← Book details Bariki Auren Soja Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 66

Sashe 44

Bariki Auren Soja Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jindadin Abin takeyi sosai kamar karya cire lips dinshi a bakinta jin test dinsu takeyi sosai sai kara rikoshi takeyi tana kara haukata shi, ganin yana kokarin janyewa daga jikinta yasa jikinta na rawa ta tashi tareda maida kofar ta rufe gam tadawo ta fara cire kayan jikinta don mugun bukatar Abin takeyi tarasa dalilin hakan zuba mata ido yayi cikeda mamakin ta don bata taba nunsmai tana bukatar Abun ba sai yau saidai shi yayita kwakwa, fadomai tayi yayi saurin rikota "oh baby kibi a hankali mana cikina karki mun asara, ko jinshi batayi ta dora hannun ta saman wandonshi saida yayi y'ar kara ta balle belt din tareda sanya hannu ta bude rigar jikinshi yana taimaka mata tuni ta zautar dashi baijin zai iya barin wannan garabasa ta wuceshi

Tuni ya fita zakewa suka fara tumurmusa juna cikeda kewar juna da sukayi, karar wayarshi ya dawo dashi daga duniyar tsotse tsotsen da yatafi dakyar yake iya bude idanun shi ya daga wayar saida ya gama sauraren su kafin ya mike ya ware idanun shi oh my god ya fada da kyar sannan ya Ajiye wayar , dakyar ya bude bakin shi "baby zanje office am sorry I will be back for you get ready for me in the night kintayar min da kwadayi ga shi sunkira ni a wurin aiki, cikin sauri ya mayarda kayan shi ya tsuguna tareda manna mata kiss take care of my baby, ya fita da Sauri tabi bayanshi da kallo,

Tashi tayi tana murmushi tareda jin soyayyar shi na da da karuwa koda yaushe cikin zuciyar ta shi na daban ne a cikin maza tana son Muhammad Abdullah so mai tsanani tanajin kishin shi gani take har gobe mata nabi mata miji,

Baisamu dawowa ba saidai kiranta yayi yabata hakuri saboda soja baida hutu koda yaushe yana bakin Aikin shi, duk da yazo ya huta ne amma bazai taba hutun ba sai ranarda yayi ritaya,
Da safe su mama hindatu da Aunty maryam da kuma wasu Y'an Uwan mama suka zo domin rakata gidan mijinta baba yace ba wani taro da za ayi ta bari idan ta haihu sai ayi taron tunda ga ciki nan, saidai uban gayya tuni ya shirya kwarya kwaryar liyafa a officers mess domin Abokan Aikin shi yace maza zalla ne kawai zasu hada barbecue domin tayashi murnar Aure da kuma samun karuwa,

Cikin sirri yasa aka kwashe kayan da akayiwa yasmin yace akaiwa Aunty maryam mama kawai ta sani da mama hindatu don gudun fadan baba, itadai Aunty maryam tayi farin ciki sosai domin ko a Aurenta bata samu wannan dama ba, kayan kitchen dinta ma da suka kai mata ajiyewa akayi domin ba abinda ba a zuba a yafjeken gidan da suka kira da Aljannar duniya nera tayi kuka gidane d'an karere ga katon garden da yaji kayan marmari Kala Kala gefen shi da sweeming pool mai burgewa, furniture's din kuwa set ne na royal Italians masu shegen kyau masu ruwan Zuma da fari gida dai Masha Allah , tuni sunkai mata kayanta gidan harma da motocin hawan ta,

Washe gari karfe biyu baba yasa ta shirya da kanshi ya dauketa domin yimata rakiya dakin mijin nata domin ya nemi Alfarmar yanason tazo da wuri akwai party da aka hada mai,
Tasha nasihohi masu karya zuciya da shiga jiki daga gefen mama harma su baban da suka zaunarda ita, su mama sun mata Nasiha mai Amfani sosai saida tayi kuka Aunty tace sai sun hadu a BARIKI yanzu ta zama matar manya gidan ta shigasaida izini saboda sojojin dake kofar gate dinta, zuciyar ta ta karye sosai ganin da gaske shikenan yau zata koma gidan Muhammad gaba daya,

Hawaye ta share tareda yin shiru, komai nata yazo daban da na mutane Aure ba shiri tarewa da ciki kuma ba taro, ba kuma mai rakata, haka suka isa gidan nata tafkeke, shi kanshi baba ya tsorata da ganin irin wannan katon gidan yanzu a nan y'ar shi zata zauna, Allah mai iko da kuma girma , bude musu katon gate din sojojin sukayi baba ya shiga da motarshi suka fito wata dattijuwa ce ta fito tana musu Maraba da isowa tayi musu jagora saida ta sadasu da falon tace. "Sannu da zuwa uwar gida Sannu da zuwa gidan ki Allah ya kade fitina, fitowar su Aunty Halima dukan su suka fara mata Maraba da Amaryar baban hajiya yaudai zamu ganki ko, dukarda kanta tayi tareda kara janyo hijabin ta, har kasa suka duka suka kara gaida baba tareda godiya ya Dan ka musu Amanar ta tareda sa Albarka ya tafi, sunata mai godiya,

