← Book details Bariki Auren Soja Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 66

Sashe 23

Bariki Auren Soja Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Nidai zantafi kaga kusan sha biyu, riko ta yayi suka sakko bayan ya saka y'ar Riga, "muje inraka ki kafin indawo inyi wanka,

Karamin gyalenta ta yafa tareda daukar wayarta yana biye da ita Kamar ya riketa a gidan yakeji, har kofar gidan ya rakata tashige cikin sauri ta kulle kofar sannan ya wuce, saida ta leka dakin Aunty taga tana baccin ta hankali kwance, sannan ta wuce dakinta saida ta Kara kitmtsa kanta ta cire rigar shi mai she gen kamshin jikinshi Kamar yana wurin ta sunsuna tareda lumshe ido ta ninke ta Ajiye a kayanta,

Katifa ta haye tareda janyo wayarta ta Dora saman kirjinta ta runtse idanun ta tana tuno Abinda ya faru moment ago "MA karshen Y'an iska Wallahi bata taba ganin iskanci irin nashi ba,

Wani irin yamm taji tsigar jikin ta na tashi da ta tuno da yanda yake lasar kirjinta Kamar wata Zuma kai yau ta hadu da namijin Zuma,

Shima MA haka ya kasance bayan yayi wanka ya Kara dumama Abincin da ta dafamai ya zsuna yaci sosai badon yunwaba saidon hannun da ya girka shi saida ya wanke baki kafin ya jefa sweet mai tsada da kamshi ya haye gado wayar shi ya janyo ya duba time,

Runtse idanu yayi yanajin Kamar yaje ya dawo da ita murmushi yake na farinciki da Kuma shauki, Kasa daurewa yayi ya Kira layinta,

Ba bata lokaci ta daga, "hmm yace na dogon lokaci ya Kasa cewa komai sai fitar numfashin ta kawai yake saurara,

"Baby am speechless bansan mezan fada ba, kingama da zuciya ta kintafi da natsuwa ta I can't sleep today kitayani hira kozan samu natsuwa,

Narkewa takarayi akan filo tareda kwanciya lub ta rike wayar gam Kamar shine, "ina ganin komai baby Kamar indawo da hannun ago go baya nakeji,

"Ki soni don Allah bazan iya hakuri da rashin kiba ke rabin jikina ce ki soni baby please kisoni, ya mai maita yafi cikin kwando, tayi Ajiyar zuciya tareda sharce hawaye masu zafi,

"Kadaina maganar so Aure zan..... "Please kidaina zancen nan karki samun ciwon zuciya yanzu Aure Hmm in my foot Wallahi ba wannan limamin a kaduna da zai daura Aurenki da wani babu shi, ko abani ke ko indauke ki muyi rayuwar da kowa bazaiji dadinta ba ke tawa ce koma waye ya cire idon shi akan matata,

"D'an uwana ne yanada ikon Aurar dani ga koma waye bare shi karan kanshi ne zai.... Stop YASMIN banason ji karkisa inyi Abinda banyi niyya ba,

Saida safe kawai yace tareda katse kiran zuciyar shi na zafi, Wato YASMIN d'an uwanki kikeso har kike iya fada min Baki damu da halinda zuciya ta ke ciki ba, ko Y'an biyu ne ku sai ya bar minke baby, ya furta tareda yin jifa da wayar shi ya dafe kai,

A ranar Kasa bacci yayi har saida Asuba tayi ya tashi yayi salla kafin yayi wanka yafita wurin da yake motsa jiki,
Ko kiranta baiyiba yau ya shirya motocin shi suka iso ya wuce bakin aiki cike da haiba da kwajini ga kaki na mugun karbar shi dole maza su girgiza idan ya fito

***************
Karfe goma YASMIN ta hada kayan ta domin ismail zai zo ya kaita gida duk ta damu da rashin kiranta da baiyi ba ga shi baxata iya kiranshi ba itama haka har ismail yazo suka wuce, saida suka kai kofar gidan su kafin ya fara yimata magana don yau komai bai ce mata ba tunda suka fito,
"Yasmin Akwai matsala fa, ta kalle shi " mai yafaru? Ki shiga baba na ma na nan yazo, zakiji koma Meye,

Saidai kisani ina sonki sosai YASMIN, kanta ya d'aure haka ta fita jikinta yayi sanyi ta shiga gidan shi ya kwashe mata kayan ta ya shiga dasu,

Muryar baba Zango tafara ji yanata ruwan fada domin shi yafi baban su zafi, "Yaya bai isaba mu zai mayar mutanen banza?

