← Book details Bariki Auren Soja Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 66

Sashe 48

Bariki Auren Soja Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk ya rura mata jiki, haka suka farantama juna duk da kasanta na neman agajin gaggawa haka ta sake mai ya murjeta son ranshi sai la asar sukayi wanka suka fito domin tafiya, a falon suka samesu itada Y'an matan ta, "ai har cigiya na bayar ko kun wuce a she kuna ciki, itadai Yasmin kunya rufeta tayi ta dukar da kanta kasa "ina hutawa ne hajiyata gobe fa zankoma yanzu ma idan na shiga gida sai gobe idan zantafi zanfito, yafada ko a jikin shi, "to naji mara kunya a sauka Lafiya, shiga daki tayi ta fito mata da zumar ta da turarukan wuta ta hado mata tabawa cikin Y'an matan suka kai musu mota, ta rakasu da Addu a suka tafi cikeda farin ciki, shi ya tuka motar har suka isa gida Lafiya taso ya kaita gida yaki yace yaushe tabar gidan, ta kuma so ya kaita BARIKI yaki yace basai tajeba ga gidan ta, Shiru kawai tayi mai ita Kadai tasan me ta shirya bayan tafiyar shi,

A daren ji sukayi kamar kar gari ya waye saboda kar su rabu sun raya wannan daren hade da taimakon magun gunan da hajiya ta bata shi kanshi ya haukace da jin wani sabon gardi da galmi tayi mugun laushi koda Asuba saida ya kuma lallabe ta kafin yayi wanka, cikin kakin shi ya shirya tareda baza kamshi ya fito a sojan shi, karfe bakwai Ahmad yazo , rungume shi tayi tsam taji wasu irin hawaye masu zafi nabin kuncin ta tuni tafara jan sheshsheka ya tallsbota sosai a jikin shi, "karki karya min guiwa madam kiyimin Addu a sannan ki kulamin da baby na please take care of your self and my baby bakuda matsalar kudi kunada komai a hannun ki inkina son Aike you can send those soldiers, ya duka yabata kiss a cikin ta kafin ya bata a lips dinta saida ya lashe hawayen fuskar ta tas sannan ya saketa tareda yin dariya "haba matar soja ki zama jaruma mana yanzu idan baby yazo yaga zantafi yaga Maman shi na kuka Shima kukan zaiyi kenan,

Murmushi tayi tareda cewa "kaje baban Auwal na jiranka Allah ya kare mana ku, "Amen sweet wife Allah yasadsmu da Alkhairi, bata iya rakashi ba saidai yana fita tasa kuka mai sauti ta koma dakin sai taji gidan ya mata mugun girma yanzu dama ganin shi tare da ita yasa Sam bata ganin girman gidan, komawa tayi tareda kunna wayar ta tafara chart a grp domin rage zaman Kadai ci,

A haka Rayuwa taci gaba da tafiya yanzu tana samun shi akoda yaushe idan ya kirata saidai kullum Kara tuna mata yake ta musu Addu a, tayi matukar kewarshi Shima haka ne a gefen shi saidai aiki bazai barshi yazo ba, a cikin wata daya duk sati suna haduwa a gidan su itada y'ar uwar ta sometimes ma tare suke zuwa gidan hajiya ta jajje gidan Y'an uwanshi dake nan kaduna suma sukanzo mata, ga cikin ta baya bata matsala Allah ya bata ciki mai saukin gaske

Bayan wata uku itada Oga saidai waya ko video call duk lokacinda yayi video call da ita sai ya rikice mata ga cikin ta ya fara bayyana sai budewa takeyi tana Kara haskawa batada damuwar komai saita rashin mijinta, yau ma da sukayi waya rigima tasa mai ita dai Tanason ganin shi, dariya yayi "madam kina tunanin kinfini damuwa ne? Kawai ina matsewa ne ji nake ko yanzu kamar in janyoki a wayar nan inji ni a jikin ki, kullum hadarin wurin nan karuwa yakeyi duk lokacinda muke tunanin Abin yayi sauki sai su kuma bullo mana ta wani wurin don haka ko zamu samu shigowa sai karshen watan nan please take care of your self and my baby kice dadyn ta na missing dinta da Maman ta,

Tarasa dalilin da take yawan jin faduwar gaba gashi ya hanata zuwa gida ko zata rage damuwar sai yawan mafarkai da kuma take yi akan mijin ta kullum sai ta kira shi taji ko Lafiya yake yace mata kalau yake tadai Kara Addu a akan Wanda sukeyi, ganin hankalin ta bai kwanta ba Yau ta shirya ta tafi gidan hajiya tareda fada mata Abinda takeji, "nima Fatima kullum hankali na ba akwance yake ba idan na kirashi zai ce min kalau suke ,

A gidan hajiya ta kwana a ranar don bazata iya komawa gidan ba gaskiya hajiya sai Kara kwantar mata da hankali takeyi, da sassafe tana zaune akan daddumar salla tana lazimi wayarta tayi Kara hajiya ce ta mika mata gashi ana kiranki, saida gabanta ya fadi kira da sassafe waye wannan ganin bakuwar numba yasa gabanta faduwa, taga bakuwar numba, dauka tayi kawai tareda hello, "please am I talking to Mrs Muhammad Abdullah? Gaban ta ya mugun faduwa tareda cire wayar akunnen ta domin dagaji ba Alkhairi za a fada mata ba ta saki wayar hajiya dataga haka ta taso tareda daukar wayar jin Ana kan magana, tuni ta sulale kasa tayi zaman yan bori, jin salatin hajiya yasa ta dawo hankalinta,

