Sashe 15
Ali Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Kaga Almaksashi yarannan ne zomuci uwarsu, tsorone ya sanya suka fito gaba dayansu banda humaira dabata iya tashi sam, dariya suka kwashe da ita sukayo kansu, sumar kan Manga ya cabko iya qarfin shi ta qwalla uwar qara ya turata seda kanta ya daki wannan dutsen take jini ya soma fita daga goshinta, ya qara yi kanta ze cafko ta zaro bindigar dake qirjinta ta harbshi a qafa, ita kuwa Hannatu ta qwace ta hannunshi suka nuna awurin dayan, hannatu ce ta harbe dayan ma a ciki, a take ya fadi wurin a mace shikam, dayan me suna Almakashi se riqe qafarshi yake yana ihu, aljihunshi suka lalubo suka dauke musu wayoyi Manga ta goya humaira dake kukan ruwa suka danna a guje....sunyi tafiya me nisan gaske yayinda jiri ya soma daukar Manga kasancewar dukda tayi amfani da dankwalin humaira wurin daure wurin dataji ciwo hakan be sanya jini ya dena zuba ba, haka ta daure saliha ta karbi humaira se bayan salla asuba gari ya gama wayewa suka isa cikin wani qauye da ake kira 'yankara, wasu yara manga ta gani tace dasu
"Kai inane gidan sarki?" kallon medan wayon ciki yayi ya kalli yanayin shigarsu yace
"Muje na kaiku gun meri dai shine sarkin garinnan" jin jina kanta tayi suka bi bayan yaron har zuwa wurin me garin, ba'ama soma zaman fada ba wannan lokacin seda jira kusan karfe tara sannan aka soma zaman fada, kafin nan har sunci abinci sunsha ruwa, an kuma gasawa Humaira raunin ta abisa roqon da Manga ta musu, zaman fada ya tashi anan su manga sukayi bayanin meya faru dasu tiryan tiryan, hankalin me gari ya tashi da kanshi yayi waya ma en sanda suka hallara garin, kai tsaye aka miqasu manga sokoto kasancewar dukkansu gari daya suka nufa, sunsha mamakin su a katsina suda sunmabar zamfara state sun doshi sokoto sanda abin ya faru, kenan ba qaramun yanka sukawa dajin ba sunsha wuya, A state C I D aka kaisu inda kowa ya bayarda Number din en gidansu, Manga bata da Number din kowa akanta, dan sandan ya kalleta yace
"Toke er gidan waye ai dole dai mu nemo gidan tunda kinsan unguwar keba yarin ya bace ba" kanta dake sara mata ta dafe, wurin na mtuqar yi mata zogi tace
"Gidan sarkin musulmi dake kan wuri" kallon sosai D P O ya mata yace
"Matar yarima kenan danakejin an kawo report ana kan nemanta me suna hafsatu Manga?" kallonshi tayi ta d'aga masa kanta alamar e, murmushi yayi yace
"Alhamdulillah lemme call him, befi 10 mnts dagama waya daniba, yarima na cikin tashin hankali sabida ke kullum zeyi waya yafi so 20 a wuni game da case dinki mun damke wasu en fashin dake operation a wannan yankin amma sun sanar mana sedai idan team din wanine su basa kisa kuma basa rape" yana maganar ne yana danna wayarshi domin dallawa Ali Abbas kira....ringin biyu ya daga
"D P O ya aiki?" Murmushi yayi tamkar yana ganinshi yace
"Yallab'ai congratulation, ga madam a station namu ta sauka da kanta" gigicewa yayi yace
"Da gaske ka tabbatar ita dince?" ganin hafsat ta tafi luuuu zata fadi ya sanya D P O Din miqewa tsaye gaba daya yana kalima batare daya amsa wayar ba, ta suma, shine abinda yaji suna fada aikam ta gudun shi ya zadi key yayi hanyar state C I D, koda yaje aka sanar mai itace ta suma an kaita uduth, juya akalar motarshi yayi zuwa uduth din cikeda tashin hankali.....
