← Book details Bariki Auren Soja Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 66

Sashe 64

Bariki Auren Soja Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Jinjinar bangirma zuwa gareki zainab Adam maman jibiril makociyata uwar gida a wurin lcpl Muhammad gombe sgnt to be insha Allah very soon Allah yakaresu a duk inda suke ina yinki Allah ya biyaki ladan ruwan da kike zubo min daga sama🙄

"masoya munzo gangara da izinin Ubangiji komai yayi farko zaiyi karshe zankammala labarin Auren Soja soon ina matukar godiya da Addu oin ku Allah yasaka da Alkhairi Addu ar ku nada matukar tasiri A Rayuwa ta ina godiya Allah yabar kauna inayin ku fisabillahi,

*Matar Soja*
[10/11, 7:22 PM] Asli Smasher 💕: (¯`*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿`°¤,¸.•*´¯)

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

FACEBOOK: https://mobile.facebook.com'/groups/2455147078097572/

TWITTER: https://twitter.come m/pro__writers?s=09
🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
*BARIKI*
_Auren Soja_
🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

Written by FENERH

*Dedicated to*
Fiddausi mainasara feby

69&70➡🔚

Alhmdulillah Anwatse taro lafiya yarage daga mai jego sai su mama hindatu da hajiya Aunty maryam ma ta nufi nata gidan ba karamin Alkhairi tasamu ba a wannan haihuwar daga Y'an uwa da Abokan arziki
Yaranta na samun kulawa sosai, mama hindatu taso tafiya da Yasmin gida kodan rawar kafar da taga MA nayi kar suje su cutar da yara tunda Yasmin din ma batawa kanta fada Amma ya murzawa idon shi toka yace Sam ba inda za akaima i mata da yara dole suka hakura don har su baba aka fadama suyi mai magana baban zango ya hau fada "hindatu Al Ada ko addini kubar yarinya a dakin mijinta kici gaba da kula da ita in ta cika sati biyu ki tattaro kidawo tunda uwar mijinta na nan kuma tanasa ido, baba ma ya yarda da maganar kanin shi dole hakan suka hakura, tuni sun fara tsumata domin gyara hanyar da ya'ya uku suka fasa, gyara suke mata na musamman harda hajiya ta gayyato wata y'ar Niger tazo ta fara gyara ta, su hajiya sun sami lafiya domin sati daya da suna MA yaje jaji yin wani aiki na kusan wata daya, ita kanta Yasmin taji dadin tafiyar don mugun tausayi yake bata don tasan halin kayanta mayenta ne idan suna kusa da juna baya iya hakuri, don koranar da zaitafi saida ya latseta ciki da waje kafin ya wuce,

Sati biyu mama hindatu ta shirya komawa gidan ta Hajiya da kanta ta mata Alkhairi bare uban gayyar da ya bata dubu Dari harda zannuwa masu tsada itada mama kafin ya tafi yasmin ma ta kara musu, saida tayi kuka saboda murna tace " nikam bana kishi da wainnan kishiyoyin gaskiya ga takwaran me gida ga kuma kuma kishiyar saurin kwarai Allah dai ya raya manasu akan sunnah, hajiya tace Amen, kamar karta tafi sukeji, driver yakaita gida cikeda harkar arziki, gida yarage daga hajiya sai masu aikin, yaran sunyi bulbul dasu kyansu na kara Fitowa da wayau, kullum sai sunyi waya da ubansu sama da goma yana tanbayar yaranshi,

Yauma suna kwance a gefen hajiya itama tana zaune suna hira ya kira wayar ta ta dauka tareda yin sallama, Ajiyar zuciya ya sauke, " baby ina kewarki fa kinsani gaskiya zanshigo, " ga momy na zaune, tayi saurin bawa hajiya wayar, dariya yayi wato bazata iya Amsa mai ba tunda tana kusa da hajiya, saida suka gama gaisawa kafin ta tashi ta fita, "my beautiful wife say something are you missing me too? "Sosai ma ai basai na fada ba, ya dauke ne? "Mene? "Jinin. "Aa ta "har yanzu? Tree week's fa baby, "idan ya dauke zanfada maka kazo ai nima ina kewar ka sosai mijina, "tanks my wife, I love you , yana kashewa tace tab bangama hadewa ba nasan kana zuwa saika tsoma inkasan ina sallah, dole intaimaki kaina ai don kana shiga kaji canji daraja ta zata iya raguwa, sorry zauji kainakewa tanaji, ita kanta tasan tanashan gyara ga na HQ gana ciki duka y'ar Niger ke mata ga wani irin murjewa da takarayi tayi shar da ita, tasan oga na ganinta zai rikice,

Saida suka kwashe sati uku cur kafin yasamu shigowa kaduna saboda wani couse sukeyi na karin girma ranar surprise yayi musu suna baje a falon ta yaran na cikin gadajensu dake falon don baban ko ina ya Ajiye musu gadaje, akwai a dakin shi akwai anata kuma, Abulkhair ne kawai ke kan kafar hajiya, " Fatima wannan me gidan sai kin dage akwai tsotso shiyasa yafisu karfi duk da shine karami, "wallahi momy har ma kar dare yayi mai hakuri sai momy na ko Ihsan tana taba rigima, dariya hajiya tayi tana mejin dadin yanda yasmin ke mata kara a KO ina tana kiranta Momyn ta don haka take karajin sonta har cikin jinin ta,

