← Book details Ali Abbas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 38

Sashe 37

Ali Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Zan sanar da mahaifinta domin a iya sanina yana saudia din, idan yana madina seyaje ya sallace ta,Allah ya mata gafara ya sanya mutuwa hutu agareta Allahu ya bamu hakurin jure rashin ta,halinta na gari ya bita a duk inda take" sallama sukayi Ali Abbas ya qara bin gawar dake gabanshi da kallo ko shakka babu indai akanshi huddaisa zata aljannah tokuwa taje sumul domin babu shamaki ya daga mata qafar sa tafiya babu gargada, shida kanshi ya sani yayi rashin matarsa me nagarta da sanin Allah yana wa kanshi kuka domin huddy ba itace abin tausayi ba shine, yaya ze rayu babu hudaisa, a haka har kiran mahaifin huddy yashigo wayarsa ya d'aga cikin qunan rai, take yamai bayani anyi sa'a yana madeena sekashi yazo se rarrashin Ali Abbas yakeyi Manga ma anacen kwance anata kuka ba qaqqautawa ga yara suna wurinta se tambayan momyn su sukeyi gwanin tausayi gata kwance ba lapiyan jiki.

Huddy ta samu jama'a kam ba laifi kazancewar shi ranar juma'a ana idar da sallan juma'a aka sallaci gawarta da wasu mutane guda uku, aka kaisu kushewa, Ali Abbas se ciwo yakeyi a tsaitsaye mahaifinta ma yafi sati tare dasu,har me martaba da Ummu suka zo domin akula da Manga tare da wasu hadimai susu biyu.....

  Kallon sosai Ali Abbas kewa jaririyar yar tashi yana jin santa yana ratsa ilahirin jikinsa, lumshe idanshi yayi yace "Allah ya rayarmun dake da sauran en uwanki Hudaisa, Allah ya sanya kiyi halin karamci irin na takwararki Allah ya baiwa mahaifiyarki lafiya Ameen" Yarinya kam a kwalba take kwana anan take wuni har akayi sati biyu seda tayi qwari tukunna sannan aka sallamesu.....

   Manga har zuwa wannan lokacin bata dawo hayyacinta ba, yauma ban d'aki ta shige se faman ruwan hawaye takeyi  ba qaqqautawa,kukan harda shesheka, Ali Abbas ganin ya jima a d'akin bata fito ba ya sanya yaje ya tsaya jikin qofar toilet din

"Hilwaty yada jimawa a toilet ki fito mana ko" share hawayenta tae ta saisaita nutsuwarta sannan seta fito kallo daya ya mata ya gano kuka tayi jan hannunta yayi suka zauna bakin gadon

"Hilwaty kuka kuma? Yanzu dama haqurin dakike bani akan rashin huddy ba gaskia bane, yaya zaki koma ban daki ki dinga kuka abinda ya dace ki zauna kinawa hudaisa fatan samun dacewa da rahamar Allah, dan Allah Hilwa ki dena kuka, kidena damuwa idan kina yawan kukannan zaki karyarmun da zuciya" kallon shi tayi

"Yaa Ali duk sanda na tuna da Aunty huddy nikan kasa tsayar da ruwan hawayena, mutuwan aunty hudaisa yamun ciwo ban taba kawo mata mutuwa ba,tayi ciwon dayafi wannan zafi amma sam bata mutuba se yanzu" hannunshi ya daura a bakinta yace
"haba mana hilwa, karki yi sab'o mana mutuwa ai se lokacinta yayi ake yinta bawai haka kurun ba, ki sani mutuwa ba'a gane wanda zeyita domin kuwa marasa lapia wanda suka bushe ma sun tashi sun dawo garau, masu lapia kuwa mutum yana a tsaye seya fadi kan a daga ya zama gawa sabida haka ki gane Allah yana saukar da ikon sane da iyawarshi aduk sanda yaso,alokacin dayaso bisa kuma wanda yaso hakan ta faru dashi, ba'a barin wani dan wani idan akama mutuwa kaqiyin tawakalli se a da d'a maka me mugun zafi yanzu a misali a rashin hakurin nan dakikai kurin sena mutu ki huta tunda bakya san kowa naki ya mutu" kallon shi tayi da sauri