Mom nu'aiym....
Se zuwa yamma zan bayar yanda nai alqawari inshaa Allah.
*HASKE WRITER'S ASSO. (Home of expert and perfect writer's)*
*👑ALI ABBAS👑*
*Sadaukarwa gareki qawa ta gari Fulany saddy*
11
Emergency aka karb'eta, cikin gaggawa, ta bugu sosai aka, gashi ta zubar da jini sosai ba kadan ba, gakuma tafiyan wahalan datasha, jinin data zubar yafi komai bata wahala sabida dolene ma se an mata qarin jini, Gabaki d'aya kuwa Ali ya gama rud'ewa gida yaje ya sanarwa Ummu abinda ake ciki, ita kanta ta shiga tashin hankalin rashin Manga gashi ta dawo ba daidai ba, babu lafiya, yaudai da kanta ta fita zuwa asibitin cikin rud'u, ganin Manga batasan inda kanta yakeba ba qaramun tayar mata da hankali yayi ba, jinin daine ake buqata cikin gaggawa, Ali Abbas ne ya bada jini kasamcewar nashi o+ ne yakan baiwa kowa jinin, Seda tasha leda biyu tukunna ta dawo wa hayyacinta, wanda har loacin bata bude idanta ba kasancewar tasha alluran bacci.....
Humaira dai bata shaba, a wannan yammacin ta komawa mahaliccin ta, ta bada tausayi ainun, tunda ta rasu hankalin Ali da ummu ya qara tashi, dukda yake suaran en matan sun bada labarin cewar humaira kadai akaiwa fyd'e amma wannan be sanya zuciyar Ali nutsuwa ba sam ya gagara barin asibitin duk inda hankalinshi yake a tashe yake.......
Se bayan kwanaki uku sannan Manga ta samu kanta, koda ta farka ummu ta gani kusa da ita, inno kuma tana zaune a qasa tayi tagumi, bazata iya tuna meya faruba tun bayan zuwan su station, ganin komai takeyi tamkar a mafarki, murmushi ta sakarwa ummu dake kallonta tana murmushi cikeda farin ciki sannan tace a hankali
"Ummu lafiya dai?" hannunta ta riqe "Karki tilastawa kanki yin magana Auta, bakida lafiya ki saving strenth naki plss, ko akwai abinda kike buqata ne?" kallon Inno tayi tace
"Ummu yaushe mukazo kaduna?" murmushi fulany tayi
"Babu wata kaduna damu kazo, muna sokoto ai, kina asibitinr manga, raunin ya baki wahala dole tazo dubaki da kanta" murmushi tawa inno
"Inno ina Baban Manga?" kallonta ummu tayi
"Auta nace ki dena yawan magana sabida raunin dake kanki, ba a so kike baiwa kanki wahala koda ta magana ce" marairaice fuska tayi
"Ummu ninaji sauqi fa, Ina su Humaira?" shiru Ummu tayi tana kallonta sabida batasan ta daga mata hankali, seda ta gama nazari sannan tace "Duk sun komawa iyayen su, ko jiya ma sunzo duba ki" murmushi tayi tace
"Allah ya isarwa Humaira muguntar da aka aikata mata, Allah ya saka mata, Allah ka wulakanta masu irin wannan halin halin ya saka mana " se kuma ta fashe da wani irin kuka me ban tausayi, ita kadai tasan me ta gani, ita kadai tasan kalar arzikin dasukayi,Allah kuma kad'ai ya sanya musu hannu suka kub'uta daga hannun wa'yannan azzalu man, tsorata takeyi kazalika takan samu kanta cikin mummunan fad'uwar gaba duk sanda ta tuna yanda ta karyawa wancen ogan nasu banana, tana roqon Allah ya sanya bawai mutuwa yayi ba, kuma kar Allah yasa wannan ma data harba a qafa shima ya mutu, sosai take cikin rudu mara misaltuwa ,bata fata ace wai ya mutun sabida bazataso ace tayi kisan kaiba har qarshen rayuwarta dukkuwa dayake ta aikatane bisa kare kanta datayi....... Rarrashinta ummu ta somayi harta koma baccin sannan ta nisa tace
"Ina roqon Allah ya cire miki wannan abin dakikeji a ranki Auta, Allah kuma ya sanya ki manta komai da kika gani" Ameen inno ta furta a hankali, tana tausayin rayuwar Manga sosai ba kadan ba.....