"Mamuda babu ruwanka yarodai ya fadi ra ayinshi don haka dole mubi don iya biyayya yayi mana,
"Yaya Wallahi kai ke biye mai don haka babu ruwana bada miyau naba,

"Dama ai bamusa miyanka ba nidai don kana uban Yasmin ne nafada maka karkaji daga baya,

Gaishe su tayi bayan tayi sallama ta Kuma ji duk sharhin su Amma bata kamo bakin zaren ba,
Ta gaida baban Zango yanda suke kiran kanin mahaifin nasu,

"Mama na kin iso? Ya maryamar da yarinyar ta, ? Lfy lau baba yasu innan Zango? Duk suna Lafiya mama na ismail ya shigo baba ya kirashi,

"Kaje ku gama magana a tsakanin ku Gobe insha Allahu zamu kammala komai kaji karka damu,

Dakin ta yasameta har ta cire hijabin jikinta zani ne single da Riga play tayi kyau sosai duk da ba make up tayi matukar haskawa,

Zama yayi tareda zuba mata ido "Fatima ya Kira real sunan ta yau tasan akwai magana, um ta zauna tareda zuba mai idanun ta tana sauraren shi,

"Kiyi hakuri da Abinda zanfada miki, yaja numfashi ya fara magana, " lokacin da narasa maryam mun hadu da wata yarinya a wurin Aikin mu gaskiya bazan boye miki ba naso Zainab sosai kafin mahaifin ta ya yi mata miji ya Auradda ita na dauki dangana a lokacin na Kuma y'arda da kaddara nasan Allah da ya hana ni Auren maryam da Zainab shi zai yaye mun soyayyar su cikin zuciya ta,

Cikin satin da ya wuce kwatsam na samu labarin a she sabodani taki yarda Sam tayi zaman Auren ta har mijin ya sauwake mata, ina wurin aiki ta sameni da kuka sosai akan idan ban Aure ta ba zata kashe kanta,

Maganar gaskiya YASMIN ina son Zainab Kuma nayi mata Alkawarin Aure, ina sonku duka don haka na fadawa baba zan hadaku baki daya ina fatan zaki bani Goyon baya kanwata,?

Tunda yafara maganar ta zuba Mai idanu tareda yimai wani irin mugun kallon Kama raina min wayau,

"Yaya kenan to ni na hakura kaje ka Aureta ba laifi Wallahi na yafe ka tafi kawai, wani irin kallon ta yayi "karkiyi mun haka YASMIN na kwallafa rai akanki don Allah karkisa in zaba tsakanin ku bazan iya barin kowacce ba a cikin ku,

"Wallahi sai ka Barni don bazan y'arda ka hadani da wata ba tun yanzu ni Yasmin kishiya a rana daya ina Wallahi kaje kawai na hakura,

Jiyo maganar su baba ne yasa sukayo waje, da sauri, mama ma tafito rike da ludayi a hannu jin jiniya ta cika ko ina a Unguwar baba ya sharce gumi ya kalli kanin shi,

Mamuda ina ganin barayin da akace suna Unguwar nan da gaskiya ne watannin baya sojoji Kamar yaki kullum cikin Unguwar nan kaga yau ma sundawo Allah ya jishe mu Alkhairi,......... 🖊️

*ai ina ganin tawagar su maman kids ne sukazo artabu ni nayi nan ba ruwana fan's love you All'*