"Dan Allah ka dena cewa zaka mutu yaa Ali,i shaa Allah bazaka mutu ba sena rigaka mutuwa kuma bama yanzu ba inshaa Allah" murmushi yayi yace

"Babu wanda yasan sanda waninsa koshi kanshi ze mutu,fatan dai kurun mu cika da imani muyi kyakyawan qarshe" sauke ajiyar zuciya tai ta lafe ajikinshi tana tunanin rayuwa yanzu shikenan ba huddy kenan bazasu qara ganinta ba bazasu qara jin muryanta ba, dariyarta yin hira da ita, ta tafi kenan dukkanin komai daya shafeta banda memorie's nata ta tafi kenan har abada?,runtse idanta tayi asarari ta furta "Allah ya jiqanki Aunty huddy, Allah ya miki rahama,Allah ya gafartq miki Annabi yasan da zauwanki Aunty huddy,halinki na gari ya biki.....matseta Ali Abbas ya qarayi banu wani option dayake da face ya zubar da hawayen dasuke qoqarin fasa idanshi su fito sabida baze iya haqura ba, shida kanshi qarfin hali yakeyi wani irin tausayin huddy da kanshi yakeji, ya tuna sanda tace dashi lokacin tana cikin azabar ciwo

"Abbi nasan cewar mutuwa zanyi amma wlhy banaso na mutu abbi, inaso in rayu dakai,inaso in rayu da yarana har girmansu, Abbi inaji ajikina bazan qara kosa kwana daya ba aduniya bare kuma sati, idan Allah yayiwa Manga tsawon rai ka sanar mata ta riqemun yara na amana,kuma ban yarda akaimun su wurin Ammyna ba koda anganta, idan kaga Ammy na kace da ita nayafe mata amma idan tayi qoqarin rabar yarana ta koya musu muguwar aqida ban yafe mata ba, babu ita babu yarana ko bayan raina,kuma itama ta yafe ni" rufe mata bakinta yae yace

"Haba mana Huddy inshaa Allah bazaki mutu ba zaki tashi garau, ciwo aiba shi bane mutuwa" murmushi tamasa cikeda qauna lokaci d'aya zafafan hawaye suna kwaranya daga idanta tace

"Yaa Ali nasani ba'a gayawa bawa ranar mutuwar sa amma kalli fa yaa Ali ko fitsari da kashi a kwance nake yinsa,kalle ni ko yanzu meye marabana da gawa banda numfashi banafa iya tashi, yaa Ali kalli sumar kaina yanda ya dawo ba komai ajiki tamkar wata tsohuwa ka tabbatar nakai mataki na qarshe a cancer,bazan rayu ba yaa Ali taimako daya zakamun shine kamun adu'a har bayan ranka adu'ar ka kurin nakeso, kuma dan Allah banida gadon komai dukiyata ka bayar a gina rijiyoyi da masallatai a qauye yanda na taho duniya a tsirara haka zan komawa mahaliccina gado fitinane, sadaqatul jariya kurun zata bini a kushewata ka taimaka kamun wannan" hannunta ya riqe sosai yana hawaye yace

"Nasan bazaki mutuba Huddy inshaa Allah zamu rayu cikin aminci ki dena diremun wa yannan bayanan dan Allah" numfashinta ya soma rawa wanda hakan ya sanya yaje ya kira doctor aka dara mata aux sabida ya taimaka mata wurin numfashi, a haka kuma ya barta da manga wanda koda suka dawo da doctor bata numfashi ashe mutuwar kenan wata razananniyar qara ya saka ya qara matse Manga gagam wanda seda manga ta firgita ya furta

"Na tausayawa hudaisa sabida batasan mutuwa,sam bata shiryawa mutuwar taba ta sanar dani tsoro takeji bataso ta mutu, yaa Allah ka gafartawa matata Allah mata rahama" rarrashinsa manga ta somayi seda ya dena kukan sannan yabar gidan gaba daya....

*Bayan wata shida*

Zuwa yanzu su Manga sun faulawa Allah lamuransu game da rashin huddy ta riqe yaran huddy da gaskia, madeena kuwa bazaka tab'a cewa wai bakwaini aka haifeta ba, yanda ta girma tayi b'ul b'ul da ita gwanin sha'awa.....Shirin tafiya Niger suke hutu sabida sosai suke buqatar ganin gida dukkansu....