Kallon ta Ali Abbas keyi cikin tausayawa, wata irin azabtacciyar soyayyar ta yakeji har cikin ranshi, yaso ace sanda ta farka dinnan yana nan, yayi matuqar kewar ganin idanta a bude, yana mata wani irin so wanda baze taba faduwa ba, yana cikin shauqin santa ainun, hannunta ta soma matsowa sannan a hankali ta daura dayan hannunta saman kanta ta dafe shi tana yamutsa fuska alamun inda ta tab'a d'in yana mata ciwo ba kadan ba, kallonta kurin yakeyi ya kasa koda motsi bayaso ya wargaza mata jin dad'in ta, karya tasheta a bacci shine damuwarshi,wasu sirarran hawaye ne suka soma sauka a asaman kuncinta, zuwa yayi ya duka kusa da ita, yace cikin murya qasa qasa
"Hilwa sannu meyake miki ciwo?" hanninta ta sauke se a lokacin ta bude lumsassun idanuwanta ta diresu a kanshi tace
"Yaa Ali kainane fa yake saramun, ina baccina nasomajin tamkar ana kwad'amun sanda aka" hannunta ya riqe yace
"Barinwa huddy waya tazo ta sanya a dubamun meyene damuwarki, sannu kinji inshaa Allah ze dena" wayanshi ya zaro daga aljihu ya soma dannawa
"Baby kizo za'a duba Hilwa ta farka kanta yana ciwo sosai" a daya bangaren tace "Mashaa Allah ina kan hanyan d'akin dama" koda suka zo alluran bacci suka qara mata, sun tabbatar masa cewar zata riqa samun ciwon kai akai akai, sabidda tasha biguwa jini ya ratsa wasu sassa acikin kanta inda ba'aso yaje, amma a hankali da kanshi ze baje sabida kadanne abin....
Washe gari ma koda ta farka Ali baya nan, amma yanzu da d'an sauqi kam ta samu ciwon kan ya lafa mata sosai.... Wuraren sha biyu na rana Ali na zaune ya tasa manga agaba akan lallai setaci abinci yayinda take ta turjiya harta baiwa Innoh dake d'akin mugun takaici wanda ya sanya tabar mata dakin ma gaba daya....suna nan ya hade rai, suka jiyo sallamar su Hannatu da sauri Manga ta miqe suka rungume juna hannatu na kuka tace
"Aunty Manga munyi arziki da ba'a mana fyad'e ba, Allah ne gatanmu kuma kece gatanmu kinga dai yanda rayuwar Humaira ta zamto tamkar ba'ayi ba, yanzu sedai tarihi Lil humaira Allah ya isan ta wlhy" dagowa tayi daga rungumar juna da sukayi tace
"Ban gane ba hannatu me kike shirin sanar dani" Ali se qiqiiiftawa Hannatu ido yakeyi amma bata lura ba taci gaba
"Ai humaira tun washe garin ranar damuka dawo ta rasu, tunkan ma a cafko sauran en fashin" kuka ta saka me tsuma zuciya gashi likitoci sunyi hani da bata damuwa, sabida yanayinta kukan nan takeyi tamkar ranta ze fita tama kasa furta komai kuma taqi zama, seda tayi kukan ya isheta har muryanta ya dashe