← Book details Bariki Auren Soja Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 66

Sashe 9

Bariki Auren Soja Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ki fada min Abinda ke damun ki nice mahaifiyar ki Bakida wanda ya fini kuka tasa mai cin rai kafin ta bude baki " mama Ahmed nakeso banason ya Ismail ki sa baki baba ya barmu Muyi Aure dashi ina son shi sosai,

Shiru mama tayi tareda zuba mata ido tama kasa cewa komai tasan cewa maganar babbace tunda duk karar Maryam ta bude bakin ta fada lallai kuwa tana son shi sosai,

Tashi tayi fita dakin megidan ta sameshi ta zauna cikin ladabi,

Baban Ismail Alfarma nake nema don girman Allah, juyowa yayi sosai ya zuba mata ido "ina jinki saude wace irin Alfarma ce?

" akan zancen Auren nan ne don Allah ka hada Ismail da Yasmin tunda ita batada w'anda takeso ka bawa Yarinyar can zabin ta,

Zuba mata ido yayi kafin ya mike kawai ya nufi dakin su Maryam din tana ganin shi ta zabura jikin ta na rawa "Maryam baki y'arda da zabi na ba ko?

Kina so ki watsa min kasa a ido har zaki iya aiko uwar ki wurina ta fada min bakyason dana sai wani bare kuma soja

" toh shi kenan kije ki Aure shi Amma ki sani ba hannu na a ciki kuma bada yawu na ba kuma na gode wa Allah da yasa bake kadai bace Yata don haka zan hada mama na da Ismail nasan ita bazata bani kunya ba,

Wani irin kuka tasa jikin ta na rawa "baba kayi haku.." Ki yimin shiru kuma ranar Aurenki da nasa ba fashi kije ki nemi wani uban ya daura miki Auren Amma nidai kin gama zama a gidana,

Ya fita Abinshi ranshi matukar bace ya kira Yasmin tareda neman Alfarmar ta y'arda da Auren Ismail,

Abin yazo mata a bazata Amma kodan ta taimaki y'ar uwar ta dole ta y'arda, saidai ta nemi Alfarmar Baban ta ya barta ta karasa karatun ta kafin ya mata Auren ya kuma Amince,

Gefen Ismail kuwa ba wata matsala domin shi a yanzu tuni dama yafara son Yasmin din don Bazai iya furtawa Baban bane don haka canji yafi yimai dadi sosai,

Baban su Mahmud shine yayi ruwa yayi tsaki har aka daura Auren Maryam da Ahmed kuma mahaifin ta yace bashi baita kuma karta tako mai gida bai kuma y'arda kowa yayi hulda da ita ba duk da irin lallashin da kanin nashi yayi ta yi Amma fur yaki,

Shiyasa Yasmin take sato jiki tazo wurin y'ar uwar ta , sai bayan ta haifi Auwal ne baba ya fara sakko wa jin labarin ta kuma samun wani ciki ba tareda d'an ya shekara ba yasa ya fauwala wa ubangiji yasan cewa rabon haihuwa ne sanadi da yanzu yayi jikoki a kan titi,

Wannan shine d'an taka'i taccen tarihin Abinda ya faru sai kuci gaba da biyoni domin jin yazata kaya da Auren Yasmin din taku"

*Matar soja*
[8/30, 2:56 PM] Feenerh Wrtr: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
_*BARIKI*_
_Auren soja_
🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

_written by fenerh_
Maman Ammar

*Dedicated to*
Fiddousi mainasara

(¯`*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿`°¤,¸.•*´¯)

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/

TWITTER: https://twitter.com/pro__writers?s=09

9&10

Wanene Muhammad Abdullah M.A? Dana ga major Abdullahi Kudan yan Asalin Zaria ne mahaifin shi yayi Aikin soja tun ana Yakin basasa lokacin sune suka yiwa Nigeria hidima,

Mahaifiyar shi Hajiya Hauwa kuwa yar Asalin katsina ce fulanin Asali shiyasa ya gado fari sai dai kirar jikin shi ta mahaifin shine kowa yasan mallawan Zaria da tsawo kamar samu dawa

Ya gaji kyau gaba da baya yanada yayyi biyu mata duk sunyi Aure da yaran su manya ata kaice shine karamin su mahaifin su ya dade da rasuwa saura mahaifiyar su kawai,

Yan uwan shi mata duk suna Auren wasu kusoshin gwamnatin Nigeria ba wadda take nema a wurin shi mahaifiyar su na cikin gata sosai shiyasa take daukar yaran jama'a tana tallafa musu,

Tun mahaifin shi nada rai yakeda burin danshi ya yi Aikin soja kuma cikin ikon Allah ya samu gurbi a NDA har ya kammala tareda nasarori da dama har zuwa yanzu,

Da yakai matakin da yake kai na general a kananun shekarun shi domin ba duk soja ne zaikai wannan matsayin ba a under fourty,

Matsalar shi shine rashin yin Aure wanda shi baida burin yin Auren ma A rayuwar shi Sam domin duk abinda yake nema ya mallake shi kudi mulki mata kuwa da kudinka sai ka zaba wasu ma kyauta zasu kawo Kansu,

Saidai har yau baiga macen da ta zauna a rayuwar shi da har zai iya Auren ta ba sai dai zuby itama kawai shakuwa ce da kuma hidima da take mai da Aljihun ta kasan cewar ta y'ar gidan minister saidai wulakanci daban daban take gani akoda yaushe wurin MA,

Saidai bata sani ba yana ganin kimar ta fiye da duk macen da yake Hulda da ita domin yafi sakewa da ita ko a wurin harkar su yana dan samun gamsuwa da ita,