*Nigeria*

Gidan Manga dake Arqillah suka sauka ita da ahalainta, se murna suke sunzo gida, kayan ciye ciye kuwa gasunan an wadatasu dashi, Bayan sunci sun qoshi suka soma baccin gajiya, har yara, se washe gari suka shirya zuwa su gayar dasu ummu da kuma su Innoh.....Gidan sarki suka fara dira sunsha tarba me kyau acan ma, ummu tace

"Ni kuwa Auta naga se wani sussune kai kikeyi duk kin wani girma an dena shagwab'a yanzu kuma kunyana akeji?" murmutayi tace

"Ba haka bane ummu gani nayi ga yarana se kuma su ganni ina shagwaba" tae maganar cikin shagwaba wanda ya baiwa kowa dariya har Ameen yace laaa Ummi shagwaba kike kema, amma kullum sekina dungurin madeena wai kukan banza ne da ita da shagwaban tsiya" dariya suka qara sakawa ummu tace

"Gwara da ake dungurin kishiyata, dama anzo kwacen miji kuma kurwarshi kur" kwanciya akan cinyar ummu Manga tayi tace

"Uwa me dadi kaga ni bazan koma saudia ba idan kun tashi ku tafi abinku" bece komai ba se Ameer ne yace

"Idan mukace Amusement park bazaki hau lilo da dragon ba kuwa" kowa se ya kwashe da dariya Ameer an qara samun baki shekara shida se wayon tsiya, shafa bayanta ummu tayi tace

"Auta kinsan yanzu kin qara girma ko, kalli yanda kike neman b'allamun qafa dan Allah, lukuta niki d'agani dan Allah" murmushi tayi ta qara lumewa ajikinta tana cewa

"Kai ummu yanzu nice lukuta,tun yaushe rabon daki sakani a idanki,gwara ki barni in biya bashin danaci" rankwashin ta tayi ta dafe wurin tana shura kafa yayinda Abin ya matuqar burge Ali Abbas yakuma baiwa Ameer harma da Ameerah matuqar dariya suka kuwa dara ummin su tana shagwaba irin na yara...sun wuni suna raha abinsu se la'asar sakaliya suka bar gidan zuwa gidansu innon Iroh Baban Manga....Bayan gaishe gaishe aka kuma shiga hirar rabo, anan ne Baban Manga ke sanar musu mahaifinshi yazo ban haquri kuma komai ya wuce dan Haka su shirya zuwa Niger kai Madeena aganta tare dashi zasuje kuma bazasu dawo ba shida innoh kasancewar an saka rana mahaifinshi zeyi murabus shiya hau karagar mulkin.....sunyi murna matuqa daga haka aka tsaida ranar tafiyar....

*Niger republic*

Kowa seda ya hallara aka daura mahaifin Manga kan mulkin qasarsu ta yamai, inda abin Mamaki Mahaifiyar Manga ciki ne da ita harna watanni hudu amma bata gayawa kowa ba se manga acewarta kunya ma takeji wlhy, haka dai akai shagulgula irin na al'ada masu ban sha'awa aka watse, mahaifin Baban Manga ya baiwa me martaba sarkin musulmi da ahalinshi haquri kuma komai ya wuce......

Tafiya takeyi a sukwane,tayi baqi qirin zaka rantse da Allah ba Ammyn su huddy bace yanda ta lalace, a wani gindin ice ta zauna, a garin na Akrah dake cikin birnin Ghana se kallon motocin dake shawagi takeyi, sam bata iya tunano rayuwarta ta baya ko sunan ta, gabaki daya ta fita hayyacinta kowa kallon mahau kaciya tuburan yake mata, Mahaifinsu huddy daya taho gana siyan wasu qarafa acan ya hangota zaune tana zare idanu, kallo daya ya mata qirjinsa ya doka, me taxi din ya tsayar ya fito daga cikin motar yaje gareta,kallonshi tayi amma sam bata gano shiba, gashi dai a kasan zuciyarta tanaji tasan wani abu gameda wannan mutumin amma sam ta kasa gane komai, shine yayi qarfin halin kiran Allah
Chapter 37 · 0% Book details