawa kirjina yayi da mugun karfi acikin baccin da nake wan da nakoma bayan sallar asuba,
afirgice na mike zaune tare da dafe kirjin da yake harbawa da karfi-karfi. jikina na rawa na zamo daga kan gadon na nufi kofa da sauri na fita ta cikin babban parlour nabi nanufi side É—in sa da sauri na tura kofar bedroom É—in sa yayin da na dafe kirjina da hannuna guda,
ya na tsaye cikin É—akin yabai wa kofa baya da sauri na isa na rungumo shi ta baya,tare da manna kirjina da ki bugawa da karfi cikin bayan shi.
"Ya SALEEM".
nakira sunan shi muryata na rawa,
juyowa yayi yaciro ni a jikinsa da karfi tare da watsa min wani irin kallo, fuskarsa ta rikiÉ—e takoma irin fuskar Ya SALEEM É—in baya babu wasa ko annuri kan fuskar nasa,
cike da fargaba da tsoron ganin yanayin sana cikin muryar kukan da ya suɓuce min nace
"Ya SALEEM wani mutuwar a ka kuma ko? dan Allah ka faÉ—a min yanzu ba sai naje gida ba kafaÉ—a min kawai nima na mutu ko zan huta da azabar da nake ji cikin zuciya ta".
hannuna ya damko da karfi ya janyoni ya nufi kofa dani cikin muryar kuka nacigaba da faÉ—in
"Ya SALEEM karka kai Ni ka nuna min gawar wani, mutuwa zanyi".
baiyi magana ba bai kuma sake hannuna ba har muka fito cikin parlour'n sa,kana ya saki hannuna cikin fusa tacciyar murya wanda ko a da can baya kafin zuwa na gidan da kuma farin zuwana gidan ban taɓa jin yayi min magana da irin saba yace
"Waye uban sa!!?".
bin in da ya sauke yatsar sa nayi da ido kana naÉ—a go na kalli fuskarsa da babu ko É—igon annuri cikin rashin fahimta nake kallon sa.
wani uban tsawa ya buga min tare da kuma faÉ—in
"Waye uban sa nace!".
wani irin zabura nayi da jin sawan da ya bugamin ya kuma danna yatsarsa da ke kan cikina sosai,nan take abun da ke cikina ya motsa da karfi.
jikina na rawa na kai yatsata sai tin kirjin sa nace
"Gashi nan".
hannuna ya bige da karfi cikin kuma tamke fuska yace
"Raina min hankali zakiyi faÉ—a min waye shi waye shi da har zai haÉ—a muhalli da ni!".
kuka na sake da karfi ina faÉ—in
"Kai ne uban sa Ni bansan wani ba Ya SALEEM dan Allah ka dai na min wannan wasan kai ne uban sa kaine-kaine!".
nafaÉ—a da karfi.
ida nunsa ya É—aura cikin nawa kana yace
"Ni abokin wasan kine da zan miki wasa in tan bayeki uban sa kice ina miki wasa akan bakisan uban nasa bane ko..."
da karfi na rufe idanuna batare da na bari ya karasa faÉ—ar abun da zai faÉ—an ba nace
"Ni ban sani ba, ban sani ba, ban sani ba, ban san kowa ba Ni kai nasa Ni kai ne uban sa".
nafaÉ—a da karfi cikin muryar shashsheka da toshewar kwakwalwa da gaza fahim tar in da ya dosa.

