Sashe 7
Ali Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Na sani huddy inaji ajikina wlhy bazaki mutu yanzu ba, likitan me shi ai besan gaibu ba, kuma dukiya ta sedai inga bayanta wurin nema miki lafiya da yardar Allah" qara rungumeshi tayi sosai sun jima a haka kafin tayi yunkurin shiga ban daki, wanka tayi sannan ta sauya kayan jikinta ta sallaci sallar magrib wanda koda ta idar baya nan ga alama masallaci ya tafi.....
* Wani yammaci naquda ya tasowa huddy batare da kowa ba, tasha wahala sabida kasa zuwa koda parlor tayi ta ciro wayanta caji, haka ta wuni dakin tana jiwo rurin wayar gashi Manga tana school, Ali Abbas yana ganin yayi ta neman wayarta baya samu ya kamo hanyar gida, tare suka shiga part d'in da Manga kallon juna sukayi lokaci d'aya qirjin manga yayi wani irin mugun dokawa. "Mesa nake ganin tamkar na saba gauraya idona dana yaa Ali aduk sanda na sanya idona da nashi,mesa qirjina yake linka luguden dayakeyi aduk sanda na ganshi?" wannan itace tambayar da manga kewa kanta a zuciyar ta, yayinda Ali ke cewa a ranshi
"Mesa arayuwa nakasa dauke idona akan Manga? Tayaya zuciyata zataci gaba da nunamun abinda baze taba yiyuwa ba? Mesa nakejin tausayinta yaya zanyi da raina?" A tare suka had'a baki wurin cewa juna "Sannu da zuwa!" batare sun shirya fitar kalaman ba murmushi suka sakarwa juna a tare sannan tace
"Sannu yaa Ali ya aiki?" amaimakon ya ansata seyace
"wannan gayun beyi yawaba Manga kalli qaramin mayafin dake kanki? Plss kisani akwai aure a kanki, ki sauya yanayin fitarki" duqar da kanta tayi tace "Allah yaa Ali hijabaina ne sukayi datti, wannan ne karon farko danaje school da mayafi ma" gyaran tsayuwar shi yayi yace
"Mesa?" bata fahimceshi ba tace "Na'am?" jan gashin gemunsa yayi yace "Mesa sukai datti?" sadda kanta qasa tayi tace "Sabida ban wanke ba" juyawa yayi ya soma tafiya
"k'waya nawane dake hijaban?" murmushi tayi "k'waya hud'u ne"
"sunyi kad'an gobe zakuje da Amadu driver kasuwa ki dinka k'waya ashirin" da sauri ta kalleshi tanaso tayi magana amma yatafi da nisa abinshi dole tabi bayanshi zuwa ciki, tana qarasawa tajiyo salatinsa, bin bayanshi tayi zuwa d'akin da sauri ganinshi tayi rungume da huddy da sauri tayi kansu, ita ta tayashi suka kwasheta zuwa asibitin uduth......
"Lafiya lau ta sauka cikin sa'o i uku ta sunkuto yaronta Namiji me matuqar kamanni da ita, murna awurin Ali Abbas ba'a magana, musamman data sauka lafiya,lafiyarta itace agaba da komai a wurin shi yana matuqar san matarshi ba iyakaaa....
Ranar suna yaro yaci suna Ibrahim, ana ce dashi Ameer, gabaki daya san duniya Manga ta dauka ta sakawa yaronnan, sabida ansaka masa sunan mahaifinta...
Huddy ta soma aikinta da asibitin uduth a b'angaren mata dama wannan fannin ta qware, yanzu kam akwai baiwar dake kulada Ameer dukda haka rabin rayuwarshi ne yanayine tare da Manga, dazaran ta dawo skul tofa yana wurinta inko bata zuwa skul ma bata barinshi awurin kowa se ita......
*Bayan shekaru biyu*
Rayuwa me tsafta da aminci Ali Abbas keyi da huddynshi, yanzu level 3 Manga take a jami'ar usman d'an fodiyo dake sokoto, Ameer kuwa yafi sabo da Manga fiye da kowa a gidan, Ali Abbas ya dauke idanshi akan manga a tsawon shekarunnan yayinda zancen Gadanga sam bashi ba labarin ko wanda yajishi tsawon shekaru uku da wata hudu kenan,Manga girma ya zauna yanzu shekarunta 22 a duniya, ta zama cikakkiyar mace sedai fa damuwa fal a ranta har yanzu hoto da soyayyar gadanganta rad'am zane a zuciyarta, ko zancen raba auren akai mata kuka take sakawa tukuru.....