Ai da wuri zaki fara basu Abincin su bari baba yazo don ma kinada wadatar ruwan nonon da akwai damuwa shayarda ya'ya uku, Sallamar shi ya katsesu tareda zubamai ido cikeda mamakin ganin shi, tunda ya iso ya zuba mata ido kamar baitaba ganinta ba don tayi kyau sosai cikin super din dake jikinta green ta zubo kana nan kalabarta a kafada tana daukar ido tayi wani irin cika mai burge duk wani namiji, itama kallon shi takeyi yanda yayi kyau a cikin kakin kanshi ba hula sai boot dinshi dake sheki Alamar sabuntaka yayi mata kyau sosai, wurin mahaifiyar shi ya karaso tareda daukar yaron ya fara gaisheta, " Sannu Hajiyar yasmin " yauwa mijin yasmin dina shigowar bazata Kayi mana? "Wallahi momy bamu dade fa da gama waya dashi ba baifada min zai shigoba, wani Abu kallo kawai yake aika mata don hajiya na wurin ne yasa bai isa jikinta ya rungume taba, bin ko ina na jikinta yakeyi da kallo kamar zai cinyeta duk dokin ganin yaran shi da yakeyi maman su ta daukemai hankali saida hajiya tace kawoshi ni inshiga ciki lokacin sallah yayi kar ya dameta don shi rigimamme ne, mikewa yasmin tayi ta nufi kitchen yabi bayanta da kallo tana juyamai kwakwal wa, da gayya don tasan ya gama sumewa, hajiya ta ganoshine tsab yasa ta basu wuri, wani irin Y'ar yaji tsigar jikinshi na tashi ya mike tareda leka fuskokin Y'an matan shi ya basu fake a kumatu " sorry my girls mom is calling yafada tareda nufar kitchen din cikin saurin shi,

Drinks da Abinci take shirya mai don Yau ma yayi sa a sunyi tuwon nashi don hajiya hanata cin kowane irin cima takeyi saboda cikin yaran, saurin karasawa yayi ya karbi tray din tareda Ajiyewa a gefe ya shige jikinta yana zuba mata numfarfashi da sambatu, " baby you no I came only for you jan Ajinfa kinbirkitani baki daya wallahi muje dakina , yana kwakume da ita suka fito, suka hadu da baba jummai, ta fara mai barka da zuwa yace " baba don Allah ga yarana a falo a kula dasu, tace to ranka ya dade angama, kunyar Abin yasmin taji tace, "please bari indakko Abu a dakina ina zuwa, "Nop muje tare kawai I can't wait any longer baby, one second zuma I will be back, baisoba haka yabarta, ita kuwa tayi mugun kaduwa da ganin shi don Sam bata shirya maiba gashi wani hadi ake mata Wanda zai dauki nan da sati kuma jiya aka fara tafison sai angama ta kara kame Abinta a hannu,

Dakin ta ta koma cikin sauri ta makala pad tareda kara turare a jikinta ta fito, Koda ta shiga har ya cire kayan jikinshi yarage dagashi sai boxer yanata zarya tana shigowa ya matso a sukwane ya shige jikinta yana zuba mata kalaman yadda yayi kewarta na tsawon sati biyu, birkici mata yayi domin kamshin jikinta na musamman ne yana kara daga mai hankali da kuma rikitar dashi don bakaramin gyara tasha ba kamshin ya huda ko ina na jikinta, sai bin jikinta yake da hancin shi yana zuba mata santin yanda ta canja,

Daga karshe gadon ya mayarda ita yafara rabata da kayan dake jikinta cikin rawar jiki, jikinshi yayi sanyi lokacin da yakai wurin pad ya marairaice tareda tsagaitawa, "baby why baki fadamin ba kika bari nasa rai,? "Ai baka fadamin zaka dawo ba dana fadama kuma har yanzu banyi Arba in ba, kallon ta yayi da idanun shi da sukayi jawur saboda fitina, " baby yana zuba sosai har yanzu let me see, ya fada yana kokarin tura hannun shi, tati saurin riko hannun shi "oh my Zuma kasan ina son farin cikin ka kuma nima ina kewar zumar miji na bakai Kadai ke son kasancewar mu a inuwa daya ma nima ina ina bukatar kasancewa da farin ciki na,
A haka ta mai dabaru domin ragemai zafin da ya debo kuma yasamu natsuwa sosai yanata gode mata tareda makaleta, sai gab da magrib ya koma jaji bayan ya gama wasa da yaranshi ta cika mai tumbin shi da dishes dinta masu dadi,

A kwana a tashi ba wuya gashi har sun cika kwana Ar abin da haihuwa hajiya ta koma gidanta ya rage daga ita sai su baba jummai a gidan oga MA kuwa ya kusa kammala couse dinshi ya dawo, tayi yawon Arba in dinta gidajen Y'an uwa sosai ko gidan su ma kwana tayi domin mama Sam taki yarda taje gidan ta sai su babane suka je kusan sau uku ganin takwaran baban zango da kuma uwargidan shi inji baba yaran sunada shiga rai sosai don ranar da ta kwana gida ma a wurin su baba yaran suka wuni sunkasa fita saboda yaran masu mugun shiga zuciya, mama ma duk karar ta saida ta makale yaran, ranar sunga gata sosai a gidan, daga gidan su gidan ismail taje yayi matukar farin cikin ganin ta a gidan shi, zainab dake fama da tsohon cikin ta haihuwa ko Yau ko gobe itama taji dadi sosai ganin uwar gidan MA a gidan su da kyawawan yaransu, daga karshe ta d'an gana da Bariki domin shirin ta, gidan Aunty maryam ta sauka itama tayi farin cikin ganin ta, suka baje sukasha hirar su ta zumunci kafin suje wurin matar umar taga tayi mugun laushi kamar ba masifaffiyar matar nan ba, tayi murna sosai tareda yi mata godiya akan Alkhairin da oga MA ke musu akoda yaushe, harda kukanta, ta kara Mata wani Alkhairin sannan suka nufi gidan ta masu gadin nata kwasar gaisuwa,
Chapter 64 · 0% Book details