Kamar ta riko shi takeji tana ganin ya fita tasa kuka shikenan itama An sallame ta daga yau tabar gidan su, su Aunty suka ce tayi hakuri ta tashi ga mai make up tana jira za aje partyn yanzu bata da zabi haka ta mike suka Nuna mata wani daki ta shiga saida aka hada mata ruwa tayi wanka tareda yin Alwala ta fito saida tayi LA asar sannan ta zauna aka fara tsantsara mata make up,

Wane irin party MA ke shiryawa tana da ciki meye na wani taro itadai batasoba gaskiya gashi tun shekaran jiya da yazo bata bata kuma ganin shiba saidai waya a gurguje,
Wani farin less suka bata Riga da zani na buba suka daura mata zani a saman rigar tareda daura mata wani head mai golden yana sheki suka Ajiye mata poss da takalmi mai tsini sai a shoken kalar head dinta tayi kyau fiyeda tunani, suka rika Masha Allah baban hajiya ya iya zabe gaskiya tubarkallah sai kunya take ji yanda suke kod'ata,

Kiranshi sukayi akan sun shiryata, yace motoci nanan a waje su fito harda su zasu iya zuwa don yaga Y'an gayyar sodi ma da ba gayyace suba duk sun shirya zuwa kwasar gara, domin na hango Aisha dahiru da katuwar Jakarta tareda Ummu jidda da ta kwashi katon no respect gudun raini a hankali nafara ankarewa gaba daya ma BARIKI fan's sun cika gidan harda su hussy Ali gasu maryam dina andauki wanka nace to nima dole in dauki nawa Gayun muje kwasar gara........ 🖊

Mu cigaba da hakuri da juna my fans muna nan zuwa inda mukeson mu isa da ikon Allah komai yayi farko zaiyi karshe,

*Matar Soja*
[9/16, 10:05 PM] Asli Smasher 💕: (¯`*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿`°¤,¸.•*´¯)

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

FACEBOOK: https://mobile.facebook.com'/groups/2455147078097572/

TWITTER: https://twitter.come m/pro__writers?s=09

🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
*BARIKI*
_Auren Soja_
🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

Written by FENERH

*Dedicated to*
Fiddausi mainasara feby

51&52

Motocine guda shida aka ajiye musu sababbi dal suna sheki ta tsakiyar tasha Adon balloon kana gani Kasan motar AMARYA ce ta fito tareda su Aunty Halima driver ne ya bude mata ta shiga suka shiga sauran motocin, BARIKI suka nufa basu tsaya ko ina ba sai 2 batallion officers mess, tundaga titin farko zakasan an kawata wurin sosai ga sojoji tundaga farko baka ganin karshen su kowane sanyeda ceremonial dress sunyi matukar haska wurin ga fulawowi da aka watsa saman red carpet suna tsayawa aka bude mata tafito wasu Y'an mata ne suka jero suna paret sanye da ceremonial dress na mata mai sket su goma, suka sata a tsakiyarsu gaba daya tafara rudewa don bata taba tunanin haka taron zai Kasan ceba, ko ina shi uban gayyar yake oho? Fushi ma takeyi dashi tunda rabon da ta sanya shi a ido tun ranarda yazo aka kirashi saidai yakirata yaji lafiyar babyn shi ya kashe that's means ta tashi aiki ita tunda yasamu ciki a jikinta tana haihuwa kuma shikenan,

Hango shi tayi yana takowa cikin nashi ceremonial dress din da yaji stars da igiyoyi dauke kuma da aninan shi da zasu Nuna maka he is the boss wata sandar girma ce a hannun shi yana dogarawa yayi masifar kyau tundaga nesa suka zubawa juna idanu yana mai jin farin cikin ganin ta gashi ta fito kamar wata tauraruwa karasowa yayi, ta dauke kanta tareda hade rai ya na zuwa ya rungume ta batareda ya damu da mutanen dake wurin ba ya dora hannun shi a marar ta "ya baby na? Rage murya tayi a hankali tareda cewa "ni nazama hoto ai yanzu wallahi a matsa inyi flushing din shi inga tsiya, "what me kikace? Tayi mai banza ya matse fuska sosai ya riko hannun ta suka shiga ana take musu baya ga masu hotuna tuni sun fara Aikin su,

A she kallo na ciki don Fadin kawatuwar wurin kawai zai cinye fejin yau saidai BARIKI fan's zasu baku labarin haduwar wurin ba Abinda ya burgeta irin ganin y'ar uwarta datayi a wurin ga yaronta da ke cikin nashi ceremonial dress din na yara harma da hula yayi kyau da y'ar karamar pistol ta wasa a soke a Aljihun shi, wurin zaman su suka nufa batareda ya kuma ce mata komai ba don yaji mai tafada, ga Army bands sai sakin kida sukeyi da kuma busa wurin ya tara manyan sojoji da matayen su Abokan Aikin shi gefe daya matan NAOWAS ne wato NIGERIA ARMY OFFICER'S WIFE ASSOCIATION ne suncian anko mai dauke da tanbarin gauraka Abin ba a cewa komai Abin ya mugun kawatar da ita su Aunty Halima ma gefe guda aka ware musu man yan yayyi Aunty maryam ta jone cikin su, aka fara gudanar da taro party ne mai Aji ba wani hayaniya harka ce ta girma sai masu raba drinks da kayan motsa baki keta kai da kawowa snacks ne da su namomi Kala Kala kawai kake gani, tuni na hango Ummu jidda na boye kularda ta yo guzuri don zuba rice sai yakasan ce bikin ba na rice bane,
Chapter 44 · 0% Book details