Duk iya qoqarin dan ganin ta dannewa kanta abinda takeji abin ya faskara, duk yanda taso ta hana hawayen dake idanta gangaro wa seda sukayi tattakin yin ambaliya daga manya manyan fararen idanuwanta zuwa lallausan kuncinta,zuciyar ta ke neman fasa qirjinta ta fito,duqawa tayi ta dafe qirjinta ilahirin sumar kanta ta sakko ta rufe mata kanta da fuskar gaba d'aya,jin zuciyar zata faso qirjin ta fito bilhaq ya sanya ta dafe wurin ta furta da iyakacin k'arfinta "Gadangaaaaaaa!!!! Ina kashigane arayuwa? Kasan kuwa rashin ka yana meman kaini lahira??? Yaa Allah indai gadanga yana raye Allah ka bayyanar mun dashi, in kuma ya mutu yaa Allah ka bamu ikon jin zancen mutuwarshi daga majiya me tushe...dafa bakinta tayi da sauri inaaaaa gadanga be mutuba inshaa Allah zaka dawo gareni mu rayu cikin Aminci da qaunar juna......Dafe kanshi yayi ya koma baya a hankali duk iya dauriyarshi seda yae k'walla...kwanciya yayi yana shiga d'akin a hankali ya furta
"Astagfirullah Allah!!! Allahu kamun gafara, Allah ka yafemun, ina zanje da Haqqin Manga ni Aliyu gadanga?? Ina zankai cutar dana mata, tayaya manga zata karb'eni matsayin miji, yaya zanyi idan ta gujeni? Ina zan saka rayuwata idan ta tabbatar ni Ali Abbas nine gadangan ta? Ina zankai abin kunyar dana aikata? Me zancewa me martaba? Me zan sanar da fulani Adama? Mezancewa iyayen manga? Mezance wa Mahaifin huddy? Mezancewa huddy....yaa Allah kamun agaji....Allah kabani mafita me sauqi....Allah kasan dalilina nayin hakan Allah ka gafarceni na cutar dake manga.....
Mom Nu'aiymm.....
Masu hasashe kun canka
[7/6, 1:53 PM] +234 706 571 7620: *Haske writer's Asso.(home of expert and perfect writer's)*
*👑ALI ABBAS 👑*
Billy galadanchi
Sadaukarwa gareki qawa ta gari *Fulany saddy*
*Wannan shafin tukwicine gareku en ALI ABBAS fan's group 1, ina yinku irin totally d'innan ku sani comments naku su suke qaramun qwarin gwiwar wannan rubutun, ina godiya sosai ga soyayyarku da wannan book*
*Shout out to all ALI ABBAS fan's*
05
Tasowa yayi yadawo k'ofar parlor din yana kallon yanda take kuka rayuwarshi tana tafarfasa, duka hannayenta biyu ta cura acikin sumar kanta ta jashi sosai irin cizgar da kasan tana jiyo zafin zuciyarta har cikin ranta, kukanta takeyi cikeda ban tausayi
"Ya zan rayu idan baka rayuwata yaa gadanga, nayi qoqari in kauda ka a idona da zuciyata amma nagano wahalar da kaina kawai nake, gangar jikina kawai ke tare dani amma zuciyata,ruhina da rayuwata sun tafi a duk inda yaa gadanga, yaa Allah ka tallafi maraicina, Allah ka bayyanar mun da duk halin da yaa gadanga yake cikin gaggauwa, Allah idan yana raye ka bayyanar mun da shi cikin gaggawa cikin kamanni masu kyau, yaa Allah idan har gadanga ya mutu....se kuma kawai ta qara toshe bakin ta