"Uban sa shi ne wan da yake sajewa da kayan makarantar su yazo yagama abun da zaiyi yafita, ai rana dubu ta ɓarawo rana ɗaya ce tak na mai kaya".
cak na ji kukan da nake ya tsaya a hankali na juyo in da naji maganar ke fito wa, Na'ima nagani tana tahowa cikin parlour'n cikin isa da izza ta karaso cikin parlour'n tana cigaba da faÉ—in
"Ai ita da ma haka rayuwa take zaka daɗe kana tsula tsiyar ka rana ɗaya tak a sirin ka ya tonu, baki taɓa tunanin zuwan wannan ranar bako?".
da É—inbin mamaki nake kallon ta yayin da naji abun dake cikin kwakwalwa ta yana son fin karfin tunanina,kai na na dafe da karfi jin yana min wani irin mugun sara.
maganar ta nakuma sinkayo wa
"Da auren ka karika kawo maza cikin gidan auren ka wannan wace irin rayuwa ce".
zuwa yanzu kam na fahimci duk inda batun nasu ya dosa da sauri na waigo in da take nashiga girgiza kai tare da faÉ—in
"Aunty Na'ima kiji tsoron Allah me kike son faÉ—a a kai na".
kugu ta rike tace
"Amma gaskiya yarin yar nan to in banji tsoron Allah ba tsoron ki zanji abun da kike ai katawa ne yau ashirin ki ya toni bazan taɓa zuba ido a haifo ɗan shege cikin gidan nan a matsayin ɗan gidan nan ba, da ma nasan zaki musa dan bakiyi zaton ranar tonon asiri irin na yauba".
kallon ta ta maida kan Ya SALEEM da ya zube kan kujera tare da dafe kansa da hannayen sa biyu tace
"My SALEEM Ina da shaidu kwarara guda uku wan da duk wani abun da ke faruwa a cikin gidan nan suna gani sun ma rigani gani, kuma ko Kotun koli ne zanje da su".
tsayuwar ta ta gyara ta dubi kofa kana ta buÉ—e murya tace
"Baba Mai gani,Sani direver Habu mai shara".
Da sauri na juyo jin an turo kofar da sallama,
baba mai gani na gaba Habu da Sani suna biye da shi,suka karaso cikin parlour'n kan su a kasa,
a kasa suka zauna taÉ—an gefe kana baba mai gadi yakuma sunkuyar da kai yace
"Gamu Hajiya". baya tayi ta zauna kan kujerar da ke bayan ta kana ta dube su sannan ta mai da duban ta kan Ya SALEEM,
da har lokacin hannunsa na dafe a kansa idanunsa sun kaÉ—a sunyi jajirr sannan tace
"Waɗan nan sune shai du na kuma duk kanin su sun rigani sanin abun da ke faruwa amma gasu kaji daga bakin su ranar wanka ba'a ɓoye cibi"..

Bin su yayi da ido har lokacin bai furta komai ba dan yan da yake jin kansa ya zarce tunanin mai tunani.
cikin wani irin bakar yanayi yakuma duban su kana yace
"Wa yake zuwa gidan nan bayan bana nan?".
ganin ya zuba musu ido yasa baba mai gadi gyara zama ya daÉ—a yin kasa da kai kana yasoma magana
"Allah ya huci zuciyar ka ranka shidaɗe,wata ranar da kayi tafiya da yamma ina zaune a bakin get naji ana ƙwanƙwasa kofa
sai na mike naje na buÉ—e karamar kofa naleka, sai naga wani É—an matashi tsaye da kayan makaranta a jikinsa nan nake tan bayar sa lafiya gurin wa yazo yake buga kofa,shine yace min shi É—an makarantar su HAMDAH ne gurin ta yazo dajin hakan kuma da ganin sa da kayan makarantar nasu sai na buÉ—e masa kofar yashiga,
to ina dai daga zaune lokacin
tun da yashiga kuma bai fito ba sai daf magriba, washegari yakuma dawowa da littattafai a hannunsa yace min wai zaije koya mata karatu ne ita takira sa,to tun daga ranar ya jera sati yana zuwa da kayan makaranta sai daga baya kuma ya dawo zuwa da kayan gida". yana kai wa nan yakuma yin kasa da kai cikin nuna tsantsar gaskiya.

Sani ya nisa kana yace
"Oga ranar ina cikin wanke mota nima na gansa ya shige cikin side É—in ta da kayan makaranta a jikin sa, to nima dai kusan kullum sai na gansa yashigo kuma lokacin da kayi tafiyar nan ne, wata rana kuma ina daga cikin parking space na hango su sun fito tana yi masa rakiya sai dai daga bakin kofar side É—in ta ta tsaya shikuma yafita".
Zama Habu ya daÉ—a gyarawa kana ya fuskanci Ya SALEEM da kyau kana yaso ma magana yayin da yayi kasa da kansa yace
"Oga lokacin da kayi tafiya kana da kwana 25 ranar ina cikin sharar yamma da sauri dan ranar na makara har gurin ya fara rufawa ina cikin share ta bayan É—akin ta ta gurin window najiyo dariya sosai na tashi kuma muryar na miji ne, to ban kula ba dai nacigaba da sharana dan a tunani na kunne nane yaji min karya dan nasan dai baka gari,
to can kuma sai narikajin muryar na mijin dai to da nagama sharana har zan wuce sai narika jin wasu Æ´an maganganu haka, sai kuma na leka sai naga wani mutum a kan gadon ta abun dai babu kyan gani,
to a lokacin naji muryar Hajiya tana rafka salati shine na zago da sauri".
Sani ya karɓi maganar da faɗin
"Nima ganin Habu da sauri ya shiga cikin side É—in ta da kuma ihun Hajiya da nake jiyowa shine muka rufa masa baya nida baba mai gadi to shine muka tadda mutumin yana fito wa daga É—akin ta"...
Chapter 1 · 0% Book details