*Matar soja*
[8/30, 2:56 PM] Feenerh Wrtr: PROFICIENT WRITERS ASSOCIATION

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

FACEBOOK: https://mobile.facebook.com'/groups/2455147078097572/

TWITTER: https://twitter.come m/pro__writers?s=09

🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
*BARIKI*
_Auren Soja_
🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

_written by FENERH_
Maman Ammar

*Dedicated to*
Fiddausi mainasara feby

*NA sadaukar da wannan shafin gareku my people kungiya mai tarin Albarka da dumbin hadin kai proficient writer's ina Alfahari daku Allah yakara hada kanmu Allah ya baku lfy mutane na Nabeela sarauniya tareda MAMAN Mamy SHALELEN proficient*
*Ammyn khyarat*
*Rukayyat Ikra*
*khadeja Auta*
*baba sadeq*
*nusee y'ar Amana*
*Ummu najma*
*Aisha Alto*
*Tareda kai bawan zage zagi Yusuf Indabo*

*jinjina agareku baki daya Allah ya kiyaye ku da ga sharrin mahassada ya Kara muku zakin hannu da kaifin kwakwal wa*

27&28

Wani irin trumbling cikinta yayi saboda tsabar tsorata ta zaro idanun ta waje tareda dafe kirji, "nashiga uku ta fada a fili duk suka zuba mata ido'

"Meye najin tsoro YASMIN bayan gani anan, ismail yafada ta zabga mai wani irin kallon bakasan me kakeyi ba ya nufi hanyar waje a rude domin tabbatar wa idanun ta,

Take mata baya su baba sukayi domin suma duk suna son ganin meke faruwa a wajen, baba da y'ar butar shi ya fita a hannu ta Alwala,

Kusan suman tsaye tayi domin motocine sunkai kusan goma a jere sai katuwar hummer dake tsakiya duk kalar Army sauran duka hilux ne,

Tunfitowar ta ya hangota tareda yin Ajiyar zuciya yana kare mata kallo tayi mai masifar kyau da shigar native wear din saidai ranshi yabaci data fito ba hijabi ga kirjinta sun kunburo sosai don Abinda yafara kallo kenan Ajikinta,

Kallon irin Yaran da yakwaso yayi yabasu umarnin komawa cikin motocin su don duk sunfito sungama zagaye wurin gaba daya da bindigogi,

Takowa yafarayi cikin takun girma da Kuma haiba lokacinda su baba ke tsaya suna kallon ina wa innan mala I kun duniyar zasuje? baban Zango kam kanshi kawai ya leko daga waje,

Ta Riga ta gama sumewa da tsoro jin kawai tayi anrungume ta tareda yin Ajiyar zuciya,

Saurin dawowa tayi daga doguwar sumar tsayen da tayi ta yi saurin ja baya tareda sanya kukan rashin mafita musamman data kalli gefen da baba ke tsaye ga butar hannun shi ta fadi duk ta tsiyaye sai ismail da idanun shi suka juya tsabar kishin ganin wani kato rungume da Matar. Da zai Aura,

Kara matsota yayi kamar zai shige jikinta ga wani kallo da yake mata kamar zai lashe ta tsabar so "baby meyasa kika wuce baki fada min ba?

"Nifa da nayi fushine Kuma zuciyata taki y'arda da hakan ina bakin aiki naji bazan iya hakurin rashin kiba dole na koma gida nasamu Wai kinyo nan shiyasa na biyoki, "baby I can't indure nakasa daurewa indai akanki ne zan iya yin komai baby I can do anything bcous of you,

Ai YASMIN tashin hankalinda ta shiga bai misaltuwa yau tashiga uku da baba yau MA ya gama kasheta yau ta gama yawo,

Ai tuni su baba sunkoma cikin gida har ismail ma sun barsu a wurin Sam tarasa madafa sai kukan da ya Kara kufce mata ta kalleshi hawaye share share ta ce "meyasa baka tunanin Abinda zaije ya dawo meyasa kake Abu ba tunani me yasa baka Abu cikin hankali?
Chapter 23 · 0% Book details