"Idan ya mutu mutuwa zanyi nima, Allah karka kasheni banyi rayuwa ta Aminci nida gadanga ba, Allahu ka jib'anci lamurana Allah ka sassauta mun wannan rad'ad'in da zogin da zuciyana keyi" kasa daurewa yayi yaje ya tsuguna kusa da ita, hannunta datajejan zumar kanta dashi ya sanya hannunshi ya sauke ya qura mata ido, ita d'inma kallonshi takeyi,girgiza mata kanshi yae alamar ta dena kukan haka,amma ga mamakinta shi d'inma qwallah yakeyi, ganin haka ya sanya ta tsagaita nata kukan cikeda mamakinshi kawai se ya sake mata hannun ya miqe ya koma ciki, barin parlor d'in tayi,yayinda shi kuma ya shirya a gaggauce ya nufi sashin mahaifiyarshi, yana so yau ya sanar mata damuwar shi yanaso yau kad'ai ya nuna mata haqqinshi akanta, bashida abokin shawarar daya wuce mahaifiyarshi amma abin haushi da huddy da maneer ma bata sake musu wai adole sune ahalin gidan d'an fari......da sallamarshi yashiga cikin parlor d'in ba kowa, iso ya sanya wata hadima ta masa zuwa ciki, ya dad'e yana jiranta kanta fito a hakimce ta haye kilisarta batai magana ba shine ya duqar da kanshi yace
"Barka da yamma Ummu" amaimakon ta amsa masa setayi gyaran murya tace
"Lafiya dai?" jikinsa ne yayi sanyi ya kasa cewa komai ya sadda kanshi qasa kawai, miqewa tayi ta koma ciki abinta, gwiwa a sace ya tashi ya fita, mota ya cizga kawai ya nufi gidan zuhair, a parlor suka zauna ya tattare nustuwarshi cikeda damuwa yace
"Zuhair ina cikeda damuwa, cutarwar danakewa Manga abin ya isheni haka, shekaru kusan hud'u yanzu tunda few month ya rage, naksa aiwatar da abinda kace sabida inasan Manga, bazan iya aika mata da takardar saki ba, a yanda Manga keji na aranta na tabbatar mutuwa zatayi, koma gabaki daya taqi yarda da takardar, kuma wlhy zuhair ka yarda dani yanzu ina san manga so bana wasa ba,ina mata san da aduk fad'in duniya banta b'a wa mace irin saba, ya zanyi da raina ne wani?" shiru zuhair yayi nad'an wani lokaci kanya nisa yace
"Yarima gaskia tun farko kaine kayi kuskure da kanka, narasa wace qaddarar ce ta sanyaka komawa bayan munyi dakai bazaka koma a d'aura auren ba" nisawa yayi shima
"Zuhair kasani ai yanda ya zamto, alqawarin auren ta nawa mahaifinta,nasan girman Alqawari bazan iya karyawa ba" tsaki zuhair yaja
"kasan girman alqawari amma ka wofintar da igiyar aure? Aure fa ALi? Kasan kuwa ma'anar sa? Tanada haqqi a kanka kasan qarfin sha'awanta yanda yakene? Kasan yanda ake tsine maka tulin wannan lokaci ? Kasani wlhy Yarima kayi ganganci sabida yanzu bansan ta inda zaka soma ba,me martaba ma baze saurareka ba, bare ita uwar gayyar, mafita d'ayace ka aika mata takardar saki ta huta da wannan auren dabaida maraba da dabaibayi agareta" miqewa yayi
"Banida k'arfin aikata wannan Kuma,koda za'a kasheni bazan taba sakin Manga ba wlhy, dolene nasan abinyi yau d'inann bazab zura ido inga Manga tana kukan rashi na alhalin gani kusa da itaba" zuhair dai bece dashi komai ba harya fita, mugun tausayi ya bashi matuqa,yamai gudun haka yanzu wannan abin daya aikata koshi dayake amininshi baze iya bashi gaskiya ba wlhy......
Kai tsaye part d'insu ya wuce zuwa d'akin dayake mallakin shi, wani akwati ya d'akko a sama ya janyo wasu hotuna na manga da wani wanda suka dauka atare rabar d'aurin auren su, murmushi yayi ganin yandabtake ada da sauyin data samu a yanzu, wata leda ya janyo ya bud'e ya zaro wani mask wanda yake amfani dashi sanda yake matsayin d'an aiki a gidansu huddy, shafar ta yayi ya zaro har wata jallabiya dayake yawan amfani da ita a wannan lokacin,kwasar wasu daga cikin kayan yayi yabar gidan dasu zuwa guest house nashi dake sama road.....