Cigaban labari

Kwalliya tayi sosai cikin wata doguwar rigar shadda blue kamar zataje fati ta daura dankwalin a sittin tareda yafa farin mayafi a gefen kafadar ta kana iya hango irin Aikin da gaban rigar yasha da stones suna sheki ga kirjin ta sunyi wani irin cika suna daukar hankali wani farin takalmi ne da kuma y'ar karamar pos dinta ta rike,

Hot 8 dinta take dannawa tana tura sako sai murmushi take fitar wa mai kaya tarwa,

"Yasmin har kin shirya? Taji muryar Maryam " eh Aunty ina Auwal da Baban shi nifa na matsu bamu tafi ba wallahi,

"Wai d'okin zuwa gidan Momyn MA ne haka? " bazaki gane ba Aunty Matar nada kirki kamar ba ita ta haifeshi ba wallahi sainayi sanadin da zatazo taga iskan cin da yake tsulawa a bariki d'an iska kawai,

"Nashigesu don girman Allah Yasmin kirufa mana Asiri ina ruwanki da rayuwar shi ? Nidai inkin San Abinda zakiyi kenan ki hakura bari infadawa Baban Auwal kinfasa,

" aa bazan yiba karki hana ni tafiya ai inada hankali yazan hada Uwa da d'an ta,

Fitowar Ahmed da yaron shi yasa shi tsayawa kallon ta "aa kanwa ta irin wannan wanka karkisa ace Amarya na karo wa maman Auwal,

" to dafa? Ai nice Amaryar dama, ta fada tana dariya, haka ne fa Kece ta karfen muje yamma nayi ko,

Fita sukayi tana dauke da Auwal a hannun ta Maryam ta rakosu kofar fita kafin ta koma taci gaba da Aikin ta,

Yana hango Fitowar su yana daga saman gidan nashi idanun shi a kafe akanta tana tafiyar ta a natse jikin ta na juyawa kamar tarwad'a

Gaba daya ta gama wucewa da imanin shi ya kasa koda kifta ida nunshi akan ta har saida ta shiga motar yayi Ajiyar zuciya kafin ya janyo wayar shi yayi dialing numbar Ahmed,

Yana d'auka yace "where are you? Muryar shi can kasa Alamar cike yake da kasala,
" oga ina gida yanzu dai zamuje gidan momy ne mu gaishe ta ta ce inkai mata Yasmin,

"Wait for me nima gidan zanje, yafada yana mai mikewa, shiru Ahmed yayi domin yasan Akwai matsala yanzu kam idan taji zasu tafi tareda oga,

Juyowa yayi tareda kallon ta tana wasa da yaron " kanwata tafiyar mu ta canja salo fa tareda oga zamu tafi bari in dakko babbar mota a ciki,

Ya fada yana fitowa batareda yaji Amsar ta ba, katuwar Hummer jeep din shi Army green ya fito da ita ya faka tareda jiran Fitowar oga kwata kwata,

Cikin shigar kana nan kaya kamar zashi training ya fito tree quarter da kuma wata riga mai hula kalar kaki ya bude gaban motar ya shiga saida suka fito yayi mata horn ta fito kamar bataso ta fara takowa kanta a kasa ta bude bayan motar ta shiga,

Yi yayi kamar bai sanda zuwan ta ba saida Ahmed ya tayar da mota yace "Yasmin ga oga baki gaishe shiba,

" dago kanta tayi cikin shirin daukar magana ta watsa mai harara kafin tace "la shine ogan naku? Wallahi da naga yana kwaso mata n.......

"Yasmin shine. Ahmed ya tari numfashin ta da sauri kafin ya kunna radion motar yasaka wani kida mai taushi na wakar Angel of my life,

Janyo earpiece tayi ta sanya a kunnen ta tareda sanya best wakar da take so ta Ado gwanja wakar shi ta a hayye matan Arewa kun kai mata,

Har wani lumshe idanun ta takeyi tsabar jin dad'in wakar shi kuwa tunda tayi magana yaji muryar ta mai zaki ya lumshe idanun shi batareda yaji kalamin ta ba,

Wakar dake tashi ce a cikin motar ga kamshin turarukan su ga na motar sai jin shi yake cikin wani irin yanayi mai wuyar fassara,

Auwal wasan shi kawai yakeyi a gefen ta hannun shi rike da lollipop yana sha,

Saida ya tsaya kofar tafkeken gate din yayi horn sojojin suka wangale mai ya sa hancin ta,

Suka rugo tareda bude mai motar ya fito fuskar shi a daure ya basu umarnin su koma bakin Aikin su kai tsaye ya koma gefen da zata fito ya tsaya ya kare ta daga kallon masu gadin nashi,

Saida tayi gaba dauke da yaronta ta bi bayanta tareda Ahmed wani irin kallo yake binta dashi mai cike da ma'anoni kala kala,

Kamar koda yaushe dattijuwar na zaune akasan Capet din ta dora hannun ta akan tun tun din dake kasan hannun ta rike da carbi gefen ta zuby ce zaune kanta akasa,

Gaban ta kayan motsa baki ne a Jere, tun Shigowar shi falon gaban zuby ya fadi shi kuwa hade fuskar shi yayi tareda bata rai sosai,

Yasmin kuwa baki ta saki hango wannan mayyar wato uwar shi ma tasan d'an iska ne tunda ga karuwan har cikin gidan su,

"Abin nashi Ashe har da licence ta furta a fili kuma yajita sarai, fuska Hajiya ta saki sosai ganin Yasmin,

" a maraba da Yata Fatima Lale marhabin, ta fada cikin jin dadi yau ga Fatima kai Amadu ka cika Alkawari,

Matsawa tayi kusa da ita tareda zubewa ta gaisheta cike da kunya, shi kuwa gefen zuby ya nufa fuska a matse "what the hell, why did you come hare?
Chapter 9 · 0% Book details