"Ba Abinda ya sameshi ko hajiya kifadamin Lafiya lau mijina yake kifadamin ba Abinda zai faru dashi yafada min zai dawo ya gan mu nida babyn shi, sambatu kawai take yi duk ta rude , hajiya tace shirya muje Asibiti mijin ki na can 44 ance Y'an fashi sun kawo musu hari wasu sun mutu tashi muje inga halin da yake ciki Fatima, ta fada jikinta na rawa....... 🖊

*Matar Soja*
[9/20, 11:17 AM] Asli Smasher 💕: (¯`*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿`°¤,¸.•*´¯)

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

FACEBOOK: https://mobile.facebook.com'/groups/2455147078097572/

TWITTER: https://twitter.come m/pro__writers?s=09
🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
*BARIKI*
_Auren Soja_
🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

Written by FENERH

*Dedicated to*
Fiddausi mainasara feby

55&56

A rude ta mike ko canja kayan baccin ma bataji zata iya yiba, dama da katon hijabi a jikinta suka fito harabar gidan motar ts suka shiga gaba daya ta gama rudewa ga wani irin juyi da cikin ta keyi, sai salati kawai hajiya keyi, ikon Allah ya kaisu Asibitin, hajiya tace yanzu ki kira mana number Ahmad muji suna ina, ? Anan taji hankalinta ya kuma tashi tunawa da Ahmad da tayi yakamata a ce shiya kirata ba wani ba Allah ya rufa musu Asiri kuwa,

Tunda daga bakin gate suka fara tanbayar sojojin da aka kawo daga birnin gwari a yau ne ko jiya? Wani yace "oh MG Abdullah suna operation Lafiya dole word madam, ya nuna mata wajen gaba daya basa iya cewa komai karfin hali kawai takeyi ga hajiya ma gaba daya ta gama rudewa, a zaune suka samu Ahmad hannun shi nannade da bandages ga goshin shima da plasta tayi saurin karasawa wurin shi jikinta na rawa, duk ta rikice hajiya ce tafara cewa "Ahmadu ina baban nawa,? "Mama meyasa kukazo waya fada muku? "Wani yakirani a waya yanzu, yasmin ta bashi Amsa, "Oga na emagency ya samu rauni sosai akai da hannu koda muka iso nan baima sani ba zasuyi mai xray kafin musan koda wani raunin, kuka yasmin tasa mai cin zuciya tareda rungume hajiya da itama karfin hali kawai takeyi, "meyafaru daku ne Ahmadu,? "Wallahi mama tunfarkon watan nan sai ankawo mana hari Allah baya basu sa'a jiya kawai sunyi Ambushed din mune amma munkashe su sosai Oga yayi kokari sosai wajen fada dasu gashi ba muda makamin da sukeda shi, duk da yaji rauni haka yake fighting dinsu sai daga bayane ma muka gane yaji rauni bayan mun samu nasara akansu munkama wasu wasu sungudu sun kashe mana sojoji shida a ciki harda Oga umar makocina,

Wani irin kuka ta sa Mai Kara "yanzu bazamu ganshi ba? "Sai sun kaishi resting room in sun gama dubashi, kutaya shi da Addu a kawai mama, "innalillahi wa inna ilaihirraji un, hajiya keta mai maitawa, wuri ta samu ta zauna Yasmin ma ta zauna har wani jiri takeji yana neman kadata, yanzu shikenan baban Amla ya rasu wayyo duniya duk da batada halin da mijin nata yake cikiba Amma ta mugun tausayawa Maman Amla, matsowa yayi yace ta aramai wayarta zai kira maryam,

Shiya fada mata halin da ake ciki tareda bata umarnin zuwa da breakfast saboda su hajiya , hankalin maryam ma yatashi ta kira su baba ta fada musu suma, kafin kice me Asibiti ya cika taf da Y'an uwa da abokan arziki harda Y'an Uwan shi duk sunzo kowa sai Addu ar Allah yasa suga Alkhairi sukeyi, yasmin dai tayi kuka hartaba uku lada sai lallashin ta akeyi "kidaina kukan nan haka kinga bake Kadai bace ga tea an hada miki kisha karki fadi kijama mutane wata damuwar,

Hajiya keta lallashin ta mama ce tace barta hajiya tunda batada hankali tazama yare bazaki tayashi da Addu a ba zaki zauna kina kuka ko shine zaisa ya warke ko kuma kaddarar shi ta canja, "bita a hankali Saude, baba yafada yana maijin tausayin y'ar tashi, wasa wasa har karfe goma ba su sashi a idoba ga kukan ta yaki tsayawa kowa dake wurin ita yake tausayawa domin kukanta irin mai ban tausayin nan ne, jiya ta gama waya dashi yau akirata ya na cikin mugun hali ba Abinda take tunawa irin Alkawuran da yake mata kwanan nan "baby ina dawowa zamuje muma baby na shopping baby yafara kicking? Kullum maganarshi kenan babyn shi da kuma kewar ta,

Shafo cikin tayi tareda runtse idanun ta tayi magana a cikin zuciyarta "insha Allahu babanka zai tashi ya zai yi wasa dakai my baby, duk hankalin su yagama tashi ganin har shabiyu ba wani magana sai likitoci ke fita da shiga masu kaki, sai kusan karfe daya suka kira Ahmad, yashiga saida ya dauki lokaci ya fito ta tashi da Sauri ta nufeshi "Lafiya baban Auwal? "Alhmdulillah kuzo keda mama ku ganshi basa bari mutane na shiga ciki ko yanzu na rokesu ne da kyar, cikin sauri ta wuce ko hajiya bata jiraba, saidai tundaga farkon dakin jikinta yayi mugun sanyi ganin sojoji Kala Kala a jere kowane da tashi matsalar wani ba hannu wasu ba kafafu wasu kuma bama Susan inda kansu yakeba,
Chapter 48 · 0% Book details